*ABOKIN MIJINA*
*Na*
*Aisha Alto*
*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*
*2*
Ya daɗe a zaune sake da baki yana bin ɗakin data shige da kallo kafin ya gyaɗa kai cike da jin haushi ya dangwarar da gorar ruwan data kawo masa ya miƙe tsaye yana jin wani kalar sabon ɓacin rai na sake mamaye masa zuciya ya fice daga cikin falon ya faɗa motarsa ya figeta maigadi ya buɗe masa gate da sauri ya fice daga gidan da mugun gudu.
Tana kwance akan makeken gadonsu da yaji shimfiɗu da lafiyayyen zanin gado mai laushi da taushi taji fitar motarsa. Wani dogon tsaki taja lokaci ɗaya tana gyara kwanciyarta a fili tace "Allah ya raka taki gona...ina dalili kawai dan kana matsayin abokin mijina zaka nemi ka sakoni gaba da shisshiginka ka hanani sukuni, duk shisshiginka dai dole kayi ka ƙyaleni da mijina tunda ba kai nake aure ba...haka kawai kana neman ka hanani sukuni da mijina, duk kabi ka shisshige masa kayi bake bake ka tare komai kanaso ka hanani rawar gaban hantsi, duk abinda zaiyi dole sai da yardarka yake yi...kuma munyi auren ma bazaka barni in huta a gidana ba...? To wallahi bazan iya ba dan ni Umar Farooq nake aure ba Muhsin ba...atoh..?" Ta ƙarashe maganar tana hararar ƙofar bedroom ɗin nasu kamar Muhsin ɗin ne a gurin. A haka tana wannan surutan har bacci ya kwasheta.
★★★★
_Unguwar K/Mashi_
A ƙofar wani ɗan madaidaicin gida mai ɗauke da ƙaramin baƙin gate Muhsin ya zuba horn maigadinsa Isuhu yazo da gudu ya wangale masa gate ɗin ya sulala motar ciki yayi parking a ɗan madaidaiciyar harabar gidan nasa da yake fayau, ya ɗan jima zaune a ciki ba tare daya kashe motar ba, sai zuwa can ya buɗe ya fito bayan ya kashe motar ya fito riƙe da makulli da wayarsa a hannu ya nufi cikin gidan.
Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga cikin falon gidan nasa, matarsa Jamila dake zaune taci uban kwalliya cikin wani leshi ja ɗinkin doguwar riga tayi kyau dai-dai iya nata ba laifi, tana riƙe da remote a hannunta tana canza tasha, jin sallamarsa yasa ta tashi da gudu ta nufesa tana washe masa bakinta da yasha jan janbaki take faɗin "Oyoyo My Darling..." Ta faɗa cikin wani irin salo lokaci ɗaya tana faɗawa jikinsa, kaucewa yay da sauri kana ya janyeta a gabansa ya ɗaure fuskarsa tamau ya shiga binta da wani wulaƙantaccen kallo yana taɓe bakinsa, ɗan tsayawa tayi jim tana dubansa kafin ta shiga duban jikinta lokaci ɗaya tana ƙarewa kanta kallo, yayinda zuciyarta take cike da tsantsar mamakin irin wulaƙancin da yake mata. Ƙara matsawa tayi gabansa tana ƙaƙaro murmushi ta miƙa hannu zata riƙo hannunsa, da sauri ya ɗaga mata hannu kana ya raɓa ta gefenta ya nufi ɗakin baccinsu yana danna wayarsa.
Sakin baki kawai tayi tana binsa da kallo har ya shige ya rufo ƙofa ta kasa ko motsawa sai ma wasu hawaye da suka fara taruwa a cikin idanunta lokaci ɗaya suna ƙoƙarin zubowa. Wannan wane irin abu ne..? Haba! mutum ya zama kamar dutse gabaki ɗaya ta rasa inda ya dosa ta rasa meye nufinsa akanta, shekararsu ɗaya kenan da aure suna zamansu lafiya, amma a cikin wata huɗu zuwa biyar gaba ɗaya ya canza mata ta rasa meya canza shi lokaci ɗaya ya zama haka..? Ada komai tayi tana burgesa amma a yanzu komai tayi sai dai ya hantareta ko yayi ta kyararta ko agaban waye.
A kullum in har zata yi masa kwalliya sau dubu bazai taɓa yabawa ba sai dai ya kushe koya hantareta, saɓanin da da komai idan tayi zai dinga yabawa yana ƙwarzantata, amma yanzu duk abinda tayi yace bata iya komai ba, duk ɓata lokacin kuwa da zatayi gurin tsara masa kwalliya dan ta faranta mai bazai taɓa yabawa ba, asali ma sai dai ya kushe ko yayi ta farfaɗa mata maganganu ko yace bata yi kyau ba babu abinda ta iya sai rawar kai, ta rasa inda yasa gaba, ita kam har ga Allah ta fara gajiya da irin wulaƙancin da Muhsin yake mata, kawai idan ya gaji da zama da ita ne ya sawaƙe mata ta koma gidansu, amma ita wannan wulaƙancin ya fara isarta.