JINNAH MATAR ALJAN part 2 ep2. N and N writers association
Salam yan uwa mabiya bibiyar novel din,mu kusani cewa Jinnah matar aljan kashi na biyu ne wannan kuma yazo da tsarabe tsare be na musamman za kuga kamar labarin ya canja amma idan kukai hakuri kuka nitsa cikin labarin zakuga labarin ba canjawa yay ba kawai mudan koma baya ne tun lokacin su Khufu na birnin misra kasar Egypt kenan ko? Dan jin dadin Ku muke debe muku kewa naku akoda yaushe N and N writers.association.......... A shekara ta 2021 a kasar NIGERIA yau antashi ana zabga rana kusan kowa zaka ganshi da lema banda ma,aikata. wani gidane tsararre awata unguwa mai suna farawa layout gidan tamkar wani gidan sarauta tsarinsa ciki da waje, Wata murya naji tana kiran nafisa kai ko ba,a fadaba naso gane wake magana sarace kuwa cikin wata irin shiga ta alfarma Sara kenan uwar dakin Jinnah marigayiya, nafisa wai ba ke nake kira ba kina jina wai kwana 2 meke daminki ne eye idan kika zauna saikita tunani lafiya kuwa! ina aya take tun safe bangan ta ba? nafisa tace eh ta cemun makaranta zata tana da text din history but I don't know when zata dawo. amma sai nayi maganin yarin yar nan shine zata fita bata fadan ba tashi kishiga dakin Abdul ki duba ko lafiya yau banji duriyar saba to mama Sara, nafisa ta tashi ta nufi dakin Abdul a can ban garan anayin gidan su bata dau wani lokaci mai yawa ba ta karaso wajen kofar dakin Abdul din kwan,kwa sawatai kusan sai uku amma shiru kakeji anya kuwa lafiya kodai Abdul baya nan dai inda yana nan da ya kamata ace ya amsa bari dai naje na dawo in anjima ko yana bandaki ne harta juya wata zuciyar tace kawai ki shiga ai dakin yayan kine makullin kofar ta murda tare da shiga dakin tana me sallama amma shiru Abdul baya falo to bari na duba dakin baccinsa koda taje dakin baccin ta shiga sai ta hango Abdul bisa kan gado yana hada wani irin gumi bacci yake amma duk Wanda yaga fuskar sa yasan wannan baccin wahala yakeyi da gudu nafisa ta karaso kusa dashi ta zauna tana me karan ta masa addu,a tana tofa mai tare dai masa firfita tsan,tsar tashin hankali nafisa take ciki domin bataso taga ya,yan ta cikin matsala ko kadan tunda ta fara mai addu,a sai ya dena mummunan mafarkin nan amma kuma bai farka ba a dai dai wannan lokacin ne aya ta shigo cikin dakin tana sallama ayace tabbas wacce ayanzu ta ke shekara 18 kana ganinta kaga Jinnah sak ba abun da ta bari akaman nin uwarta idan da Jinnah zata dawo agansu tare cewa za,ai yan biyu ne tsabar kamar tasu tayi yawa anti nafisa kizo inji mama Sara, wai dubo Abdul din ke,nen? inji aya nafisa juyowa tai suka hada ido take aya ta karanci tunaninta nan da nan,kwa ta karaso kusa da Abdul din tasa hannunta ta akan goshin sa hakan na faruwa sai ga Abdul ya tashi firgigit yana mai salati aya ce ta kalleshi tace mafarki kake ko? Eh yace! dame kake mafarkin haka daya saka cikin wannan halin bara na baka ruwa dai inji aya tashi tai taje ta dauko ruwa ta mika mai Abdul ya karbi ruwan ya bude ya fara kwan,kwada, ruwan kamar Wanda yay tafiya mai nisa acikin rana mai zafi, bai ajiyeba har saida ruwan ya kare nan da nan ya fara sauke wata irin ajiyar zuciya To bamu labarin abunda ka gani. juyowa yay yakalle su duka duk sun zuba mai ido sunaso suji mai zaice ajiyar zuciya yay sannan yace yau kusan wata na daya kenan ina wani,irin mummunan mafarki mai furgitar wa To kaba mu labari mana! Kasan yadda hankalin mu yake atashe kuwa! inji nafisa aya tace, nafisa kibishi ahankali mana ai zai fada mana meke faruwa ko,Abdul ne yace acikin wata alkarya ce nake ganina sa,e da lokaci cikin wata masarauta dauke da yan mata cikin shigar ado na muta'nanda ga kayan mar,mari agabansu suna sha ni kuma ina kan wani gado na alfarma tare da wata kyakkyawar budur wa tayi ado irin na mutanan kasar Egypt tana sha yar dani ruwan inibi bayan ta gama shayar dani sai ta kwantar dani ta hau'ruwan cikina ta dauko wata jar wuka zata cakamun acikin kirjina ni kuma duk lokacin da hakan ta faru ina rike wukar muyita kokawa har sai wani acikin Ku yazo ya tai makeni da'zarar ta fara shirin cakamun wukar