YAR TSILLA-TSILLA

10 2 0
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
(Sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

Story & written
By
khadeejah lawan usman
(Deejerleen)

_______✍️_______

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A

__________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/
___________________________

Follow me on Wattpad
  @deejerleen

Didicated to my sweetheart (aysher humaira) 💋💋💋

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.

NOT EDITED 🛠️

PAGE 29&30

Ƙofar gidan kawai dana hango gabana yace rass!!, Cikin rashin kuzari nake taka ƙafata zuwa ƙofar gidan, da sallama dauke a bakina na shiga, na tarar da anty fanna ɗin a tsakar gida kan tabarma, amsamin sallamar tawa tayi, abinda ya bani mamaki yadda bata nunamin komai ba, aina kika tsaya?,

"Hajjo ce ta tsayar dani sbd iska daya taso", inji Abuu,

Shiru tayi bata ce komai ba, kallonta tamaida zuwa ga kayan dake hannun Abu din, tace mata,

"Mene a hannunki?", Abu tace,

"Kaya ne dasu hajjo suka bani",

Kwace kayan aunty fanna tayi sannan
Tace da ita,

"Ki wuce ki gyara ga aliyu nan zaizo ku gaisa", cikin rashin fahimta tace wani aliyu ɗin anty?".

Wanda yazo jiya yace yana sonki nikuwa na bashi iznin zuwa zance kuma dama ɗan uwanki ne dan haka ki shirya ya kusa zuwa.

Tana kare faɗar hakan ta nemi wuri abinta ta kishingiɗa, Abu cikin rashin kuzari ta nufi ɗakinsu ta shirya, ana cikin hakane yayi sallama cikin gidan, gaisawa sukayi da anty ɗin, kwalawa Abu kira tayi shi kuma ta bashi darduma ya shimfiɗa a zauren gidan, yana zaune Abu ta shigo zauren bakinta ɗauke da sallama nesa dashi ta samu ta zauna.

Firarta su bawani dadi saboda taki sakewa su tattauna karshe ma tace dashi dan allah ya fita harkarta ita bata sonsa sannan kuma ita ta gaji ta tashi takoma cikin gida abinta.

Yajima azaune yana tunanin ko ta halin ƙaƙa saiya auri Abu ko taso ko karta so shibai dame shi ba barima ya bawa anty dan wani abu, tashi yayi ya bar dardumar wurin ya karasa ciki gidan,

Abu kuwa tana shigo wa tacewa anty ɗin ya tafi, bata jira cewar ta ba tayi hanyar ɗakin su tana shiga ta sa sakata ta kulle ɗakin dan tasan anty zata biyota.

Ita kuwa anty fanna ganin bai shigo ba yasa ta tashi zata leƙa zauren sukayi kicibis a hanya.

Sallama ya mata tareda bata kuɗin da baisan nawa bane ya zaro su kawai, hannu tasa ta amsa tana godiya tace masa ai kamar ka aure ta ne indai nice fanna, murmushin kasaita yayi yace,

"Ainasan banda matsala dake, amma dai a kara jan kunnen ta dan taso mun rashin kunya, amma don allah karki doketa yarinya ce",

Kwafa tayi tace "dama nasan hakan zai faru dan kunnen ƙashi gareta batajin magana ta amma kayi hakuri bazai sake faruwa ba, agaisheda mutan gidan", ya amsa da ameeeen sannan yasa kai ya fice.

Haka rayuwa tayi ta ganganɗawa inda baƙin ciki yau yafi na jiya a wurin abu, kullum aliyu kuwa saiya zo zance dolen Abu take fita gudun masifar anty fanna.

Abu da tarasa abunda zatayi kawai sai ta yanke shawarar zuwa wurin anty hadiza ta faɗa mata yadda ake ciki, koda taje gidan ta sanar da anty hadizan hakuri ta bata tace ba yadda zatayi da inna hurera da fanna, inna mata  maganar ta nunamin zumunci shiyasa na 'kyaleta abinda zance dake kawai kiyi hakuri ki rungumi kaddarar ki insha allah zata wuce kinji niko Abu!, Tana kuka tace "naji anty shikenan ni zan koma kar anty fanna ta nemeni", daga haka tayi ma anty hadiza sallama ta koma gida.

