JINAH MATAR ALJAN BOOK2 EP12 DAN KARIN BAYANI KUNE MEMU TA SHAFIKAN MU KO NUMBER(09037786636) EP12( N AND N) bayan su aya sun baro wajen taron nan basu zame ko inaba sai wajen wannan katon dakin da mashinan dinasour din suke duk sun gaji kasancewar dare yayi musu a wannan lokacinne jarimi halanchal ya ce dasu su shirya don ya kamata ace sun fara koyar yadda ake tuka wannan masarrafin robot din dinasours da mutum zai iya yin yaki dasu da sauri sauri sukaje suka canja kayan jikin su sannan suka dawo wannan katon dakin inda jarimi halanchal yake bisa wani table Wanda yake a tsakiyar dakin, to Ku zauna inji jarimi halanchal bayan sun zazzauna ne ya fara jawabi kamar haka. ina so Ku tattara hankalin Ku waje daya, zanai muku bayanin yadda zakuyi amfani da wannan nan,urar robot din dinasour , na farko dai wannan na,urar mun samo tane daga duniyar Jupiter shekara Dari hudu baya, aliens sun sauka a wannan burnin kuma munyi mutunci dasu sosai kuma suka nemi abasu wasu daga cikin jama,ar mu don suje dasu duniyar su ta Jupiter don suma suga yadda suke tsarin al'adunsu to da aka tashi tafiya sai aka tafi da sarki akeem lokacin baifi shekara hamsin ba lokacin da suka je duniyar Jupiter sai sarkin aliens din ya bawa sarki akeem wa yansu duwatsu masu launi launi guda biyar yace dashi in ka koma duniyar Ku da akwai wani kogon dutse acikin gefen birnin Ku na Khufu to kaje cikin wannan kogon dutsen zakaga wani ruwa ka zuba wayan"nan duwatsun acikin wannan ruwan bayan kazuba zaka ga wayansu irin gumakan dinasour sun futo daka kasan wannan ruwan to da zarar kaga haka kaje ka fadawa sarki yasa a debesu a shirrince a boyesu a cikin wannan dakin da muke ciki kuma ba wayanda zasu iya amfani dasu sai tsatsan sarki Khufu jikokinsa Wanda zasuzo shekaru masu zuwa suma zasuyi am fani dasune alokacin da duniya take shirin shiga tashin hankali wannan shine takaitaccen tariyin wayannan dinasour din bayan haka da akawai Abudaya Dana manta ban fada mukuba wayannan na,urar dinasour din aya da ayu baza su iya an fani dasu ba don karfin dake jikinsu bai kai na jikin kuba da zarar dayanku ya shiga cikin su kuwa to baza su kara aikiba har abada kamar yadda kuka gani wayannan dinasour din da akwai mai suffar tsuntsu masu tashi sune guda uku ja da kuma kalar pink sai kuma ragowar ukun Jane da blue sannan kuma ni bansan mallakin na kowa ba amma a yadda sarki akeem ya bani tarihin abun da zarar mamallakin daya daga cikin dinasour dinnan yaje kusa da nasa to zaiji ajikisa cewa lallai wannan nasane sannan da akwai heart din dinasours din Wanda yake acikin wancen dakin, heart din kuwa sune wayansu irin duwatsun ne guda biyar,to dazara kowannen ku ya sami nasa to a wannan lokacinne wannan dutsen zaizo inda kake kuma zai zama yana tare dakai ako ina kake ko kayi tafiyar shekara dari da zarar ka bukaceshi zai bayyana a inda kake, yanzu zamu karasa wajen don kowa yasan nasa acikin ku zunbir noor tariga kowa tashi don tana ganin abun kamar wasan yara koda suka karasa wajenda dinasour din suke sai suka tsatstaya sukai layi daya a wannan lokacinne jarimi halanchal ya umarci malik da ya fara gwada kansa nan take yaje saitin wannan bakin dinasour din Wanda shine na gefensa nan take kawai yaji ajikinsa lallai wannan na sane kawai sai ya matsa gabda na,urar dinasour din nasa ya tabashi kawai sai gani