terrified

28 4 0
                                    

JINAH MATAR ALJAN BOOK2 EP13 DAN KARIN BAYANI KUNE MEMU TA SHAFIKAN MU KO NUMBER(09037786636) EP13( N AND N)bari mu koma ban garensu Hindu kamar yadda bokanya Hindu ta fada haka abun ya kasace domin sai da suka kai duniyar Jupiter sannan suka dauki barauniyar hanyar da zata sada su da burnin Khufu ayayin da suke tafiya cikin mugun gudu na futar hankali basu tsagaita ba ko kadan wajen tafiyar su. idan muka koma ban garensu bokanya zarishat ma haka tafiyar tasu take domin basu tsaya ba har saida suka kai ga kofar burnin Khufu sannan suka tsaya nesa da ita sanadiyar wannan bakar guguwar datake kanannade da bakin kofar a dai dai wannan lokacinne bokanya zarishat ta fara yin aikinta na bokanci tana mai karanto wasu surutan tsafi tana maimaitasu cikin wani irin lafazi da nikaina bansan wanne yare takeyi ba faruwar hakan keda huya sai wannan bakar guguwar ta kara sauri wajen juyawa tana mai kara baki take wajen yakara hargitsewa yayi bakikkirin tsantsa ga wata walkiya da take wallawa gami da karar tsawa nankwa aka fara wani yayyafi, haka bokanya zarishat taci gaba da karanto surkullanta ana cikin hakane saiga wata irin jar walkiya ta wallah ta daki wajen kofar take wannan guguwar ta koma ja tana mai cinyewa da wuta adaidai wannan lokacinne kofar garin itama ta kone kurmus wannan shine abunda ya faru a bakin kofar burnin Khufu ..... Idan muka koma bangaren su aya kuwa koda suka is filing yakin ba'a fata lokaciba sarki ya bada umarni da a kafa tantuna tare da rufe tarkunan da'aka tanada nan take aka fara ai watar da duk abundant sarki akeem ya CE ayi a bangaren su jarimi halanchal kuwa tunda suka baro cikin gari suka bayyana Kansu koda sukazo cikin filing yakin ma sai suma suka koma gefe suna kara rihazal akan abunda zasu fuskanta koda aka gama rufe tarkunan na daban daban said sarki akeem ya bada umarni da ahau salon yaki kuma nan take mayakan kasa suka jeru tare da daukan wata garkuwar haske a hannunsu garkuwace wacce amma ilahirinta haskene jikinta, a mayakan sama ma abun haka yake domin wani irin jirgine mai suffar karamin tsuntsu kowannen su yake ciki jirgin ba irin namu bane domin fuka fukaine dashi masu kadawa kuma shi yana amfani da hankalinmutum ne bada controller ba dakarun saman wayanda sunkai su dubu ashirin dukkansu suna cikin irin wannan jirgin nasu masu suffar tsuntsu  a tsakiyar dakarun kasa kuwa sarki akeem ne da sarkin yakinsa da jarimi halanchal a gefen hagu da dama a bayan su kuma Abdul malik ne da Abdul da kuma ayu a gefe cikin robot din dinasour dinsu sama kuma ayace da Maya da nafisa cikin iska cikin robot din dinasour dinsu suma a dai dai wannan lokacinne sarki akeem yace wa jarimi halanchal ya koma sama ya tai makawa dakarun sama nan ya fude duka fukansa ya tashi sama, a ban gare su Abdul kuwa Abdul ne ya kunna na'urar sadarwa da ta hadashi da su Maya aya nafisa Abdul ayu malik da noor sannan ya fara magana yana mai cewa aya aya duk rintsi karkiyi nisa dasu nafisa da noor da Maya ki zame musu garkuwa to race,sannan yace noor ke kuma kikasance koda yaushe cikin kula to noor tace sannan ta kara da cewa wa zaiyi leading din mu Abdul ne yace malik ne zaiyi, tam tace ta juya ta kara gara zamanta tare da rufe kanta da wannan hular da muka fi kiranta da hular kwano hhhh komai yayi dai dai  kawai jiran karasowar bokanya zarishat kawai ake dakaru sama da dubu darine a filing yakin gefe da gefe sama da kasa a can gefe kuwa wasu makada ne suke buga wasu irin gan guna masu futarda sautin girma da darsa'tsoro a zuciyar abokan gaba ga wata irin sautin busa dayake futa na kakaki hmmm duk Wanda yaga mayakan burnin Khufu sai yayi mamaki domin ba'irin abun yakin da babu na zamani da nada duk da akwai, kai har abunda babu shima sun kirkira kawai don kare duniya daga sharrin bokanya zarishat adoran kasa, !dim !dim !dim wani sauti nake juyowa yayinda yanayin garin ya sauya hasken rana ya fara raguwa sanadiyar