*ABOKIN MIJINA*
*Na*
*Aisha Alto*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*Alhamdulillahi ina miƙa godiyata ga Allah daya bani ikon dawowa gareku da sabon novel ɗina. Yadda na fara lafiya ina roƙon Allah ya bani ikon kammalawa lafiya.*
*1*
*KADUNA*
_Malali Gra_
Zaune suke akan dinning table suna karyawa cike da farin ciki, ta debi dankali a cokali lokaci ɗaya tana aika masa da wani irin kallo mai cike da zallar so da tsantsar ƙauna ta nufi bakinsa dashi tana lumshe masa idanu cike da nuna shauki haɗe da tsantsar soyayya, ya buɗe bakin shima yana sakar mata wani ƙayataccen murmushinsa mai tafiyar da zuciya zata saka masa dankalin kenan acikin bakinsa wayarsa ta soma ringing, da sauri ya kauda kansa ya ɗauki wayar dake kan table agabansa yana dubawa, ganin mai kiran yasa da hanzari ya ɗauka lokaci ɗaya ya kara a kunnensa cike da ladabi yace "Morning sir...an tashi lafiya..." Ya faɗa tare da miƙewa tsaye, ɗan jim yayi kafin ya cigaba da faɗin "Yes...yes sir...insha Allahu sir, ok sir..." Ya ƙarashe faɗa yana kashe wayar. Galala kawai ta tsaya tana dubansa, kafin da sauri ta riƙo hannunsa ganin yana ƙoƙarin zaro tissue ya goge bakinsa, marairaice fuska tayi cike da shagwaɓa tace "Habeebi wai me naga kana shirin yi ne...Ba dai gurin aiki kake shirin tafiya ba tun yau...?" Ta ƙarashe faɗar maganar lokaci ɗaya tana tsaresa da ido. Ɗan janye hannunta yayi ya yagi tissue ɗin ya goge bakinsa ya juya yana faɗin "Ya zanyi Habeebti...? Tafiya ce ta kamamu yanzu zuwa Lagos, shine kika ji Ogana ya kirani..." Miƙewa tayi da sauri tana dubansa kafin lokaci ɗaya ta riƙo duka hannayensa tana kwaɓe fuskarta cike da shagwaɓa tace "Haba mana Habeebi...Haba dan Allah wannan wane irin abu ne haka...? Yau kwana huɗu da yin aure kawai saika tafi aiki har Lagos ka barni ni kaɗai a gida kamar mayya...Sai kace ba amarya ba...? Karka manta fa yau kwanan mu huɗu kenan da aure Habeebi amma kake shirin tsallakeni ka tafi wani gari ko gama cin amarcinmu ba muyi ba...?" Da sauri ya katse ta da faɗin "Nima ba laifina bane Habeebti, bada son raina hakan zata kasance ba...karfa ki manta soja kika aura, kuma kema kinsani a yadda nake ɗoki da muradin son kasancewa dake bazan iya tsallakeki haka kawai in tafi wani gari in barki ba...kema kinsan yanayin aikin namu dole sai kinyi haƙuri da wasu abubuwan..." Sake marairaicewa tayi lokaci ɗaya tana shigewa jikinsa tace "Haba ai kasan bazan taɓa iya sabawa da rashinka ba, yanzu tun ba'a je ko'ina ba daga yin aure ana neman a nisantani da kai ai dole zan nuna damuwata..." Ta faɗa yayinda lokaci ɗaya ƙwallah ke shirin zubowa daga cikin idanunta. Ɗago fuskarta yayi yana kallon cikin ƙwayar idanunta yace "Haba Habeebti karki damu...ai ga abokina Muhsin nan ko bani shi zai dinga kula da komai naki, zan bar masa kuɗi enough a hannunsa duk abinda kike buƙata sai ki gaya masa ya kawo miki...kinji..?" Ɓata rai tayi ta haɗe fuska tamau tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki da jin haushin kiran sunan Muhsin abokinsa da yayi, saboda ita tun asali fa dama ko alama tun lokacin da Farooq yake nemanta kwata kwata Muhsin bai taɓa yi mata ba, saboda ta lura da cewa ba halinsu ɗaya da Farooq ɗinta ba, domin ta ga take takensa ɗan iska ne shi na karshe in suka haɗu yay ta ƙureta da ido yana mata wani irin mayen kallo kamar zai lasheta, tun daga lokacin bata sakar mai fuska amma ta lura da cewa shi mijin nata baida wani amini kuma aboki da yake ji dashi irinsa, abun yana matuƙar bata mamaki amma sai bata nuna ba saboda tasan tun lokacin da Farooq ɗin yake nemanta komai take buƙata Muhsin ɗin ne yake kawo mata, abun yana masifar ɗaure mata kai ko dan ya taso a gidansu shi kaɗai ne bai da wani ɗan uwa..? Muhsin ɗin ne kaɗai abokinsa tare suka taso tun suna ƙanana. Cike da takaici ta kallesa tana faɗin "To ai ba Muhsin nake aure ba, ba shi bane mijina, ni kai nake aure kuma kaine mijina saboda haka karka bashi komai duk abinda zaka bar min ka bani kawai zan iya yiwa kaina komai ba sai kasa wani yayi min ba..."