mukai jikin dinasour din wani bakin hayaki yana ratsashi daga karshe sai gani mukai dinasour din ya bude bakinsa sai ga wata kujera a can cikin bakin nasa tare da wani mariki daga gani kasan cewar wannan marikin dashi ake tukin wannan dinasour din nan take sai ga bakin dutse mai launin hayaki ya baiyana agaban malik koda faruwar hakan malik bai kara Sanin inda Kansa yakeba ya bungire da bacci kawai sai gani mukai hayakin jikin dutsen ya daga gangar jikin malik ya kaishi cikin wannan dinasour din wajen wannan kujerar take itakuma dinasour din ta koma yadda take sannan ta rufe bakin koda ganin hakan sai noor ta fara komawa da baya tana buya abayan Abdul wai ita tsoro Abdul ne yace menene kuma ina zumudin zuwadin yake futo mana karki bada mata hhhhha mayah ta fara dariya tana mai cewa ai daman haka take dason ganin Abu ga kuma tsoro to ahaka zakiyi yakin da dakarun aljanu da matattu huuum nadema jin tsoron ma ni kunga tafiyata wannan pink din ne nawa nan taje kusa da pink din abunda ya faru da Maliki itama shi ya faru da ita bayan ganin hakane Abdul shima yaje wajen Jan dinasour nafisa taje yellow mayar taje wajen ja amma wani abun mamaki duk dinasour din da su mayah suka hau to masu fukafukai ne sabanin na Abdul da malik kafin wani lokaci sai wajen yay tsit bakowa awajen sai aya da ayu da kuma jarimi halanchal a wannan lokacinne najib sawiris ya futo ya samesu a wajen wannan dinasour din bayan ya tambayi yar"yansa an bashi amsa sai kuma jarimi halanchal yay garan murya yana mai rusunawa wa najib sawiris yana mai cewa sakon sarki akeem yace na sanar daka cewa ba za,aje filin yaki da kai ba amma da akwai Tai makon da zakai. To ina jinka malam najib sawiris yace wa jarimi halanchal, wannan jarimi halanchal ya ce gaba da cewa da akwai wani katon robot da aka kera dominka Wanda kana daga gida zaka ringa juyashi kuma shi bada komai akejuyashi ba saida tunaninka dashi kawai zaiyi amfani lokacin daka shiga cikin dakin da ake control din robot din to ruhinka zai tafi jikin robot din gangar jikinka ce kawai zata zama,anan amma hankalika da komai yana can to ai ni bansan yadda yan ringa sarrafashi ba? inji najib sawiris yace jarimi halanchal ne yace kamar yadda zaka iya daukan huka kai yaki ko bunduga haka zaka gani baban banci kuma da akwai irin wannan robot din har guda Dari biyar koda an lallata daya to wani ne zai bayyana bazama kasan wani ya bayyana ba domin da zarar wani Abu yazo Wanda yafi karfinsa to a dai dai nan robot din zai mai dawa Dan uwansa ragamar abun. ya kamata muje mu kwanta domin dare ya raba gashi gobe futar safiya zamuyi eh haka ne inji najib sawiris yana me hucewa dakinsa anan shima jarimi halanchal ya yi musu saida safe ya tafi dakinsa aya ce ta kalli Dan uwanta ayu kana tace ya ayu ba zamu kara samun ilimiba kuwa acikin wayan nan duwatsun dinasour din me zai hana mu hada karfi mu shiga cikin hankalin su Abdul muma mu Debi wani ilimun tunda kaga muma ba wai yaki muka iyaba kawai dai karfin ne tsantsa a jikin mu eh haka ne yar uwa to amma kin manta baba kafin ya mutu ya hana mu shiga cikin tunanin kowa inji ayu ,aya ta kara cewa amma ai wannan ai da daliliko ba haka kawai zamu shiga ba to shikkenan taso mu shiga tawowa tayi kusa da shi suka zauna a kasa sannan suka kalli juna hade da tankwashe kafafuwa sannan suka rufe ido take wani irin