JINAH MATAR ALJAN BOOK2 EP7 DAN KARIN BAYANI KUNE MEMU TA SHAFIKAN MU KO NUMBER(09037786636) EP10( N AND N)a wannan lokacin shiru kakeji kamar wucewar mutuwa kowa yayi tsit yana nazari da mamakin wannan Sabin abunda suka hadu dashi daga masu bude baki sai masu tsorata karara sai masu salati tashin hankali kenan duk Wanda ka kalli fuskarsa zakaga tsantsar damuwa don ido ba muduba yasan kima, adai dai wannan lokacinne bokanya suzaina tabaawa dakarun bokanya zarishat umarnin da su afkawa su sarki akeem batare da jiraba nankwa suka kurma urban iwooo gamida karaji suna masu gudu da tsalle tsalle ji kake DUP DUP, idan kaji ana ga ki gudu to sa gudun ne bai zoba nan da nan tashin hankali ya darsu azuciyoyin dakarun sarki akeem suka fara ja da baya koda ganin hakan sai sarkin yakin birnin Khufu ya daka musu tsawa yana mai karaji dacewa wallahi duk Wanda ya kara wani taku makamina ne ajalinsa, mun ginune akan Kare birninmu na Khufu kuma mundau alkawari zamu bada rahiwar mu wajen kare shi to mene yasa zaku ja da baya don kun tsorata shikansa tsoro in kana bashi tsoro tsorata yake kowa yana jina kowa ya tsaya a inda yake zamu fuskanci abokan gaba koda dukkan mu baza mu rahiba !!!nan take wani Sabin karfi yazo musu suka fara kabbara suna masu fuskantar abokan gaba tare da fitar da wannan garkuwar hasken suka kakkafata a cikin kasa duk wannan abunda yake faruwa a ban garen su mayah ma suna sunyi shurin su yayin da Abdul ne ya jagoranci tawagar tasu duk da cewa Maya aya da noor da nafisa suna cikin tawagar sararin samaniya adadai wannan lokacinne naga naurar rabot din malam najib sawiris suna yawo acikin iska fiye da guda Dari biyar amma nayi mamaki Dana gano cewa Wanda malam najib sawiris yake amfani dashi shine mai wani koran haske a kirjinsa haka Dana tsarin yake duk Wanda malam najib ya dauka to wannan hasken zai koma jikinsa koda suka kusan haduwa sai sarkin yakin birnin Khufu ya kurma uban kara yana me cewa!!MADANNIN NAKIYAR FARIN HASKE!!!nan take wani aljani ya falfala da gudu yaje wajen wani madanni yai tsalle akai sa faruwar hakan keda huya kawai sai gani mukai wani darin haske yayi futar burgu daga kasa yana wani irin sa kasa tana girgiza tana tsagewa tawagar bokanya zarishat suna nutsewa cikin karkashin kasa, yana daga cikin abunda ya karawa bokanya zarishat Bacin rai kenan ta takarkare ta kurma uban iwoooo mai kashe dodan kunne nankwa tawagar birnin Khufu suka fara rufe kunnuwansu suna masu kara, kawai sai dai kaga jini na futa ta bakinsu da hacinsu da kunnuwansu koda ayu ya fuskanci cewa indai ba,a tsayarda bokanya zarishat ba nan bada jumawa ba za,a sami mummunan matsala bai yi shawara da kowa ba yay wani irin shillo cikin wani irin salo da kwarewa wajen Sanin makamar aiki yai katantanwa acikin iska kawai sai aka nemeshi akarasa kamar wucewar tauraro mai jela ya gibta fitttt!ta cikin mutanan wajen ya ratsa ta cikin tawagar bokanya zarishat yaje ya daki kirjinta take tai baya taga taga zata wadi kawai sai naga ta caki kasa da kafarta ta yi tsalle ta tsaya acikin iska nan ta tofar da wani bakin jini tana murmushi tace gaskiya ne ayu Dan gidan Jinah matar aljan uwar aya, akan me kike son saka duniya acikin bala'e da masifa!! ayu ya fada cikin daga murya yana karaji, murmushi tai mai sannan tace saboda na kawar da bil'adama adoran kasa ya zamana sai iri,irin mu a doran kasa in kanaso kazo muhada hannu mu kafa mulkin zuriyar mu ta masu irin jikin mu rabi aljan rabi mutum ka sani yanzu adoran kasa babu wani mai karfi da nazari da hangen nesa