JINAH MATAR ALJAN BOOK2 EP 4 DAN KARIN BAYANI KUNE MEMU TA SHAFIKAN MU KO NUMBER(09037786636) EP4( N AND N) WRITERSASSOCIATION.................................................... Tunda malam najib sawiris yaji wannan abunda tace hankalinsa ya tashi domin kamar yasan wani abu game dasu haka yakeji acikin ransa eh tabbas yasan wani Abu domin tun lokacin mahaifin su na darai yace kar Aisha tai aure har sai ta cika shekara 40 saboda wani boyayyan sirri dake jikinta inkwa tai to duk abunda ta Haifa zaisha wahala bayan girmansa wahalar da sai sun gwammace sun mutu subar duniya yanzu dai mubar wannan zancen aya mutafi zuwa Giza pyramid don karasa aikin mu daga baya munyi wannan zance. yata zaki iya kaimu can ko murmushi aya tai sannan tace mai zai hana kuzo mu tafi mana OK malam najib sawiris yace to amma so nake mushiga aboye ba tare da ansan da shigar mu ba mai yasa? malik nassif sawiris ya tanbaya, saboda idan muka CE zamu je da sanun ma,aikatan wajen zasu bata mana lokaci kafin muje mu aiwatar da aikin mu kunga kuwa Bacin lokaci zai kawomana tangarda babba shine babban dalilin dayasa na zabi muje aboye OK kutawo mu tafi inji aya tana mai bude hannuwa, hannun nafisa ta rike nafisa itama tarike hannun Abdul shima ya rike hannun malik malik ya rike hannun mayah mayah tarike hannun noor noor tarike hannun babanta malam najib sawiris ba bats lokaci aya ta bace dasu zuwa cikin Giza pyramid suna bayyana kuwa nafisa ta kalli wajen sosai sannan tace ai da nan wajen nake yawan mafarki a dai dai waccan kofar nake farkawa kuma koda yaushe a rufe take amma yanzu naga kamar abude take sai da bayan tayi magana sannan duk aka kula tabbas wannan kofa abude take da sauri dukkansu suka shiga cikin dakin babu komai da alama ma an Dade da dauke abunda ke cikin ayace ta karasa wani waje da kana gani kasan da akwai wani abune awajen wanda aka dauke hannunta tasa akan Kasan wajen tare da rufe idonta nan ta fara ganin duk abunda ya faru awajen, gani sukai aya ta fara hada gumi sosai gashi kuma fuskarta ta Na nuna lallai da akwai matsala, ta dauki kusan akalla minti 15 tana daukan bayanai sannan ta tashi ta buds idonta awannan lokacin kwa ta hada wani mugun gumi jikin ta yayi wani sanyi jitai kawai ta kwanta zai fimata kawai sai gani sukai aya ta mirgina ta kwata akan iska tare da rufe idonta hankalin kowa ya tashi ganin aya acikin wannan halin har malam najib sawiris ya nufo wajenta sai sukaji aya tace Ku kwantar da hankalin Ku INA lafiya kawai na tafi Neman mafutane,nan ta kara yin'tsit nanma dai wajen yay tsit kowa da tunanin da yakeyi acikin ransa tsayawa akai ana sauraron ta tashi bayan wani dan lokaci aya tafi away daya akwance cikin iska sannan ta juyo ta tashi ta fuskance su duk Wanda ya kalli fuskar aya yasan ba lafiya,ayace ta kai kallonta kan malam najib sawiris tace dashi muna cikin tashin hankalin babba, wata bokanya mai suna suzairat tazo nan ta dauki akwatin gawar da bokanya zarishat take ciki kuma ta tafi da it' wani waje Wanda na kasa gane inane, bokanya suzairat tanason ta bude bokanya zarishat don ta tashi yayarta Hindu wacce nice ajalinta acikin binciken danayi na gani cewa bazamu ga inda bokanya suzairat take ba face har sai ta tashi bokanya zarishat tashin bokanya zarishat shine babban tashin hankalin mu don Indai ta tashi da Abdul zata fara don yana kama da masoyinta Wanda ruhinsa yana can wani gari mai suna birnin ruhanai amma yanzu anakiransa da birnin Khufu babban tashin hankalin shine yadda zamu Shiga cikin garin ban sani ba kuma bansan in