YAR TSILLA-TSILLA

9 0 0
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
( Sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

Story & written
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)
________✍️________

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A

____________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/

____________________________

Follow me on Wattpad
  @deejerleen

Didicated to my sweetheart (aysher humaira)💋💋💋

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem,da sunan allah mai rahma mai jin kai.

NOT EDITED 🛠️

Page 11&12

CIGABAN LABARI...
★★★★★
Shirinta ta gama cikin doguwar riga light blue mai ratsin fari da baki farin hijabinta ta dauko tasa, fita daga gidan tayi tasa mukulli ta kulleshi.

Tana tafiya tana yar waqarta har ta isa gidan goggo abu, da sallama dauke a bakinta ta shiga cikin gidan, tarar da goggo abu tayi a tsakar gida tana gyaran garin kunu.

Kara sawa tayi tana cewa

"Goggo ina yini"

Neman wurin zama tayi ta zauna, goggo dake bakin murhu tace

"Lafiya kalau abunah yana ganki yanzu badai kicemin harkin fara fita ba da auren naku ko sati baiyiba"


Zama abu ta gyara tana faɗin

"Haba dai goggo azaba ce ta koroni"

Goggo abu tace

"Bangane ba yimin yadda zan fahimta bangane azabace ta koroki ba"

Abu cewa tayi

"Ai wallahi goggo inda kikasan jaka aka kai masa haka yake dukana ga baya kawowa abinci kullum sau daya mukeci..😭"

Ta ida zancen cikeda kissa da kari akan abinda ba'ayiba

Salati goggo abu tayi tace

"Yanzu haka hamza zaimin na bashi riqon ƴa amana amma yake dukamin ita, yau naga karshena ni zainabu..🤔"

Ita kuwa abu jin zancen ta yasamu karbuwa ta kara da sharin kulle ta yakeyi tun safe sai dare yake bude ta.

Goggo tashiga lallashin ta da cewa

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now