haske Wanda ban San sunansa launin hasken ba ya zagayesu Jim kadan sai gasu suna tashi cikin iska kafin wani lokaci sun zama iska sun shige cikin wayannan injinan dinasour din wannan shine abunda ya fara bayan su Abdul Maya da nafisa da malik da noor sun kwanta bacci acikin robot din dinasours din su...................................................... idan muka koma bangare su bokanya zarishat kuwa lokacin da suka zo wata mararraba wacce zata sadasu da kofar da zata kaisu zuwa birnin Khufu take sai Hindu ta daga hannunta take wayannan dakarun aljanun da matattu suka tsatstaya sannan ta juyo ta kalli bokanya zarishat tana mai risinawa kana tace daga nan zuwa kogon da kofar birnin Khufu take babu nisa to amma wani tunani nai mu raba kan mu gida biyu rabi subi ta nan rabi su shiga ta sihitacciyar hanyarda aliens din Jupiter suka taba bi mu ukune kawai mukasan wannan hanya banda mu bana zaton wani yasan hanyar ya ke bokanya zarishat in ba damuwa nida aljani ra'asu da dakarunsa zamu bi ta waccen hanyar inyaso Ku kushiga ta nan ta yadda zamusa su a tsakiya Dan Jim kadan bokanya zarishat tayi sannan tace to shikkenan sai mun hadu a filin yaki alokacin dakarun bokanya zarishat suka bita na aljani ra'asu suka tsaya saida su bokanya zarishat da suzaina suka bace sannan Hindu da aljani ra,asu sukabi wata hanya daban koda suka fara tafiya sai hira ta barke tsakanin azzalimun sarkin aljanu ra'asu da Hindu shin Hindu wacce hanyace zamu bi nidai asanina ban San da wannan hanyarba, eh daman bazaka sani ba dalilikwa shine mu uku ne kawai mukasan hanyar a doran kasa ankirkiri hanyar ne bayan muhaifin mu marigayi sarki birnin Khufu aljani mankas ya shiga birnin na Khufu bayan shekaru masu yawa ne was aliens da suka shigo duniyar nan suka kirkiri wannan hanyar da ilimin su tunda suka kirkireta ba Wanda yake ganin wannan hanyar inba tsatson sarki Khufu ba ko kuma tsatson aljanu mankas baza mu taba Sanin hanyar ba har sai munkai cikin duniyar Jupiter sannan ne zamu sami hanyar saboda hanyar hanya ce wacce akayita da ilimin zamani inba kasan wani Abu acikin lamarinba zaka ka dauka kamar ta tsuniya ake fada maka, ni kina bani mamaki ace ke tsatson aljani mankas ce amma ta yaya kika gujisu kika hada hannu da abokan gabarku kinsan duk zaluncina ba zan guji yan uwana ba abunda aljani ra'asu ya fada kenan ita kwa Hindu yin shiru tai yayinda suke tafiyar, can kuma sai tace nasan abunda baka sani ba kawai kabini in ba sokake rahiwarka ta salwanta ba kabar zancen nan na nemoka ne don nasan indai baka tawoba to indai bokanya zarishat ta sami nasara akan aikinta to zatazo har inda kake ta kasheka dalilin abunda yasa na biyo damu ta yankinka kuma karo na biyu ina baka shawara duk abunda zai faru kayi shiru da bakin ka nan aljani ra'asu ya fara tunani yana mai nazari daga baya yace ba komai ai nasan ke wacece kuma nasan duk rintsi ba zaki kaini halaka ba nan bokanya Hindu tayi murmushi sannan tace da shi sai mun kara sauri in ba haka ba mu bata lokaci domin tafiyar wata biyu ce agaban mu amma inaso muyi ta a kwana biyar shine dai dai lokacin da bokanya zarishat da tawagar ta zasu isa cikin birnin Khufu ina mai umartar ka daka cewa yaran ka su kara sauri don mu isa da wuri koda bokanya Hindu ta zo nan azancenta sai tai shiru sannan shikuma aljani ra'asu ya bawa yaransa umarni su kara karfin gudunsu nan kwa suka kara baje ragowar fukafukansu nan suka fara gudu cikin iska kamar tauraruwa mai hutsiya, wannan shine abunda ya faru abangarensu bokanya Hindu da sarki aljani ra'asu....
