Mysterious city

33 3 6
                                    

JINAH MATAR ALJAN BOOK2 EP7 DAN KARIN BAYANI KUNE MEMU TA SHAFIKAN MU KO NUMBER(09037786636) EP7( N AND N) WRITERSASSOCIATION.................................................... Tunda suka shege cikin kofar nan suka ga sun shiga wani wajen na daban Wanda ba ya kamada irin shashin cikin duniyar mu ta earth bakomai awajen sai farin hadari ko ina awajen, wannan farin hadarin ya zagaye wajen,matattakalar hanyar ma ta gajimarece duk kallonka da hangenka bazakaga karshen fading wajen ba saboda hadarine ya zagaye wajen malam najib sawiris ya bada umarni da acigaba da tafiya nankwa kowa yaci gaba da tafiya daya bayan daya malik na gaba sai mayah sai noor sai Abdul sai nafisa sai aya sai malam najib sawiris. Noor ce ta matsa kusa da Abdul ta kalleshi tana murmushi sannan tace ya Abdul yaya Nigeria take inason ka bani labarin kasar Ku Abdul yay daria yace kinaso kiji labarin Nigeria ko to kije wajen nafisa ko aya, yamutsa fuska tai cikin suffar tabara tace nikai nakeso ka bani ba suba to ki bari sai munkarasa sai na baki lbr ko ummm Dan Allah. ke dai ai kincika naci yace kibari mukarasa zai baki inji mayah to ai bake nace ki bani ba ai nicewa nai yayana ya bani to sannu mai yaya aya tace to ke kuma ina ruwanki. adai dai wannan lokacinne zuciyar aya tafara zafi tana zugi nan ta zube akasa tana nishi tana danna wajen nan hankalin kowa ya tashi ganin aya acikin wannan halin wani Abu na faruwa da ruhin ayu! Wani Abu na faruwa da ruhin Dan uwana ayu! Ayu kana ina kana ina jikina na bani cewa karfinka ya dawo kuma ka tashi kabiyo mu kabiyo mu zuwa cikin birnin khufu mysterious city nan ta wadi ta suma lokaci ba jiran mu zai ba malik dauketa muci gaba da tafiya nan malik ya sabi aya suka kara nausawa ciki nan kwa kowa ya bishi aka cigaba da tafiya ba'a tsayawa in ba sallah ba ko sun gaji yaudai kwanan su 3 ahanya. noor ta kara matsowa kusa da Abdul ta rankwafa fuskarta dai dai kusa da yadda zata iya kallon Abdul tunda ya fita tsayi tana murmushi tace yaya ya maganar mu yay murmushi yace tamefa nan noor ta zumburo baki tana yamutsa fuska zatai shagwaba, to shike nan Shekenan saki fuskarki nan tai murmushi tace to aikaine sai ka ringa jawa mutum aji saikace wata budurwa, nan dariya CE ta subucewa kowa aka dara Abdul yace kiyi hakuri yanzu hankalina atashe yake bazan iya baki lbr komai ba murmushi tai sannan tace to ni bari na baka labari. wanne lbarine zaki bani kai dai ka saurara zan baka labarin nan ne don hankalin ka ya kwanta don bana son ganinka cikin tashin hankali sai bayan ta fadi hakan ne ta rufe bakinta tana zaro ido Dan ta tuna baram baramar datai nan aka kara kwasewa da dariya wannan karan har da malam najib sawiris to shirikina kasaurara kaji me budur wartaka zata fadi nankwa ta rife ido tana jin kunya. muna sauraranki inji mayah nanta bude idonta tana mai cewa me yasha feki da labarin mu toai ke kikace zaki bamu labarin ko inji mayah to ai bake zan bawaba yaya abdul nace yaya abdul kana jina, yace eh labarin jaruma arisha.! jaruma arisha yer wani sarkice wacce ta tashi da jarumta amma ita batason harkar sarauta kuma ita bata yadda da tsafiba jarima arisha ba abunda tafiso irin ta yi yawan duniya hmm arisha wata rana ta tafi wata kASA mai suna Istanbul kawai don tai yawan bude ido ahanya ta hadu da wani saurayi kyakkawa ma'abocin fararan kaya arisha ta kalli wannan saurayin tana me cewa yakai wannan saurayi kai wanene daga cikin mutanan Istanbul murmushi yay sannan yace ni sunana yasir kuma ni musulmine addinin musulunci ne addinina arisha tace eh tabbas nasan addinin kuma nima inaso na zama daya daga cikin mabiya addinin Alhmdllh amma naji dadin hakan ka gaggauta fadan yadda zanshiga addinin yasir bai kai ga yin magana ba sai kawai wani aljani ya sun kuci arisha ya face dasu bat nan ran yasir ya baci buskarsa tai ja ya dauko ta kobinsa ya kwalla kabbara yai tsalle cikin iska yana me Neman arisha ya juma bai gantaba har ya hakura ya sakko yana me hawaye sannan ya kudiri aniyar duk inda take sayya nemota nan ya dauki kayansa ya koma cikin Istanbul. ..hmmm nan noor tai shiru Abdul ya juyo ya kalleta yace sai akai ya kuma noor tace bakaga munzo kofar birnin Khufu ba in kanason ka karasa jin labarin nan kaje ka nemi littafin LITTAFINA NA GABA TAWAGAR WUSHA ta birnin shin adai dai wannan lokacin kowa ya tsaya cak! abakin kofar garin nafesa ce ta karasa wajen kofar garin ta tsaya tana me kallon kofar dai dai wajenda aka yi rubutu nan ta fara karantawa tunda ta fara karantawa wannan guguwar ta fara zagaye a tsakiyar su nafesa haka ta ci gaba da karantawa harta gama. faruwan hakan keda huya sai ga kofar ta bude nan wannan bakar guguwar ta bace bat!  