kamarka duk kana da irin salona da karfina amma dole sai ka hada hannu dani sannan zaka San hakan,tana maganan'ne tana mai juya hannun ta wani irin haske na futowa daga cikin hannu yana shiga cikin kan ayu, shine dalilin abunda yasa ya Kasai mata komai domin tana sone ta juyar mai da tunani tana so tayi amfani da shi bayan ta juyar mai da kwakwalwa, tasami sa,ar yin hakan, to amma kafin ta karasa cika burinta kawai sai sukaga aya ta bayyana tsulum agaban su ta dauke ayu tayi mai wani Abu a jikin goshinsa sannan ta juyo ta kalli bokanya zarishat tana mai cewar karyarki azzaluma tsohuwar banza kiyi sani cewa bazaki taba ai watar da abunda kike so ba saboda haka ki juya dake da shegun dakarun matattunki da aljanunki subar cikin birnin nan in kuma ba haka ba dayansu ba zai futa daga nan da ruhinsa ba idan kuma kina ganin hakan ba zai yiwuba to bissimillah tana wannan maganar ne don ran bokanya zarishat ya bachi saboda indai rants baibaci ba to wannan hasken da ya kawarda hankalin ayu ba zai sakeshi ba har sai tasa bokanya zarishat tabar cikin hankalinsa, kafin aya ta gama rufe bakinta sai kawai taga Bokanya zarishat ta tunkarota a yayinda fuskarta tai jajir koda taga haka kawai sai aya ta huro wata iskada bakinta, iskar bata tsaya ko ina ba sai cikin kun'nan ayu faruwar hakan keda wuya sai ayu ya dawo cikin hankalinsa firgigit a dai dai wannan lokacinne bokanya zarishat ta karaso kusa da aya ta na mai kawo mata cafka da hannunta wowowo ba,a Sanin Maci tuwo sai miya ta kare awannan lokacinne suka fara wani salon yaki hadi da kai wa junan su mugayen hare hare lokacinne naga ayu shima ya tashi zumbir ya taresu suka zama sun hada karfi dashi da aya wajen yakar bokanya zarishat cikin filin yakin ya hargitse duk inda ka leka kajuya sama ko kasa a hargitse yake ga kuma wa ta irin walkiya da ake da wani yayyafi na masifa noor na hango ita da nafisa suna uwar watsi da bokanya suzaina duk da cewa suna cikin wannan robot din dinasour din hakan bai hana bokanya suzaina ta kuntata musu ba haka suka wanzu suna musu kaiwa junansu wawan duka naushi da bugu cikin bakin zafin nama juriya da bajinta ana cikin wannan wawan gumurzun ne bokanya suzaina ta sami damar hadawa su noor da nafisa wawayan naushi Wanda sai da yay sanadin da suka yo kasa daga cikin iska looooooo zasu wado a dai dai wannan lokacinne mayah ta tawo wajensu cikin wani bakin zafin nama da azababben gudu cikin iska ta taresu koda tarike su cikin iska sai tai amfani da karfin dutsenta ta na robot din dinasour ta kara musu karfi faruwar hakan keda wuya karfin su ya dawo suka kara hada karfi daya suka tun kari bokanya zarishat suka kara kacamewa da mugun gumurzu yayinda Maya take leading dinsu ana cikin wannan gumurzun ne na hango hucewar robot din malam najib sawiris yana mai wulla wasu kananan bama bamai duk ida ya fashe sai kaga dakarun bokanya zarishat na tar watsewa suna bunduga haka shima ya wanzu yana mai gumurzu hakan nan malam najib sawiris ne ya hango wasu dakarun bokanya zarishat suna shirin su afkawa sarkin birnin Khufu akeem nan take yay wajen tare da futo da wata irin bulala mai shock nan take ya nannade su da ita ya matsesu, wani badakare ne ya shako huyan robot din malam najib sawiris ya shake faruwar hakan keda wuya sai malam najib sawiris ya sauya reshe zuwa wani robot din a dai dai wannan lokacinne jarimi halanchal da sarkin yakin birnin Khufu suka kawowa sarkin akeem dauki suka wanzu suna mai kai wa abokan gaba mugayan hare hare hadi da Sara da suka naushi gamida bugu jarimi halanchal