YAR TSILLA-TSILLA

9 0 2
                                    

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

YAR TSILLA-TSILLA
(Sanadin rashin kulawar uwa da uba)

☘️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

Story & written
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)

_______✍️_______

TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION
🔱((Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))

T.W.A

__________________________

https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/__________________________

Follow me on Wattpad
@deejerleen

Didicated to my sweetheart (aysher humaira)💋💋💋

True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.

NOT EDITED 🛠️

Page 15&16

Da matsanan cin ciwon ciki, yanata murkusu suwa har allah ya kawo abokinsa bala, halin da bala ya tarar dashine yayi bala'in tada masa da hankali, waje yaje yasamu mai keke napep ya tara, dawowa yayi suka daukeshi sai special hospital azare..

Koda suka isa asibiti sunsamu ba mutane sosai, cikin sauki aka musu komai, binciken da akayi ne ya tabbatar musu da cewa ciwon mara mai tsanani ne kedamunshi,,

Likitan yabashi shawarar da yayi aure shine kadai maganin matsalar sa sannan ya bashi wasu magungunan dazasu taimaka masa.

Koda suka fito waje bala ne ke ce masa,

"Taya ya kabari wannan abu yafaru dakai haka bayan kanada mata..?".

Shiru hamza ya masa, sake maimaita kansa yayi sannan hamza yace,

"Kaine babban aminina hakan zaisa na fadama kozaka bani shawara, nidai har yanzu bansan abu matsayin ƴa mace ba",

Cikin tsantsar mamaki bala ƴace,

"Saboda mi...?",

Hamza ne daya fara gajiya da tambayoyin bala ƴace,

"Taki yarda tabani hadin kaine, muje karakani gida na kwanta".

Bala bai qara cewa komai ba suka wuce gida...

**********
Alhmdlillah sunsauka gida lafiya, yan uwa da abokan arziki sai zuwa duba jikin goggo sukeyi, cikinsu harda ƴaƴan ɗan yar uwarta wanda suke garin da wanda basa garin, mallam musa ma yazo, alhj mai nasara ma yazo dukkan dauke da abin arziki sukazo,

Aranar abu ta koma gidanta, tarar da gidan tayi yayi kura da datti, dayake bata da son jiki Cikin kankanin lokaci ta gyara gidan tsaf, wanka tayi tabi lafiyar gado, rabonta da bacci mai kyau tunkafin sutafi Kano,,

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now