YAR TSILLA-TSILLA

19 1 2
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️'
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
(sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

Story & written
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)
_______✍️______

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A

____________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/
___________________________

Follow me on Wattpad
   @deejerleen

Didicated to my sweetheart (aysher humaira)💋💋💋


SADAUKARWA GA AISHA MUHAMMAD DAUDA, ƊIYATA FATY, UNCL KAWU COMMENTS DINKU YANA KARAMIN KUZARI DA KARFIN GWIWAR CI GABA DA RUBUTU, SONSO FISABILILLAHI 😘😘😘

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.

NOT EDITED 🛠️

Page 19&20

Salati inna keyi har sau uku aunty hadiza da hankalin tah ya tashi tace,

"Lafiya meke faruwa...?".

Ta jera mata tambayar tashi daya cike da fargabar me inna taji, inna ce tace,

"Wai kinji ansameta a barikin karuwai, hadiza zama bai kama muba tashi muje mu gano",

Cike da jimamin abun tareda takaici ta dauko hijab dinta tasa suka fita dan ko magana takasa sai zancen zuci da take yi,

"Anya abu ce kuwa nasan tsoro ne da ita bazata iya zuwa ba( jan hankali uwa na tareda danta ko yarta amma bata san halinta ba ma'ana miza tayi da wanda bazata yi ba har sai wani na waje ya gane mata Allah yasa mudace), hakadai ta karaci zancen zucinta bata samu mafita ba,

Suna fitowa waje suka nemi taxi ya kaisu unguwar karuwai na garin, atare suka isa da hamza, Mutumin da ya kira hamza ne ya qara so wurinsu,

Gaisawa sukayi sannan yace su biyoshi, bin bayansa sukayi can cikin wani gida mai dauke da dakuna daban daban, haka suke ratsa jama'a suke wucewa can kusan qarshen gidan ya nufi wani daki, juuyowa garesu yayi yace,

"Hajiya ku qaraso mana",

Cike da fargabar komi zasu tarar suka tunkari dakin, bude kofar yayi ya shiga yace,

" koba itace wannan bah ",

Ya nuna musu wata budurwa tareda ita kuma wani saurayi ne.......

************
Bangaren abu kuwa koda nafarka naganni inda ban sani bah sai nakasa magana bayan Kuma ga maganar arainah nakasa fadinta sai zancen zuci da nakeyi, dakine da babu abinda babu na buqatar ƴa mace aciki, can ina cikin tunanin a'inah nake naji anbude kofar dakin da nake anshigo, wata mata ce baka bacan sosae ba mai kirar samudawan da ga tsayi da jiki, kana ganinta kasan ba musulunci tattare da ita, kanta attachment ne da aka masa kitso kanana kalaba.

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now