ne ya dauki daya daga cikin samudawan dakarun yayi wurgi dashi bai wada ko ina ba sai a kansu malik da Abdul yayinda suka rabashi biyu waje ya hargitse yayinda Abdul da malik suke ragar gazar wayan nan dakarun hmmm ina ina ina! Yanayi ya juya domin yanzu ba wani ganewa da ake suwaye ke samun nasara a tsakanin su duk India ka juya ba abunda kakeji face karar iwun mutane da makaman yaki tashin hankalinsa kenan an kai makura cikin wannan gumurzun adai dai wannan lokacinne bokanya Hindu ta karaso filing yakin harza su shigo tace a tsagai ta sarkin azzaliman aljanu ra,asu ne ya jiyo ya kalle ta cikin mamaki yace tayaya zamu tsaya alhalin bamu San halinda bokanya zarishat take cikiba bokanya Hindu ta kalleshi tana mai murmushi tace ya kai ra,asu shin zaka iya fada min Wanda ke samun nasara tsakanin bokanya zarishat da tawagar birnin Khufu nan sarkin azzalumai ra,asu ya girgiza kai alamar bai sani ba take bokanya zarishat tai murmushi tace koda bokanya zarishat ta sami nasarar'cin karfin tawagar birnin Khufu to ni zan tunkareta na yaketa saboda na kare mutuncin ubana da birnin nan Badon komai na zabi na biyo ta wannan hanyar ba sai don na kare ka da jama,arka daga Sharrin bokanya zarishat amma in kaima kana da burin cika mata burinta sai ka dau harama amma kasani indai ka sake ka saki jiki da ita kaima sunan ka gawa domin da zarar ta sami nasara to hattani kaina saita nemi kasheni saboda haka mu tsaya anan har sai munga suwa ye suke cin nasara tsakanin bokanya zarishat da tawagar birnin Khufu da zarar munga bokanya zarishat ta ci nasara to mukuma sai mu yaudareta mu kasheta ta hangar caka mata waccen hukar da take jikin abudul da itane kawai zan iya kasheta amma nafi kyautata zaton ayu shi zai kasheta baniba don zai iya kasheta ba tare da yayi amfani da wani makami ba suna nan a tsaye cikin iska kawai sun saka ido akan me yake faruwar lailai Abu kamar wasa sai gashi tawagar birnin Khufu suna sami nasara akan tawagar bokanya zarishat ba komai ne ya ja hakan ba face bokanya Hindu CE taringa karanto wash surutan tsafi kawai bakinta ne ke motsawa amma ba zakaji komai ba wannan tsatsuba data kene yasa karfin mayakan ya rings karewa suna zagwan yewa suna zama bakar kasa duk wannan abunda take faruwa bokanya zarishat ba ta sani ba domin dalili shine aya da ayu sun hanta sakat sun takurata da suka da sara da suka hakama bokanya suzaina Maya nafisa da noor sun takurata kafin su farga duk dakarun aljanun Dana matattun nan babu ko daya sai bokanya zarishat da bokanya suzaina suma cikin bakin gumurzu suke fafatawa sai ya zamana cewa yakin su kawaima babban tashin hankaline haka aka wanzu ana wannan bakin artabun tsakanin su, sarki akeem na gani cikin wani bakin zafin nama ya bace daga inda yake ya baiyana a dai dai bokanya suzaina a lokacinda su Maya nafisa da noor suka haka karfi waje daya suka kawo mata mummunan Sara kafin saran ya karaso tuni sarki akeem ya bace suka sari iska bai zame ko ina ba sai cikin tawagar sa yana yana sauka bokanya suzaina tana mai ajiyar zuciya don duk azatonta mutuwar ta ce tazo kallonsa tai tace ya kai babban abokin gabar mu mai yasa ka tai maken Baka bari sun kashe ni ba murmushi yay mata sannan yace saboda banaso ki mutu in kuma kika mutu Nima zan iya'mutuwa saboda kaunar da nake miki tun da na fara ganin hotonki' a ina kaga hotona bayan kai Baka shinga cikin duniyar mu? murmushi ya kara yace eh bama shiga duniyar Ku to amma duk wani Abu da kuke ai watarwa muma muna gani ta hanyar sadarwar sirri nasan cewa don ki tashi yar