YAR TSILLA-TSILLA

11 1 0
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
(Sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️ we
☘️

Story & written
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)
______✍️_______

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A

__________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/
__________________________

Follow me on Wattpad
     @deejerleen

Didicated to my sweetheart (aysher humaira)💋💋💋


Godiya mai yawa ga ɗin bun masoya na, nagode da irin qaunar da kuka nunamin na tayani murnar zagayowar ranar haihuwa tah, hakika Godiya ta tayi kadan wajen gode muku saidai nace Allah yasaka da alkhairi yabarmu tare ya kara dankon zumunci......😍🥰❤️🧡💛💙💜🖤

Ina miga saqon gdy ta ga YAR TSILLA-TSILLA FANS GROUP inajin dadin comments dinku 🤗🤗🥰🥰🥰

Jinjina gareku TAMBARI WRITER'S, dagiyan bayanku nake takawa, Allah ya kara hada kawunan mu yakara daukaka tambarin mu, domin da tambarin mu muke tafe 🔱 san so fisabilillahi 🥰💖💖🥰😍😍😍

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.


NOT EDITED 🛠️

Page 5&6

Bayan sun kwanta ne, kowa ya juyama dan uwansa baya, tuni abu tayi baccinta shiko hamza idonsa biyu ya kasa bacci yana ta tunan nin ta ina zai bullowa abu tabashi hadin kai....

Yana cikin wannan tunanin yaji tana minshari, dasauri ya tashi yana innalillahi wa'inna ilaihir raji'unn mina keji haka, wani wawan duka ya mata a gadon bayanta hakan yasa abu ta tashi kamar mahaukaciya tana ihu tana akawo mata dauki zasu kasheni.....zasu ballani......wayyo jama'a nayi gamo da mungayen daji masu cin mutane!!!

Haka tayi ta fada can dai ta tsagaita kukan, takai dubanta ga gefenta saita ga hamza tsaya akanta yana kallonta, shafa bayanta tayi inda ya duka, ce masa tayi ina suke basu dakeka bako duk lokaci daya ta jera masa tambayar? Baice da ita komai ba kallonta kawai yake,,,,,

Ganin da yayi haryanzu bata dawo cikin hankalinta ba yasa ya daka mata tsawar da takusan tarwatsa tunaninta da kwakwalwar tah, jikin tane ya fara karkarwa tana ja da baya tana nuna shi.....

Dam.....aaaa.......kaiiiiii....neeeeee.......kaaaa.......daaaaaaaa........keniiiiii....... Haka taja maganar bakinta yana karkarwa cike take da tsoro da fargaba,...

Cike da rashin tsoro da imani yafara taku zuwa gabanta, yayinda ita kuma saija baya take hardai ta je karshen bango, karasowa inda take yayi, batai tsammani ba sai saukar mari da taji tauuuu!!! Dafe kuncinta tayi cike da fargaba da sabon tsoronsa da ya shigeta tace

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now