wannan yan mata duk! suke juyewa su koma wayansu bakaken aljanu marasa kyan gani shiru yadanyi sannan ya Dan ja numfashi sannan ya kalli kanwarsa nafisa yace kinga yau kece kika tai makeni kikazo kuka Ringa fada da wan'nan kyakkywar budurwar har kika sami damar korarsu, amma jiya,mayar da kallonsa yay kan aya ,sannan yace jiya Jinnah ce ta tai maken bayan ta tai makeni ne take cemun na dage da addu,a domin muna cikin tashin hankali babba sannan tace mun aya ke diyace awajen mu ba ban mu shine kakanki kuma tace na fada miki tana tare da mu akoda yaushe duk rintsi duk wuya tace ki rike addu'a karki sakaci saboda mai son abunka yafika dabara idon aya ne ya fara zubda hawaye tana shashshekar kuka tana cewa, na Dade da sanin cewa baban ku shine kakana amma na bar abun ne don inajin ba kin ciki aduk lokacin dana tuna da yadda aka sami mamana ba ta hanyar halak bace shiyasa, nafisa ce ta dafa kafadar ta tana mai ce mata hakuri zaki haka Allah yayi abun zai kasance sannan kuma, Abdul yace, A mafarkina ina ganin yayanki ayu na zuwa tai makona yana cemun ba mutuwa yay ba yana nan atare da mu, nan'kwa kukan aya yatsa'nan ta don ta tuna da Dan uwanta ayu tabbas itama tasan bai mutuba amma ba ta yadda za,ai ya iya ci gaba da rahiwa bayan ya rasa karfinsa nafisa ce tace Ni kuma abunda ke damuna ina yawan mafarki da irin ginin gidan tarihin nan na misirawan Egypt muna wasa aciki nida wasu ya ra kyawawa dukkan mu cikin shigar mutanan misra haka zamuta gudu har sai munzo wata kofa to a dai dai nanne kawai sai na farka tunda na fara mafarkin nan bana gane kai na.aya bakya gani da akwai matala babba kuwa eh da akwai matsala tunda mama tace muna cikin matsala yanzu abunda zamuyi kawai tafiya kasar Egypt wajen wani malamina najib sawiris; Dan yasanar damu meke faruwa damu; to amma kinsan mu ba kamar ke bace baza mu iya kai kan mu ba sai ta hanyar jirgi ko, nafisa tace ? Aya tace tana mai murmushi shin kin manta babana yana iya daukan mama suje kasar Egypt amma ni nakasa daukan ku kin manta cewa nafi banana karfin kafce kisani cewa karfi na Dana banana kamar girman Dan tsako agaban jimina ne zan iya daukan Ku daga nan har zuwa birnin shin batare Dana kosa ba ,to yaushe zamu tafi? inji abdul eh dole sai mun sami karyar da zamuyi wa mama Sara sannan mu tafi ,to yakike gani zamuyi da,ita? inji Abdul eh yadda zamuyi da ita shine zan kirkiri takardu na cewa nafisa ta sami damar zuwa karatu kasar Egypt zaka kaita can wajen yan uwan maman Ku tazauna acan taya kikasan maman mu yar asalin kasar Egypt ce? inji abdul. Aya tace mamanku bata taba gaya muku cewa acan baba ya aurota ba? Abdul yace Eh ta taba bamu labari amma tace karmu damu muci gaba da zama a Nigeria zaman mu anan yafi, banda haka bata taba ce mana wani abuba .. Kinsan yan uwan mu dake can kasar Egypt kenan? Eh inji aya yadda akai nasani shine lokacin da nake bincike akan su wane yan uwana na jini anan nake gane cewa kakata babar mamata itama asalin yar kasar Egypt ce hatsarin jirgine ya kaita kasar Niger ita kadai ta tsira amma ta rasa idonta sauran duk suka mutu acikin wannan halinne ta hadu da kakana harya keta mata haddin ta...nan take aya ta kara fashewa da kuka mai tsuma zuciya nafisa ce ta rungumeta tana rarrashi ita kanta nafisan kukan takes son yi kawai dai ta kai zuciya nesa ne abdul kwa tuni idon sa ya kawo ruwa tsabar kunar zuciya ayace ta cigaban da cewa da kakata da maman Ku Yan uwane kuma sun futo ne daga babban gida sun futo ne daga zuri,ar sawiris nasan Abdul kai zaka rinka jin labarin wani mai kudi a kasar Egypt maisuna NASSIF SAWIRIS ko? Abdul yace eh ina ji to nassif sawiris kaka ne awajena ku kuma uba domin shine babba acikin family din sawiris daga shi sai najib sawiris sai Aisha maman Ku sai kuma kakata Mayah sawiris su wudune awajen babansu, kakata mayah ta biyo jirgine don tazo Nigeria Neman maman Ku Aisha shine harta hadu da wannan matsalar naso na sanar daku tun shekara 1 da mutuwar mamata amma malamina najib sawiris yace na kyale Ku wannan rahiwar tafi muku kwanciyar hankali na kyale har zuwa wannan lokacin