Koda kofar ta gama budewa sai ga cikin kofar wata korama ta bayyana ba abunda kake ji in banda karar ruwa daya ke sau kowa da sautin kukan tsintsaye, nan nafisa ta shiga cikin kofar batare da shakkar komai ba tana mai jin wani nishadi da farin cikin wanda bata san name neba kan kace me kowa ya shigo cikin burnin khufu (mystrious city)  nan kwa duk muka zama yan kauye duk yawan yawon aya acikin duniya bata taba ganin gari mai kyan wannan ba ana cikin haka ne noor taje bakin koramar nan ta debo ruwan koramar ta watsa wa abdul tana dariya shima biye mata yayi ya dibi ruwan zai watsa mata aikwa ta futa da gudu ta kauce aikwa sai ya wa,tsawa mayah itama tace bazata hakura ba sai ta rama nan kwa wajen ya hau tsine ba abunda kake ji sai dariyar su Mayah da noor da malik nafisa Abdul aya shikwa malam najib sawiris yana gefe kawai murmusawa yake yi ana haka ne kawai sai sukaji wata irin iska ta shigo cikin birning mai dauke da guguwa bazaka ga komai ba sai zagayawar iska ana cikin haka n sai kowa ya rife idonsa ba Wanda ya bude sai da akaji tsagaitawar iskar sannan aya  tai karfin halin fara bude idon ta koda ta gama budewa sai ta kurma ihu ta futa da gudu tanufi inda yake ta rungumeshi  sannan tasa kuka tana mai cewa daman nasan ba mutuwa kaiba kawai karfinka ne aka dauke koda jin hk sai kowa ya bude idon sa don yaji wai dawa aya take magana AYU ne !  Nan itama nafisa ta futa da gudu itama taje ta rungumeshi eh tabbas ayu ne duk yawan shekarun da sukai yana nan dai yadda kaman ninsa suke ikon Allah kenan shima hk abdul haka dai kowa. ayune yace karku damu ina tare daku akoda yaushe ruhina yana jikin aya kawai karfina da narasa ne yasa ruhina yabar jikina lokacin da aya ta wadi alokacin ruhina ya futa daga jikinta ne yakoma nawa shiyasa ta suma duk abunda ke faruwa danikukeyi kuma na bada muhimmiyar rawa aciki. kawai dai baza ku gani bane amma nasan kunyi mamakin yadda kuke samun nasara kai tsaye abunda bakusani ba shine ruhina dake jikin aya shine abunda yake tai maka mata wajen kara kaifin bashirar nemo abubuwa da dama  nankwa kowa ya fara mamakin wannan alamarin mai dauke da ban mamaki ana haka ne suka jiyo karar jama,a tako ina cikin garin abunda basu saniba shine rindunar mayakan aljanun garin ne suka futo akan damusa su masu kamada suffar kuraye kan kace me duk sun zagayesu ba abunda kakeji banda gurnanin wayan nan abubuwa masu kamada kuraye nan take kwa ciki ya debi ruwa hankali ya tashi har noor ta fara kuka saboda azatonta yau karshan tane yazo adai dai wannan lokacinne mayakan suka yi wani irin salo suka raba kansu gida biyu suka yi wa kansu hanya saiga wani kyakkawan aljani mai suffar mutane ya nufosu yana mai murmushi yana me cewa lale da zuwa yaku tsatan zuriar sarki khufu barka da zuwa birnin mai ban mamaki nasan zakuyi mamaki ni wane ko to ni sunana aljani akeem da ga mankas  kusani cewa babana ya dade da mutuwa amma yabani wasiyar cewa kune kawai zaku iya shigowa garinnan kuma mu karbeku muyi muku duk abunda kukeso shine zaman lfy mu adoran kasa bakomai ne ya kashe babana ba sai wani asiri da bokanya zarishat tayimai wannan ashirin kwa shine duk ranar da ya yaudareta to shima bazai kara shekara dariba sai ya zama gawa dalilin haka ne ya kasheshi yanzu babban tashin hankalin na shine yar uwata hindu wacce aka hada hannu da ita dana yar uwarta suzairat kusani cewa hindu ita kadai ce zata iya shigoda su bokanya zarishat cikin burnin nan dole ne duk tsiya mu sami hanyar da zamubi don tsayar dasu da zarar sun sami shigowa garin nan to mu ba ta yadda zamuyi dasu don shumfimu karfin sihiri. amma karda muyita bata lokaci anan kuzo mukarasa cikin gari sai mu cigaba da tattaunawa nan kwa aka kawo  musu wani keken doki na alfarma tsaya,fadar tsaruwar kekan ma bata lokacine koda kowa ya shiga cikin keken dokin sai matukin keken ya saki linzami nankwa keken ya fara tafiya bamu ankaraba sai ga abu yana tashi sama ikon Allah kenan Wannan shine abunda ya faru acikin garin Khufu ( mysterious city)

 amma karda muyita bata lokaci anan kuzo mukarasa cikin gari sai mu cigaba da tattaunawa nan kwa aka kawo  musu wani keken doki na alfarma tsaya,fadar tsaruwar kekan ma bata lokacine koda kowa ya shiga cikin keken dokin sai matukin keken ya saki l...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
jinah matar aljan book2 ep1Where stories live. Discover now