*ABOKIN MIJINA*
*Wattpad: Aishaalto09*
*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*
*Ina matuƙar godiya sosai masoyana, hakika ina alfahari daku, ina matuƙar jin daɗin nuna soyayyarku ga wannan labari na ABOKIN MIJINA. Nagode ƙwarai masoyana na nesa da na kusa ina sonku ina ƙaunarku ina kuma ji daku. Ina muku Son So domin Allah.*
*15*
Itama Jamila abun ya bala'in baƙanta mata rai gashi tana tsoron tayi mai magana yayi mata tijara agabansu Fa'iza ya bata kunya, shiyasa tayi shiru ta kama kanta amma da sun haɗa ido sai tayi masa alama kan ya tashi su wuce gida, amma sai ya fuske ya ɗauke kansa yayi kamar bai gane abinda take nufi ba, gani haka yasa ta ƙara marairaicewa amma yayi biris. Can sai wata dabara ta faɗo mata da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga gurin tura saƙo ta rubuta masa.
_Dan Allah ka tashi mu tafi gida, baka ganin mun takura musu..?_
Ta tura masa kafin ta ajiye wayar ta duƙar da kanta saboda bata so su haɗa ido dashi, ballantana ya nemi ya tata mata rashin mutuncinsa dan bata so su raba abun faɗe a gidan mutane tunda tasan halinsa abun kunya ba damunsa yake yi ba.
Muhsin kuwa yana gama karanta saƙon ya ɗago kansa da sauri fuskarsa a haɗe yana watsa mata wani mugun kallo kafin yace "Ai sai ki tashi mu tafi tunda kin matsa..." Ko kafin ya gama rufe bakinsa Jamila har ta miƙe da sauri tana gyara zaman jakarta dake rataye a kafaɗarta lokaci ɗaya tana faɗin "Toh Fa'iza zamu wuce, saduwar alheri sai mun sake haɗuwa kuma..." Ta faɗa tana yin gaba da sauri.Cike da jin haushi Muhsin ya bita da mugun kallo, saboda ta ɓata mai tsarinsa dan ba haka yaso ba, yaso ne ace su kusan raba dare a gidan ta yadda idan suka tafi Farooq da Fa'iza ba zasu samu damar yin komai ba sai bacci, amma da yasan wannan iskancin Jamilan zatayi masa da babu abinda zaisa sukai har wannan lokacin a gidan, da tun da rana ya kwasheta sun koma gida. Haka ya miƙe a sanyaye ba dan yaso ba, inda gefe guda na zuciyarsa kuma yake raya masa ƙila Farooq zai ce ya dawo ya zauna, dan yasan ƙa'ida ne shima Farooq ɗin ba zai so tafiyarsa tun yanzun ba, saboda shi a gurinsa baiga wani dare da yayi ba, kuma yasan Farooq idan yaga ya ɓata rai ya nuna baya son tafiyar zai iya cewa su dawo su zauna sai sun gama hirar tukunna. Amma ga ƙarin mamakinsa sai yaga Farooq ɗin shima ya miƙe yana faɗin "Habeebti muje mu rakasu ko...?" Fa'iza ta gyaɗa masa kai kana ta miƙe ta riƙe hannunsa suka bi bayan Muhsin dan ita Jamila ta jima da ficewa abinta.
Tsaye a jikin mota suka iske Jamila wacce duk ta ƙagara su wuce su bar gidan saboda ta lura sosai suka takurawa su Fa'izan kawaici ne kawai ya hana basu nuna musu ba, amma kana ganinsu kasan a mugun takure suke, ita sai yanzu ne ma data ga yadda Fa'izan ta ruƙunƙume hannun Farooq taji wata uwar kunya ta ƙara kamata, ta ɗauke kai cike da jin mugun haushin Muhsin a ranta tace "Gaskiya rashin sanin darajar kai baiyi ba wallahi..."
Da ƙyar Muhsin ya tsaya sukayi sallama da Farooq, dan wani irin bala'in haushin Farooq ɗin yake ji, ya haɗe fuska tamau sai faman hura hanci yake yana muzurai, Farooq ya miƙa masa hannu lokaci ɗaya yana faɗin "Mun gode matuƙa aboki, Allah ya bar zumunci ya kuma ƙara haɗa kanmu, ina matuƙar alfahari da kai, dan kai ɗin na musamman ne har gobe kuma ina alfahari da kasancewarka shaƙiƙin aboki kuma amini a gareni, wanda nake jinshi tamkar ɗan uwana na jini..nake kuma matuƙar alfahari da samunsa da nayi a cikin rayuwata...." Ya ƙarashe maganar yana haɗe hannunsu guri ɗaya. Wani irin sanyi jikin Muhsin yayi, ya saki yaƙe kafin lokaci ɗaya yace "Nine da godiya ai abokina kaima kasan ka cancanci har fiye da hakan a gurina, nine kuma ya kamata in kiraka da na musamman saboda ka gama min komai a rayuwata, ta sanadiyyarka na zama cikakken mut..." Saurin rufe masa baki yayi yana faɗin "Nidai bana son irin waɗannan maganganun da kake faɗi aboki...kuje gida Madam ta gaji da tsayuwa sai mun haɗu goben idan Allah ya kaimu..." Ya faɗa yana ƙoƙarin juyawa kana yace "Toh Madam mun gode fa Allah yabar zumunci, Allah ya kaiku gida lafiya..." Jamila ta amsa da Ameen tana murmushi kafin ta ƙarasa ta rungume Fa'iza tana faɗin "Toh Fa'iza mun tafi sai munyi waya..." Ta gyaɗa mata kai tana ji kamar kar ta tafi, dan ita da kanta Jamilan ta kwanta mata sosai a ranta, kawai dai zaman Muhsin ɗin ne kwata kwata bata so a gidanta, amma in dan ta Jamila ne ita kaɗai bata ƙi ma ta kwanar mata ba.