*ABOKIN MIJINA*
*Wattpad: Aishaalto09*
*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*
*32*
Cikin sanyin jiki Muhsin ya fita daga gidan ya shiga motarsa.
Ya daɗe zaune a cikin motar ya haɗa kai da sitiyari yana sauke numfarfashi kafin da ƙyar ya aro jarumta yayi ƙoƙari ya kunna motar ya tadata yaja ya fara tafiya sannu a hankali a hankali yana kallon layin da haka har ya fita daga cikin unguwarsu Fa'izan ya hau kan babban titi sosai yana murja sitiyarin a hankali kamar wanda ke tausayinsa.Tunda ya ɗauki hanya tuƙi kawai yake yana sharara gudu wanda kana gani kasan ba a hayyacinsa yake ba.
Gabaki ɗaya hankali da natsuwa da tunaninsa sunyi ƙaura daga gangar jikinsa babu abinda yake iya tunanowa yake kuma kallon faruwarsa kamar a lokacin yake wanakan sai badaƙalarsa da Khadija a gidansu Fa'iza da yadda iyayensu suka fito suka taddasu a wannan halin da maganganun da Fa'iza da mahaifinta suka dinga gaggaya masa.
Sai tona asirin kansa da yayi da bakinsa ba tare da wani ya tambayesa ba ballantana yace matsa masa akayi ya tona asirin da kansa, shima kawai tsintar kansa yayi da faɗar abubuwan da ya aikatawa Farooq ɗin da Fa'iza wanda yaji a lokacin idan bai faɗa ba kamar zai mutu saboda wani irin zafi da zuciyarsa ta dinga yi tana mugun bugawa kamar zata faso ƙirjinsa ta faɗo ƙasa.
Wannan abun shine babban abun kunyarsa da tozarci wanda ya taɓa cin karo dashi a rayuwarsa wanda kuma koda a mafarki bai taɓa hasaso faruwarsa a garesa ba.Tabbas sai yanzu ne yake ƙara daya sanin jefa kansa a halaka da yayi da biyewa sharrin mummunar muguwar baƙar zuciyarsa mara lissafi da tunani. Kuma sai yanzu ne yake ƙara tuna alkhairi da tsantsar halaccin da Farooq yayi masa a rayuwa.
Wanda ko kaɗan Farooq bai cancanci irin wannan mummunar sakayyar daga garesa ba.Farooq ya ƴantasa, ya ɗaukakasa, ya ɗaga darajarsa ya inganta rayuwarsa ya fifitasa sannan ya kyautata rayuwarsa daga mummuna izuwa kyakkyawa.
Farooq bai taɓa bambanta kansa dashi ba, haka itama mahaifiyarsa duk abinda zata yiwa Farooq ko mene shi sai tayi masa ko dai-dai da rana ɗaya bata taɓa bambanta tsakaninsa da Farooq.To wai me Farooq yayi masa ne da muni har da yaga ya cancanci ya aikata masa haka..?
Karaf kuwa wata kyakkyawar zuciyar ta bashi amsa da faɗin
"Tsabar ƙyashi da hassada ne kawai da mugun nufinka akansa sune suka dinga gwada maka nasabarsa da kyaun halayensa da ingancinsa har hakan ya ɗarsa baƙin ciki da hassada da mugun ƙulli a zuciyarka..."Saurin katse tunaninsa yayi yana sauke ajiyar zuciya kana yana ci gaba da tuƙi lokaci ɗaya a fili yana faɗin
"Yanzu kuma shikenan na gama la'anta rayuwata...?
Na zubar da kima da mutuncin kaina a gurin waɗanda suka ɗaukeni halattacen mutum mai gaskiya da riƙon amana sannan suka maida rayuwata cikakken mai ƴanci da daraja suka bani duk wani nau'i na jin daɗin rayuwa kana suka fifitani...?
Yanzu ta ina zan fara a ina kuma zanga Farooq..?
Da wane irin ido zan kallesa...?
Mezan gaya masa wanda zaisa ya yarda ya ƙara amincewa dani ya ci gaba da zama dani...?
Idan naga Farooq na roƙesa yafiya ya yafemin anya mahaifiyarsa kuwa zata amince ya ci gaba da tarayya dani...?
To taya ma zan iya roƙarsa garafa..?
Zan kalli cikin idanunsa ne ince Farooq ka yafemin sannan in gaya masa duk abinda na aikata masa da neman matar aurensa dana dinga yi ko kuwa na roƙesa nace ya yafemin sannan na gaya masa cewa nayi masa asiri na mallakesa ko kuma roƙarsa gafara kawai zanyi ba sai tare dana gaya masa cikakken abinda na aikata masa a rayuwa ba...?"
Haka dai Muhsin yay ta surutai shi kaɗai kana lokaci ɗaya kuma yana ci gaba da zuga gudu akan kwalta.A can Kano kuwa cikin sanyin jiki Hajiya Nazifa da Momynsu suka kama Khadija wacce keta birgima a ƙasa har lokacin tana ihun kuka tana faɗin
"Ni dai Abba ka ɗaura mana aure...dan Allah nace zan auresa ka ɗaura mana aure ka daina korarsa wallahi idan ya tafi zan mutu..."
Nan suka kakkamata tana tirje tirje tana ihu suia shiga da ita cikin falo.
Hajiya Umaima da Alhaji Bukar na biye dasu a baya.