*ABOKIN MIJINA*
*Wattpad: Aishaalto09*
*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*
*31*
A kiɗime ya miƙe tsaye jiki na rawa saura kaɗan ya wurgar da Aarif dake kan jikinsa saboda tsabar tashin hankali da firgici kafin cikin tsananin tsoro da karkarwar jiki ya kwantar dashi a kan kujera kana lokaci ɗaya ya ɗago ya nuna Khadija yana girgiza kai yace
"A'a bake ba! Bake ba!! ina Fa'iza...?..ni Fa'iza nake nufi bake ba!!!..."
Ya faɗa cikin tashin hankali da rawar jiki yana kallonta.Ita kuwa Khadija cikin tsananin shauki da Ƙauna ta fara takawa tana tunkararsa fuskarta ɗauke da kyakkyawan murmushi tana faɗin
"A'a dan Allah karka ce ina take...ai ni kake so kuma nace nima ina sonka zan aureka na amince a ɗaura mana aure yanzu yanzu..."
Ta ƙarashe maganar tare da ƙarasawa gabansa ta tsaya ta ƙura masa ido ƙirr tana ƙare masa kallo lokaci ɗaya kuma tana sakin wani murmushi mai nuna zallar shauki da ƙauna.Wani irin mugun tashin hankali ne lokaci ɗaya ya ziyarci Muhsin wanda a take ya rasa ya zaiyi duk ya ɗimauce ya juya da sauri zai fice daga falon aiko Khadija na ganin haka tasha gabansa ta tare hanyar tana wani kashe ido tace
"Wai ina kuma zakaje...? Dan Allah ka tsaya mana nifa aure kawai za'a ɗaura mana sai mu wuce abun mu...."
Ta faɗa da dukkan gaskiyarta kana tana sake matsawa gabansa kamar zata faɗa jikinsa.Wani matsanancin bugawa ƙirjinsa yayi yayinda ya fara ɗaga ƙafa a hankali ya fara yin baya yana kaɗa mata kai lokaci ɗaya yana faɗin
"A'a pls Khadija ni kam ba dan ke nazo nan ba, saboda Fa'iza kaɗai nazo. Kuma ni ita nake da muradi ba ke ba.
Dan haka a bakin Fa'iza nakeson jin waɗannan kalaman ba a bakinki ba...pls kiyi haƙuri ki fita na roƙeki dan Allah...."
Ya faɗa cike da tashin hankali kafin ya fara ja da ba da baya, inda yana ɗaga ƙafa itama Khadijan zata ɗaga tata ta bishi yana baya tana binshi da haka suka kai har gurin kujera bai ankara ba yana yin baya ya afka saman doguwar kujera tayi kansa gadan gadan zata faɗo masa da sauri ya zame ya faɗo ƙasa yana zaro idanu kana da hanzari ya sake miƙewa a firgice yana kallonta, itama zuba masa nata idanun tayi tana kallonsa kafin ta miƙa hannu tana ƙoƙarin riƙo nasa hannun cikin shagwaɓa tana faɗin
"Ni dai a'a ka daina bana so, ka daina kira min sunan wata ni kaɗai zaka aura...kuma ni kaɗai na isheka..."
Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana turo baki.Sake matsawa yayi da sauri yana zaro ido yace
"Nifa bake nake nufi ba Khadija kiyi haƙuri yayarki Fa'iza nake so in aura..."Aiko ta matsa da sauri tana zaro mai ido tace
"Aiko wallahi ni zaka aura..."
Ta faɗa a zafafe tana kallonsa.Shiko Muhsin wani mugun tashin hankali ne ya sake dabaibayesa yaji gabaki ɗaya jikinsa ya ƙara ɗaukar rawa da kakkarwa yayinda a gefe guda na cikin ransa kuwa faɗi yake.
Lallai yau ni Muhsin na tabka babban kuskure kuwa a rayuwata, kuma yau itace ranar nadama mara amfani a gareni wacce tun da nake ban taɓa zato ko tsamanin zuwan wannan ranar a gareni da gaggawa irin haka ba.Ganin Khadija na ƙara tunkarosa ne yasa ya matsa da sauri yaja da baya yana faɗin
"Dan girman Allah kiyi haƙuri Khadija nace miki ni yayarki Fa'iza kawai nakeso in aura bake ba. Dan Allah ki ƙyaleni haka..."
Ya faɗa yana haɗa hannayensa guri ɗaya alamar roƙo kana ya nuna mata ƙofa lokaci ɗaya cikin kwantar da murya yana faɗin
"Pls kije ki kira min Fa'iza ni ita nakeson gani bake ba dan Allah ki taimaka ki tausaya min pls Khadija..."Cikin hanzari Khadija ta wani cakumosa ta haɗasa da jikin bango ta matsesa kana lokaci ɗaya ta zazzaro idanu cikin wata irin murya tace
"Wallahi baka isa ba ni kakeso kuma ni zaka aura dolenka..."
Ta faɗa tana shaƙo kwalar rigarsa ta fizgosa da ƙarfi kana ta sake maidashi da baya ta bugasa da jikin bangon cikin haki tana faɗin
"Kuma idan ka sake kiran sunan wata anan kace ita zaka aura wallahi saina kasheka..."
Ta faɗa da dukkan gaskiyarta.