YAR TSILLA-TSILLA

16 1 5
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
(sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

Story & written
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)
________✍️________

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A

__________________________

ttps://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/__________________________

Follow me on Wattpad
@deejerleen

Didicated to my sweetheart (aysher humaira)💋💋💋

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem,da sunan allah mai rahma mai jin kai.

NOT EDITED 🛠️


Page 21&22

Itace wannan ta ke nuna ni!, cikin firgici da tashin hankali wanda bantaba ganiba bansan sanda na saki fitsari awando ba dan tsananin tashin hankalin abinda nagani har jiri jiri nakeji, bansake cinkewa a alamarin ba saida naji wata arniyar dariya da aljanin keyi,

Matar da mukazo da ita, itama tafasa wata uwar dariya, tsawa aljanin yayi wanda saida kogin ya murɗa kasa take jijjiga kamar ta tsage wanda wannan karon har ita matar itama ta razana sosai sannan yace da ita.

"Kiyi gaggawar kikoma da ita dan ba tsoka ajikinta sosai, abata abinci tayi kiba sai'ki dawo da ita tareda yarinya yar shekara shida nabaki yau zuwa gobe kidawomin da abunda na buqata inbahaka ba kinsani......!!  Kinsa.......!!! baruwa nah.......!! Keki kajama kankiiiiiiiii.........!!!!!

Yana gama faɗar hakan ya bace, cikin rawar jiki tajani muka koka motar, cikin ɓacin rai da take jan motar da mungun speed, kai tsaye cikin dajin muka koma..

Tun komawar mu gidan tasa aka kawomin abinci mai rai da lafiya, abinka da najima banhaɗu da abinci mai kyau ba yasa na faraci ba kama hannun yaro, dankwa mutumiya tace gashasshiyar kaza ce da jalof na shinkafa sai sakwara da miyar agushi, tareda bulango da tsire cikin tsinkensa nema ba'a cireshi ba.

Kura ta samu nama haka ta tisani gaba kwana nayi ina ci, cikina kam kamar zai fashe, ina kuka inaci dan cewa tayi inban cinyeba zata kasheni, kuma abincin mutum goma ma ya musu yawa balle ni yar tatsitsiya dani😭😭.

Dakyar dai tabarni nasamu na kwanta, kasa bacci nayi cikin dare data fitane allah ya taimakeni nasamu amayar da wani abun danaci, cikin ikon allah nasamu naɗan yi bacci

Washegari tunda asuba tasa aka kawomin wani abincin inaci ina kuka, bayan nagama tace naje nayi wanka, koda nafito natarar da itane hannunta riƙe da kaya, bani kayan tayi ta umar ceni dana sah, amsa nayi nasa sannan muka fice, yauma kamar jiya nida itane muka fita saidai ba hanyar da mukabi jiya bace watace daban.....

****************
Bangaren hamza da inna da aunty hadiza kuwa koda sukaje kauyen ba ita bace, haka suka dinga zuwa kauyukan kusa da garin suna duba duk inda akace ƴan mata da samari nazama amma babu Abu ba alamarta,

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now