gashi kuwa yazo wajen yai tsit kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa firgigit! Dukkan su suka kalli kofa jin motsin mutum Ashe sarace a tsaye awajen ta Dade tsaye basu sani ba nafisa ce ta tashi tana mai cewa mama Sara shhhhh tana mai sa hannunta a baki alamar nafisa tai shiru. sannan ta ce naji komai me yasa da kuke son boye mun Baku dauke ni a matsayin uwa bane ko yaya bazan hanaku zuwa kuga yan uwanku ba kuna da gaskiya amma karku karai min karya banaso kunji, tam kiyi hakuri mama Sara baza mu sake ba murmushi tai ta bude han'na yanta tana musu alamar dasu tawo gareta su rungume juna nankwa suka taso suka hadu suka rungume juna cikin kauna da farin ciki duk kanin su bawanda bai zubda kwallar wannan labarin da aya ta basu ba, haba shiyasa ake cewa nida aya da abdul muna kama da juna kuma Jinnah ma tana kama damu ban bancin mu da Jinnah ta fimu haske da gashi kuma ita ba,acikin mutane ta tasoba Acikin aljanu ta girma, Sara ce ta janye jikinta sannan tace dasu kuje kushirya kayan Ku Ku kama hanya Ku tafi tunda haka ta faru kodan lafiyar ku kunyi saurin zuwa don ni kaina canjin naku yana damuna to mama Sara nan da nan kowa ya tafi dakinsa danyin shiri, Sara kawai suka bari acikin dakin abun duniya ya dameta zama tai akan gadon abdul ba abunda takeyi sai tunani duk wannan cukumurdin abubuwan dasuke faruwa saboda mijina marigayi ne Allah wadaran maka ya lalace koda bani da wani ilimi nasan yin zina ba Abu mai kyau bane amma asanadin fyade da yaiwa maman jina har ta haifi jina nima abun ya shafen duk da cewa nasan ba laifin Wanda ya aikata bane laifin shaidanin daya shiga jikinsa ne ya Allah katsare mu daga yin abun da zai jamana matsala watarana ya Allah ka tsaremu daga kusantar zina Allah ka yafe mana laifikan mu sai kuka sharrr sharrr hawaye na kwaranya a idanuwanta don haryan zu idan suka hada ido da abdul ta tuna abunda suka aikata sanadiyar rashin addu,a da cikakken ilimi yajawo mata, kuka sosai sara take kamar ba ita ba amma dataji motsin za,a shigo dakin saitai sauri ta goge fuskarta da hawayen data ke futar wa idan da sabo ta saba nafisa ce ta shigo cikin dakin tun daga bakin kofa ta kalli fuskar mama Sara tasan tayi kuka da sauri ta karaso gabanta tana mai cewa mama Sara kukan me kike bakyaso mu tafi ko rungume nafisa Sara tai tacigaba da kukanta mai tsuma zuciya adai dai wannan lokacinne abdul da aya suka shigo cikin dakin ganin Sara da nafisa na kukane yasa zuciyarsu ta karaya don sun sani cewa yadda Sara ta damu dasu bazata so su yi nisa da itaba to yaya zamuyi dolene mu tafi, sarace ta janye jikinta ajikin nafisa ta tashi tace kun gama shirin tafiyar taku eh sukace dakinne ya kara shiru nadan lokaci kafin Sara tace to ku tashi ku tafi kar lokaci ya kure muku kunji to kawai sukace jikin su duk a mace kamar karsu tafi amma ya zama dole Abdul ne yace ki kwantar da hankalin ki mama Sara baza mu Dade ba kuma kina da matsayi a cikin zuciyar mu mu mundauke ki uwar mu don tun lokacin da muka fara zama dake mukasan ke uwace ta gari kuma duk rintsin huya ko dadi bazamu manta dake ba, nan dakin yakara daukan shiru, fuskan ta tai aya idan dai basu tafiba to zasu ta bata lokaci a haka to kutawo mu tafi inji aya tana mai bude ta fikan hannunta ta dagasu sannan tabawa nafisa umarni data rike hannun ta na hagu shikuma Abdul ya rike na dama sannan tace ku rufe idan ku karku bude har sai na Baku damar budewa yin hakan ke da huwa sai aya ta bace dasu bat kamar basu taba wanzuwa a wajen ba Sara kuwa tashi tai ta shiga bandakin abdul ta wanke fuskarta sannan ta koma gidan ta don ta daurawa me gidan ta abincin dare tunda yamma ta Riga tayi wannan shine abunda ya faru tsakaninsu aya nafisa da Abdul da Sara da tafiyarsu kasar Egypt ............. ....................................................(NandN) writers association domin mu nisha dantar daku Dan Neman Karin bayani kanemi wanna. Hausachalian@gmail.com /ko kuma 09037786636 ko +227 94 20 36 32
YOU ARE READING
jinah matar aljan book2 ep1
FantasyThis story Its fantasy story abaut Devils who want destroy a wold