...........................,........,.....,,..idan muka koma bangaren su bokanya zarishat kuwa tunda suka shiga cikin wanna. Kogon dutsen da kofar da zata sadasu da burnin Khufu take sai bokanya zarishat ta fara karanto wasu karatun tsafinta tana mai wani irin Abu da hannayanta take sautin muryarta yadau amo acikin kogon nankwa ilahirin cikin kogon ya fara girgixa hadi da wata irin kura nankwa waje ya hargitse amma duk wannan abunda ke faruwa dakarun bokanya zarishat ba abunda ya faru dasu hasalima duk abunda ya tunkaro su to take yake konewa, byan wani Dan lokaci sai bokanya zarishat tayi shiru, alokacin da wannan kofar ta fara bude kanta bayan ta gama bude kanta ne bokanya suzaina ta bawa dakaru. Aljanun da matattu dama dasu kunna kai cikin wanna. Kofa kan tagama rufe baki tuni sun face zuwa cikin wannan kofar sai bayan sun gama shiga sannan kuma bokanya zarishat da suzaina suka shiga faruwar hakan keda huya kofar ta kara rufe kanta wannan shine abunda ya faru dasu bayan sun rabu da bokanya Hindu da aljani ra'asu ................................................................idan muka koma bangaren su aya kuwa lokacin da suka shiga cikin wanna injinan dinasour din sai suka tsunci Kansu acikin wata faffadar alkarya mai yawa mutane ga kuma irin injinan dinasour din nan awajen mutane kowa na harkokin sa anan ne suke hango su Maya Abdul da malik da nafisa da noor wajen wani tsowo yana musu bayani akan wayannan duwatsun da akabasu na dinasour din nan koda muka ga haka sai muka karasa wajen muna masu sauri don ayi damu koda muka karasa sai mukai musu sallama bayan sun amsa muka ci gaba da sauraron ilimin abunda ake koya musu Abu kamar wasa basai gashi muna koyar abunda ake koya mana kamar Shanruwa bamu dau wani lokaci ba aka kai mu wani daki bayan an bamu wasu manyan kaya munsa daga haka kuma sai aka kai mu cikin wannan dinasour din kowa ya shiga irin nasa su aya da ayu kuwa sai suka yi salonsu ta hanyar komawa suffar dinasour din suma aya fari ayu kuma Green bayan sun gama shiryawa ne sai suka ji ana yi musu magana cikin naurar sauraro ana mai cewa Ku zama cikin shiru saura second biyar kacal nan kowa ya saita injinan dinasour din sa ya shirya duk da cewa su Kansu basusan inda za,a kaisuba faruwar hakan keda huya sai ga wata katuwar kofa ta bude koda na leka wajen kofar wani katon filin yaki ne Wanda iya kallonka bazaka ga karshen sa ba koda muka futa wajen filin ba abunda kake gani ko ji tsit wajen yayi aya da ayu ne atsakiyar su cikin suffar dinasour din sai kuma gefe da gefe malik da Abdul sai nafisa da Maya sai kuma noor da suka sata atsakiya malik ne ya yi musu magana cikin naurar sadar wa yace Ku shirya fa na'urar dinasour dina na nunamun cewa wani Abu na tunkaro mu eh nima na gani inji Abdul wasu dakarun girdagirdan dodan'nine suka tawo sai mu shirya inji ayu nankwa dukkaknsu suka kara gyara tsaiwarsu sannan suka futo da wata sharbebiyar huka a hannunta suna dama hannu na hagu kuma wata irin bunduga ce ajiki mai aman farin haske memakon bullets kafin wani lokacin tuni wayannan dodannin sun zagayesu tsayawa fasaltama kaman'nin dodan'nin'nan