uwarki kika tashi bokanya zarishat to yar uwarki ta tashi saiki tai maka mana muma mu kawar da abokiyar ga barmu murmushi tai tacemai ni bani da burin yin abunda bokanya zarishat ta sani kawai dai inayine don na tabbatar na rama mata abunda tai min kaima kamar yadda ka tai maken nima na dau alkawarin tai makon Ku kuma nagode da nuna soyayyarka akaina nima inasonka tana maganarne tana mai yin wani murmushi mai taushi Sannan ta mike daga jikin sa ta nufi wajen da aya da ayu suke gumurzu da bokanya zarishat ta shiga da wani irin salonta tana mai futar da wasu kananan hukake guda biyu nan kwa suka kara azama cikin kai mata mugayen hara hare ran bokanya zarishat ba karamin baci yay ba ganin bokanya suzaina ta yaudareta ana cikin hakanne bokanya zarishat ta ja da baya tana wani irin murmushi tare da cewa bokanya suzaina ni kika yaudara ko to sai na kasheki murmushi bokanya suzaina tai sannan tace kin tai maken kuma nima na tai makeki tun da harna shigo na biyo ki cikin wannan birnin saboda haka ni yanzu na gama babu abunda ke tsakanina dake yanzu dani dake kawai kare jini biri jini sannan kuma ki sani bama goyan bayanki domin indai na goyi bayanki to nima nasan kasheni zakiyi. hhhhhh tai dariya sannan ta ci gaba da cewa ni da yar uwata ba jinshinki bane aljanune mu hmmmm to in ma kin manta ki tuna kodan mu kare kan mu daga sarrin ki sai mun yakeki da karfin tsiya mun kashe ki hhhhhhhhhhh bokanya zarishat ta fara dariya mai kamada kukan jaririn jaki sannan tace zamu gani tsakanin nida Ku wa zai ci nasara nan take ta daga hannayen ta sama tare da karanto wasu dalazuman tsafi take wani irin narkakken karfe ya rings futowa daga kasa yana shiga jikin bokanya zarishat take sannan narkakken karfe ya lillibe jikin bokanya zarishat sannan ya rings sauyawa yana komawa suffar basamuden mutum mai tsawon taku Dari da Hamsin kafin wani lokaci ya bace take suffar sannan narkakken karfen ta koma ta basamuden jarimin mayakin basamude koda bokanya Hindu taga haka sai itama tai futar burgu tai tsalle cikin iska kamar tauraruwa mai jela ta dira a kusa da aya da ayu da bokanya suzaina ta dafasu ta na mai murmushi a can ban garen Maya nafisa malik da Abdul da noor ma tuni sun shirya sun hade Kansu waje daya tuni suma suka tashi suka zama babban robot din dinasour din tuni suma suka karaso wajen koda ganin hakan sai kawai aya da ayu suma suka kara Nasu karfin a jikin babban robot din dinasour faruwar haka sai Girman dinasour din ya karu hakanne yasa bokanya suzaina da Hindu suma suka kara da karfin su zuwa jikin babban robot din dinasour din hakan keda wuya sai kawai girmansa ya kai dai dai da Girman na bokanya zarishat nan aka fara kallon kallo ayayinda tawagar birnin Khufu suka tattashi sama cikin iska don kallon wannan gumurzun da za,a fafata tsakanin mayakan, ba wani bata lokaci ba aka kacame da azababben yaki tsakanin bokanya zarishat da katotan babban robot din dinasour din su aya da su Hindu Inda ace kana wajen da ake wannan bakin gumurzu sai dodan kun nan ka ya fashe tsabagen bala I da mashifa haka suka wanzu suna masu kai wa juna mugayen hari suna masu kai wa juna mugayen Sara da suka aha yayinda wannan bakin gumurzu yaci gaba da wakana sai nan da nan suka kuntatawa bokanya zarishat ta kasa komai ba tare da jiran komai ba kawai sai mukaga ayu yayi futar burgu daga jikin babban robot din dinasour din ya shige jikin bokanya zarishat kawai sai ji mukai wannan katon basamuden bokanya zarishat ya kurma urban ihiuuu yana zagwanywa kan cikar wani lokaci ya zagwanye