wani hadari da yake tawowa daga yammacin garin ga wata iska mai wucin zafi da take busowa wacce a tariyin garin babu irinta agarin da take busowa harda wani sauti da yake biyowa abun tsoro da fargaba dip! dip! dip! Takun dakarun aljanu da matattan bokanya zarishat yayinda suke tafiya yayinda suke haifar da girgizar kasa wani yayyafi akeyi na ruwan zafi tsabar tsafin bokanya zarishat da shaidancita adai dai wannan lokacinne bokanya zarishat ta tashi sama cikin iska ta fara kallon mayakan burnin Khufu tana mai dariyar mugunta da ta cika dodan kunnan mutanan wajen gaba daya Sannan ta fara magana tana mai cewa yaku mutanan burnin Khufu kuyi sani ba da fada nazo mukuba amma idan kuka ki bani abunda nazo nema to lallai zan yakeku nakuma yi abunda nai niyar yi, sarki akeem ne ya mayar mata da martani yana mai cewa zaki aiwatar da abunda kike sone in harkika sami sa'ar shiga cikin burnin Khufu, mu kuma indai Muna raye to bake ba shiga cikin wannan garin, koda jin haka sai bokanya zarishat ranta ya baci zuciyarta ta fara tafarfasa tana me cewa yakai! akeem Dan bawana aljani mankasa kayi sani ko ubanka! bai isaba balle kai, sarki akeem ne yayi dariyar yarda dakai sannan yace magana ma bata lokacice kawai gwada wa zakiyi, nantake tsabar Bacin rai wata irin walkiya ta ringa wallawa idon bokanya zarishat yayi ja kamar garwashi Nan take ta kalli bokanya suzaina itakwa bokanya suzaina ta kwallakara! tana me nuna dakarun burnin Khufu take dakarun matattu suka ruga da gudu suna gurnani suka tunkari inda su sarki akeem suke ragowar dakarun aljanun kuwa sai suka tashi sama suka farwa dakarum burnin Khufu na sama ita kuma bokanya suzaina tana kusa da bokanya zarishat, koda ya kasance bai huce saura taku hamsin su haduba kawai sai sarkin yakin burnin Khufu yace cikin muryar mai dauke da amoh! Yace ruwan wutaaaaa!! Take wani sadauki ya daka tsalle ya daki wani makunni, faruwar hakan keda huya sai ga wasu mashina masu aman wuta sun bullo daga cikin kasa take suka fara zubar da narkar kiyar wuta kanka ce me tuni wajen ya hargitse nankwa dakarun matattun bokanya zarishat suka ringa konewa sai da suka kone kurmus, suka dakarun aljanun kuwa wayanda suka yi kan su aya da sautan dakarun burnin Khufu na sama sai kawai suka ji ta ko ina ana harbinsu da wata bunduga mai aman wani farin haske da zarar hasken ya taba jikin aljani sai kaga yana zagwanyewa yana bun iska kafin wani cikakken lokaci sai ya zamana saura bokanya zarishat da bokanya suzaina kawai a filin wajen  nan take filin yaki yadau ehuuuuu dakarun burnin Khufu suna ta ehooooo,!!! rashin sani yafi dare duhu domin da sun San abunda zasu fuskanta nan gaba da basuyi wannan ehun ba domin koda bokanya zarishat ta Gara tsaiwarta sai ta daga hannunta sannan ta ringa juyashi ba tare da tace komai ba nan take kwa wata irin iska mai karfin gaske hadi da rugugin masifa ta ringa zagaya duk inda dakarun ta suka mutu faruwar hakan keda wuya sai ga wannan iskar tana yayewa ahankali ahankali harta yaye abun tsoro abun mamaki abun firgitarwa da hargitsar wa wowowo! Dumbin dakarun aljanu da matattu. Bokanya zarishat ne!! duk suka tashi cikin wata irin shigar yaki ta wasu irin kaya ruwan zinare irin kayan mayakan  misirawan zamanin da amma duk kawukan dakarun yanzu na mikiyane bana matattun mutane da aljanuba Hannayen su wasu irin makaman yaki ne daban taba gani ba girmansu ya ninja na da da kamu biyar nauyinsu da zafin namasu ya ninka da ko yaya wannan gumurzun zai kasance ka biyo mu acikin a final da zamu kawo inshaAllah .............................................................

 Bokanya zarishat ne!! duk suka tashi cikin wata irin shigar yaki ta wasu irin kaya ruwan zinare irin kayan mayakan  misirawan zamanin da amma duk kawukan dakarun yanzu na mikiyane bana matattun mutane da aljanuba Hannayen su wasu irin makaman yak...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
jinah matar aljan book2 ep1Where stories live. Discover now