ma bata lokacinne domin suffofinsuma abun tsorone mai karatu kawai ka siffanta kamannin da kanka noor ce tace ya kamata tun kafin su cin mana mu fara mataki na farko OK inji malik yana mai daga hannun sa kana yacewa Abdul daya shirya nan suka shirya sannan ya cewa Maya ta matsa kusa da Abdul saman sa tunda NATA tsuntsune ita kwa noor sai yace mata data tsaya gefensa nafisa kuma tana tsakiyar su malik ne ya kara da cewa nafisa ke zaki kula damu ke zaki ringa bamu umarnin yadda zamuyi nafisa ce tace to koda gama fadar hakan sai kawai suka ga dunbin dodanninnan sun afka musu nan kwa nafisa ta fara aikinta nabada umarni akan wayannan dodannin cewa tai a sakar musu huta nankwa suka fara sakar musu huta saida suka kashe dubunnan su amma kamar karasu akeyi a dai dai wannan lokacinne nafisa tace dasu mataki na biyu wukar zarto nankwa dukkansu suka danna mabudin hukar zarto nankwa saigata ta futo tana juyawa kamar injin yanke bishiya sannan tace a afkamusu Maya da noor Ku kuma Ku ringa yin anfanida naurar bacewa kuringa ya karsu a boye nan suka amsa tare da cika aiki suka boye Kansu nan suka afka musu kawai sai dai kaga kawukan dodannin na zubewa kasa amma ka rasa ta ina su noor da Maya suke wannan aikin kamar wasu shaidanu suka koma bangaren su malik da Abdul ma haka kawai cin uban dodannin suke duk da suma dodannin suna sukkansu amma lahanin da sukewa dodannin yafi na su a bangaren su aya kuwa suma ba karamin dukan maza sukeba don idan kaga aya anan to kafin kibtawar ido zaka ganta a can gaba haka shima ayu duk kuma suna wannan gumurzu ne cikin siffar dinasours dinan sai dai su basa amfani da bunduga sai dai wata irin iska mai karfi dasuke busowa duk Wanda ya gagaresu Filin yakin ya hargitse da gurnani dodannin kashesu ake amma kamar karuwa suke a dai dai wannan lokacinne nafisa tace mataki na ukusautin kisa nan take dukkansu suka dannan matakin sautin kisa adai dai wannan lokacinne aya da ayu suka rufe kunnuwansu da karfinsu sannan suka ci gaba da gumurzu kankace me tuni ilahirin wajen wani irin sauti mai rikitarwa ya mamaye wajen take sai dai kaga kahukan dodannin nan suna farfa shewa sanadiyar wannan karar mai rikitarwa koda dodannin'nan suka ga haka sai suka tsaya da yaki suka fara rufe kunnuwansu Dan gudun mutuwa a wannan lokacinne nafisa ta kara cewa Ku shiga mataki na hudu ruwan kibiyu nan kwa suka danna madannin ruwa kibuyu take bakunan dinasours din suka bude sai ga wasu injina masu aman kibiyu nan take kwa injinan suka fara aikinsu kan kace me tuni sun kashe fiye da rabin mayakan wajen yazamana ragowar dodannin basu wuce Dari biyu ba a wannan lokacinne ragowar dodannin nan zuciyar su ta fara tafarfasa fuskokinsu suna gatsine idanuwansu ya kara ja nan take suka fara hade hannayensu waje daya faruwar hakan sai gasu suna shigewa jikin juna suna hade gan gar jikinsu waje daya kan kace me tuni sun zama katon dodo guda daya mai girman gaske duk da cewa dinasours din su Abdul manyane amma hakan baisa sun zama manya a agaban wannan garjejen aljanin ba komawa sukai kamar dan tsako a agaban shirwa koda ganin hakan sai zuciyar nafisa tabuga da karfi ba karamin tsorata tai ba cikin muryar tsoro tace ba zata iya cigaba da leading din su ba kawai su canjata nan kwa malik yace to kawai sai ya kalli Maya yace da ita mataki na biyar nan take kowa ya danna mataki