dama za bi ba nasan dai birnin na dai dai border Nigeria and Niger anan wannan mysterious city din yake acikin sama yake garin zan iya kai mu had can amma yadda za,ai mushiga ba nasan ta yadda zamu'iya zuwa cikin garin inji Abdul fiye da shekara 3 baya na sami wani lttafi acikin pyramid din mei doom Wanda yake magana akan mysterious city din, sun bada sharidan yadda za mu iya shiga cikin birnin amma Marsala daya shine da,akwai wa yansu kalamai ajikin kofar shiga cikin garin kofar bazata bude ba har sai an karantasu kusani cewa India zamu karanta sau dubu indai ba mai irin muryar yan'uwan Khufu da yar'yan sa to kofar bazata bude ba hanya ta 2 ta shiga birnin dole sai jinin wani aljani mai suna mankas babban bawan bokanya zarishat iya budewa ta hanyar dugon jinisa saboda haka meye mafuta,wannan aikin nafisa ne, inji najib sawiris kowa ya dago kai yana kallon malam, eh aikinta ne dalili shine tana kama da kanwar Khufu hatta yanayin maganar ta don da akwai littafin Nima da nasa mu a Alexander Wanda ya fasalta irin kaman'nun su yadda suke magana da sauran su tayaya zan iya karan tawa alhalin ban iya karatun characters din misrawan zamanin Khufu ba najib sawiris yace wato yar'ta nafisa karki damu kinji kina da wani boyayyan al'amari Wanda da zarar kin je wajen kofar nan zaki iya karanta lafuzan da aka iya rubutawa a jiki girGiza kai tai duk da ba wani gamsuwa tai ba, ta ya za'ace zan iya karanta abunda ban koya ba Abdul yace yawwa acikin littafin da akwai taswirar yadda za,a shiga cikin birnin kuma shinyi gar gadi duk Wanda ya tunkari garin karyai anfani da karfinsa yabi umarnin kaidojin birnin itace hanya daya dazai iya shiga cikin garin lafiya Ahan'gena ya kamata yau mu gaggauta tafiya don mu isa cikin garin nan da kwana 3 tunda tafiya ce zamuyi ta cikin sihirtacciyar matattakalar benan da zamubi zuwa wannan mysterious city din kafin nanda kwana 5 idan bamu isaba to bokanya zarishat zata cin'mana. Malam najib sawiris yace wa aya ta debesu ta maida cikin library din cairo high school nan ta cika alkinta ta debesu ta maidasu, acan wani daki malam najib sawiris ya"umar cesu da su biyo shi,koda suka shiga cikin dakin sai suka ga ka yayyaki kala kala kama daga kan Boot da traveling bag da sauran abubuwa da zasu bukata malam najib sawiris yace dasu su dauki duk abunda suke bukata daga nan wucewa zasuyi ba bata lokaci malam ka bamu damar muyi wanka mu shirya muyi addu,a tunda bamusan ranar da zamu isa can musami kwanciyar hankali ba malam yace mayah kin tuna tarda ni da abunda na sha,afa saboda haka ke da noor da nafisa Ku zauna anan dakin mu bars muje daya dakin babu bata lokaci suka fara shiryawa basu dau wani lokaci mai tsayi ba suka kammala shirinsu sukai sallah sannan suka fito cikin shigar matafiyan kafa kowa da helping stick a hanunsa malam najib sawiris yace malik ka dauko littafin da taswirar take eh malik yace tare da dago hannunsa yace gashi nan OK to aya mutafi ko nan suka rirrike hannun juna itakwa aya ta debesu sai zuwa border Nigeria and Niger ............................................................................ Wannan shine abunda ya faru a birnin Cairo cikin library din high school , shin zasu iya shiga cikin birnin Khufu mysterious city nafisa zata iya furta rubutattun kalaman da suke kan kofar garin Abdul zai tsira daga sharrin bokanya zarishat kubiyo mu acikin cikin ci gaban littafin jinah matar aljan na 2 ep5
YOU ARE READING
jinah matar aljan book2 ep1
FantasyThis story Its fantasy story abaut Devils who want destroy a wold