YAR TSILLA-TSILLA

12 2 2
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
(Sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

Story & written
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma)).

T.W.A

__________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/
__________________________

Follow me on Wattpad
     @deejerleen

Didicated to my sweetheart (aysher humaira)💋💋💋

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.

NOT EDITED 🛠️

PAGE 27&28

Keeeee matsiya ciya! Waye bawanki dazaki kwanta baki fito ba, to wlh kitashi tun kafin nazo na tattakaki nakarya ƙasusuwan ki yar iska marar amfani kawai wanda tayi yawon duniya kwararo², dan hka kitaso ga aikin kinan yana jiranki zanshiga maƙota saura na dawo bakiyi komai bah kiga yadda zan tattakaki cikin gidan nan.

Haka dai aunty fanna ke durama Abu zaki da maganganu marasa kan gado da dadi, cikin kuka abu ta fito sai dafen bango takeyi saka makon jirin dake neman kwasar tah, ahaka tafara wanke-wanken kwanuka, debowa ruwa tafita yi waje donyin wanki, allah yasota fanfo din ba layi, taɗebo tadawo gida, wankin tafarayi sannan ta share gidan tasake ɗebo wani ruwan ta shiga wanka.

Koda ta fito ta shirya cikin riga da skirt na atamfah sai ta shiga duba abincin tah na safe amma bataga komai kama da hkn bah, batasan lkcin da wani hawayen ya sake zubo mata bah, hijabin ta tazaro cikin sauri kar aunty fanna ta dawo ta fita zuwa gidan ya habu( yayan inna hurera) dake anan unguwar yake da zama, matar sa mai kirki ce kuma tasan halin da abun ke ciki hakan yasa tana zuwa ta zubo mata abinci taci.

Bayan na gama cin abincin nasha ruwa na koshi, sai nace mata,"anty uwani zan tafi kar ta dawo bata sameniba" matar da ta kira da anty uwani tace da ita"toh Abu saikin dawo", namata sallama nafito.

Ina tafe kirjina na dukan uku saura kwata ahaka na isah gidan, cikin sanɗa nake tafiya harna isa kofar dakina zan shiga naji tace "toh munafuka annamimiya gidan ubanwa kika tafi kika barmin gida ba kowa.🤨🤨

Abu dai shiru tayi tana rarraba ido tasan yau mai kwatar ta sai allah, tazaburo kanta ta cafko hannuta, bulalar dake ijeye gefenta ta zaro tafara lafta mata, ana cikin haka dinne aliyu ya shigo(dan yar uwar inna hurera ne da mahaifiyar sa da inna hurera uban su daya), yana shigowa yayi saurin amsar ta kasancewar ita anty fanna na tsoran sa kuma najin maganar sah.

Abu dake bayan aliyu sai nishin azaba take tareda kwallar data cika mata idanu, aliyu ne yace da fannah din "haba anty mene hakan zakina dukan ta bakiga ita macece bah dan allah karki sake wannan aiba daidai bane" yakarasa fada tareda buga wata tsuka.😗😗

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now