duk sai gani mukai bokanya zarishat ta wado kasa tana tari ta na mai cewa Dana zauna Ku kasheni gwanda na kashe kaina kawai ta fadi wata kalma take ta wargaje tabi iska faruwar hakan keda wuya sai komai na wajen ya tsaya cak aka dena wannan walkiyar da yayyafin sannan garin yay haske nan aka fara kabbara ayayin da su aya suka wargaje suka koma dai dai din su Hindu CE ta taba yar uwarta tana mai mata murmushi sannan tace yar uwarta yanzu bamu da matsalar komai kawai mukarbi addinin musulunci bokanya suzaina ta mayar mata da murmushin sannan tace nima abunda yake zuciya ta kenan domin ni bazan koma can ba zan ci gaba da rahiwata anan nida masoyina sarki akeem murmushi sukaiwa juna sannan suka fadi Kalmar shahada da karfi kowa na wajen yaji sanda suka furta faruwar hakan keda wuya sai kawai sarki akeem ya bayyana a gaban yayar sa Hindu ya rungumeta cikin farin ciki yace yay yaya ina acikin farin ciki gashi mun sami nasara ga yayata ta musulunta ita da Rabin raina ya dago yana kallon suzaina nan itama ta karaso wajen su ta rungumesu nan take waje ya fara watsewa . ............. End
Bayan wata daya gari yayi dadi komai ya koma dai dai a yaune sarki akeem da suzaina sukai aure yayinda akai shagalin bikin, Hindu kuwa cewa tai indai malam najib sawiris zai yadda tanason shi bai musa ba Kasan cewar sa masanin komai kuma ba yaro ba daman kuma tunda Babar noor ta rasu bai kara sure ba suma sukai aure nafisa ma ta auri jarimi halanchal yadauketa suka tafi birnin sin ba karamin kuka sukai ba kafin su rabu da juna gani sukai ba anfanin ma su ci gaba da rahiwa a cikin duniyar mutane kawai suyi rahiwar su a birnin Khufu in yaso sun ringa sauka suna shiga duniyar mutane amma duk rintsi a cikin duniyar birnin Khufu zasu ringa kwana hmmmmm aya CE take ta dauko Sara daga gidanta da mijinta ta kawo su birnin Khufu malam najib sawiris ne yakira taron gaggawa wa duk yayansa yace tunda kowannan su Nada masoyi to su shirya yau da daddare zai yi musu aure dukkan su sunyi murnar jin hakan suna zaune sai ga sarki akeem ya shigo bayan sun gaisa ya raba musu wani agogo sannan yace musu wannan agogon yana dauke da na,ura daya daga cikin hanyar da zaku iya zuwa nan birnin kuma zaku iya zuwa ko ina Ku dawo acikin abunda bai fi mintuna ba nan kowa ya dau murna ayace tace ina na nafisa sarki akeem yace suma ai yau'dinnan zasu zo birnin nan kuma anan suma zasu ci gaba da zama aikine ko makarata zairinga shigar da Ku cikin duniyar mutane YAMMACIN YAU A BIRNIN KHUFU kowa yaci ado na kece rai ni kasancewa za ai bikin da ba a tabayinsa a cikin burnin Khufu ba, ko ina ka huce mutane suna tsara yadda suke son suje wajen bikin a yayin da wajan biki tuni ya cika da mutane daga ma banbanta unguwannin birnin Khufu ba,a dau lokacinne ba sai ga amaren sun futo aka daura aure bayan an daura auren ne a all,adar gari ma auratan sai sun zagaya gari kafin su je masaukin su koda suna futo cikin gari suna tafiya sai kawai suka ga wasu aljanu su Dari sun durfafo su cikin mugun nufi faruwar hakan kawai sai dukkansu suka kalli juna suka yi murmushi sannan suka futo da duwatsun robot din dinasour din su take wani haske ya haskaka wajen duka ........... Alhmdllh anan na kawo karshen wannan littafin nawa na jinah book 2 ina godiya wa duk kan makaranta jinah
Kamarsu
Marubucin littafin jinah na daya
Da babbar kawata Aisha ina godiya bissalam mu hadu a cikin sabo littafina yana nan tafe
YOU ARE READING
jinah matar aljan book2 ep1
FantasyThis story Its fantasy story abaut Devils who want destroy a wold