Cikin kwanakin ne anty fanna takai maganar ga baban Abu da inna hurera, basu yi wata wata ba suka amince da zancen kasancewar babarsa yar uwar inna hurera ce.

Aliyu yayi murna Sosai jin wannan zance bakin anty fanna inda Abu kuwa sam zancen bai mata daɗi ba, ya tura magabatan sa cikin wata ɗaya aka kawo gaisuwa da lefe da yankan rana aka yanke sati biyu masu zuwa.

Rana bata ƙarya saidai uwar ɗiya taji kunya, a yau ranar asabat  ɗaya ga watan Satumba shekara ta dubu biyu da goma sha huɗu,bayan an idar da sallar zuhur dubban mutane suka shaida ɗaurin auren *ALIYU ABUBAKAR da amaryarsa ZAINAB USMAN akan sadaki dubu hamsin.

Anan gida kuwa ya hargitse da yan biki kala kala, can gefe na hango su momcy, deenah, lili da my bintutu dasu Yar TSILLA-TSILLA fans grp da TAMBARI WRITER'S ADMIN suna cikin sha'anin biki bakajin komai na tashi sai sautin kiɗan kwarya da shewar yan biki, taro yayi taro kasancewar su yan manyan gida, alhmdlillah anci ansha sai godiyar mai sama, haka taron ya watse cike da farin ciki ana shirin kaiwa amarya gidanta.

Bayan sallar isha ana shirin kaiwa amarya ɗakin mijinta aka nemeta aka rasa ko sama ko kasa ba Abu ba dalilinta.

Koda aka faɗawa anty fanna bakaramin tashi hankalin ta yayi ba, nan suka shiga neman Abu lungu da saƙo amma wayam kamar shirwa ta sace.

Har wajen karfe goma na dare anyi neman duniya ba'aganta ba duk inda akesa ran zataje anje bata nan, hankalin anty fanna ne ya ƙara tashi inda ta lalubo number ɗin inna hurera ta sanar da ita halin da ake ciki ganin boyen ba zai haifar musu da ɗa mai idoba yasa suka sanar da ita ɗin.

Inna hurera jin wannan zance yasa ta kiran aunty hadiza tasanar da ita, koda anty hadiza taji zancen itama hankalin ta ya tashi, tana zaune tana saƙe saƙe saiga sallamar inna hurera, fita sukayi a napep itada anty hadizan.

Kai tsaye gidan mai unguwa akaje aka sanar dashi daga nan suka bi gidajen ƴan uwa da abokan arziki harma da wanda ba'ayi duk sun leqa amma ba Abu, tuni agogo ya buga karfe goma sha biyu na dare, daga dai karshe suka yanke zuwa tasha.

Kai tsaya tasha suka nufa, koda suka je babbar tasha basu ganta ba yanke shawarar tafiya sabuwar tasha sukayi.

**     ***    ****    ****   ***   ****  ****

Abangaren Abu kuwa da taga dai dagaske anɗaura auren bamai bin kadun tah yasa ta tattara kayanta awata jaka ta rufe, saida ta duba taga bamai ganinta kowa yana kiciniyar yin sallah yasa ta saci jiki ta fice batare da kowa ya ankare bata nan ba.

Bakin titi ta fito tanemi abin hawa, kai tsaye sabuwar tasha tace ya kaita.

Ana sau'ke ta tanemi motar da zai kaita garin dutse, tana cikin motar da ana jiran fasinja su cika mota tashi ta hango su............

*Tofah ko suwa Abu ta hango muje zuwa......*💃💃

*Please share fisabilillah*

*Don't forget to*

*Vote*
*Comment*

#deejerleen......✍️

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 15, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now