na biyar faruwar hakan keda huya sai ga wayannan dinasour din suna hade Kansu kafin wani lokaci sun zama wani garjejen mutum mai irin girman katotan dodannan kafar dama Abdul ne kafar hagu malik daga cikin zuwa kafada da hannu nafisa ne da noor kan wannan katon mutumin robot din kuma dinasour din Maya ne kasan cewar a tsarin dinasours din babu su aya da ayu shi yasa koda suka juya suffar babban mutumin robot babu su acikin tsarin amma duk da haka sai ayu ya cewa aya su kara da karfinsu a jikin hannuwan wannan babban mutumin robot din nan take suka zama haske sannan suma suka shiga jinkin hannun take hannun wannan mutumin robot din ya kara kunbura sannan wasu irin kibiyu suka baiyana akai nan take wannan katon dodon ya kurma urban ihooo tare da yo kan katon mutumin robot din su Abdul koda ganin haka sai Maya tace muma mutun kareshi in ya tarar damu anan ba zamuji da dadi ba take kwa suka amsa sannan suka fara tafiyar da wannan katon mutumin robot din nankwa sai gasu suna gudu harda tsalle sai dai duk inda suka taka sai yayi wawakeken rami koda bai wuce taku goma su haduba sai kowannan su ya daka tsalle hadi da kawowa abokin gaminsa wawan naushi cikin kauciya da salo katon mutumin robot din nan ya kaucewa dukan wannan babban dodon tare da hada mai naushi faruwar hakan keda wuya sai ga dodon yayi sama loooooo kamar an wurga dutse sama kafin ya sakko kasa tuni babban mutumin robot din nan ya daka tsalle ya kara hadawa katon dodon naushi gami da bugu ta ko ina bayan haka ya shako wuyansa ya matse take dodan ya fara kakarin mutuwa faruwar hakan keda wuya sai wayannan dodon'nin suka war gaje suka koma ainayin siffarsu tada koda haka ta fara sai dukkan gawar wakin dakarun suka ringa murmushewa suna bin iska a dai dai wannan lokacinne aka fara kiran assalatu a cikin unguwar nan ta birnin Khufu anan ne dukkansu suka farka daga wannan nauyayyan bacci mai dauke da mafarkin fadansu da dodannin nan koda kowannan su ya futo daga cikin robot din dinasours dinsa jikinsu duk ba kwari alamar sun gaji ga wani gumi da suka hada a dai dai wannan lokacinne jarimi halanchal ya futo daga dakinsa kana yace dasu suje suyi alwalah suyi sallah, bayan sunyi sallane aka kawo musu abunci sukaci sannan jarimi halanchal yace dasu su je suyi sallama da malam najib sawiris don badashi zamu je filin yakin ba, bayan sunje sunyi sallama ne sai kuma suka koma cikin dakin robot din dinasours din su cikin shigar kayan yakin su kowannan su yasha riga kalar robot din dinasourd dinsa da wata wula da take kare ilahirin kan mutum da fuskarsa a wannan lokacinne jarimi halanchal yace dasu Ku zama cikin shiri kowa ya shiga cikin robot din dinasour din sa domin sarki akeem da tawagar sa sunyi gaba mu kawai ake jira a bayan gari nankwa suka shisshiga ciki suka saita komai sannan suka futo amma a sirrince kasancewa ba,aso kowa yasan meke faruwa agarin, jarimi halanchal da ayu da aya ma hakance ta faru a haka suka salallaba suka fuce daga garin suka hadu dasu sarki akeem suka ci gaba da tafiya yayinda suka bar malam najib sawiris acikin dakin masarrafar robot din sa amma duk abunda yake wakana yana gani ta jikin wani bongo dake jikin dakin, wannan shine abunda ya faru a birnin Khufu
YOU ARE READING
jinah matar aljan book2 ep1
FantasyThis story Its fantasy story abaut Devils who want destroy a wold