Part 3

644 31 0
                                    

*ABOKIN MIJINA*

        *Na*

   *Aisha Alto*

*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*

*3*

Bin bayansa tayi da wata uwar harara kafin taja tsaki lokaci ɗaya ta koma ta zauna akan kujerar data tashi ta ci gaba da kallonta.

Har ƙarfe 3pm. Tana nan zaune a falon tana kallo, kafin ta tashi ta shiga bedroom ɗinsu ta ɗauko wayarta da nufin ta ƙara kiran Farooq taji ko zai ɗauka, ganin tarin misscalls ɗinsa rututu akan wayar yasa da rawar jiki ta shiga ƙoƙarin neman layinsa.

Dai-dai lokacin ya fito daga wanka kenan yana ƙoƙarin saka kaya kiranta ya shigo, da azama ya ɗauka yana sauke ajiyar zuciya yace "Haba mana Habeebti na...wallahi gaba ɗaya kin tsinka min zuciya gabana sai faɗuwa yake, na ɗauka wani abun ne ya samar min ke duk na kasa sukuni ji nake kamar in zama tsuntsu kawai in ganni a Kaduna...amma dana tuna akwai Muhsin a kusa dake wanda zai iya baki duk kulawar data dace kamar yadda ni zan baki, sai hankalina kuma ya kwanta shine na kirasa nace yaje ya duba min ke...ina fatan dai yazo kuma komai lafiya...?" Shiru Fa'iza tayi kawai tana saurarensa ta kasa ce masa komai, dan bata san ma me zata ce mai ba, saboda Allah ya sani ta tsani Muhsin ɗin nan bata ko ƙaunar taji yana dangantata dashi amma shi ya kasa ganewa ko magana ce suke a tsakaninsu dole sai ya sakosa a ciki, abun bala'in baƙanta ranta yake yi. Bata ƙara tsinkewa da al'amarin na Farooq ba sai data ji ya sake jefo mata tambayar data faɗar mata da gaba lokaci ɗaya taji zufa ta fara tsatstsafo mata a ranta tace "Anya kuwa Farooq mijin ƙwarai ne..? Wannan wane irin miji ne haka ta aura..?"
Kasa bashi amsa tayi kawai tai shiru.
Daga can ɓangaren kuwa Farooq dake saurarenta yaji shiru ya sake cewa "Habeebti...naji kinyi shiru..ko kuna tare ne da Muhsin ɗin, dan na kirasa bai ɗauka ba...?" Ɗaure fuskarta tayi tamau kamar yana ganinta tace "Wannan wace irin magana ce haka kake yi Habeebi...? Wane irin muna tare da Muhsin kuma sai kace wani mijina...?" Ƴar dariya yayi wacce har sai da ta jiyo sautinta a kunnenta kana yace "Amma ai aminin mijinki ne shi ko...? Kuma wanda mijinki ya yarda dashi ya aminta dashi har ya iya bar masa amanarki dan ya kula dake, tunda nasan komai kikeso ko kike da buƙata Muhsin bazai ƙi yi miki shi ba..ko mene ne shi kuwa...dan haka ni a ganina dan nace ko kuna tare ne ai ba aibu na faɗa ba ko...? Tunda dai ni da kaina na amince masa indai har yana da buƙatar wani abu a cikin gidana ko mene ne shi kuwa to ya shiga ya ɗauka, ban masa shamaki da ko'ina a cikin gidana ba, haka kuma komai dana mallaka indai nawa ne to ikonsa ne shima...saboda bani da wani amini makusanci irinsa..."

Lokaci guda Fa'iza taji wani mugun baƙin ciki ya turnuƙeta, ta runtse idanunta cike da takaici tace "Haka ne ba aibu bane Farooq dan ka faɗi haka...amma bana tare da Muhsin...ni kaɗaice..." Da sauri ya katseta da faɗin "Oh Habeebti sorry please...dan Allah kiyi haƙuri yanzu zan kira Muhsin yazo ya tayaki hira ko ya turo matarsa Jamila ta tayaki zama, saboda gaskiya banaso ki zauna ke kaɗai nasan kaɗaici dole zai dameki..." Bai jira cewarta ba kawai ya yanke wayar ya shiga neman layin Muhsin ɗin.

Itama Fa'izan a nata ɓangaren hakan ne ta kasance, domin yana katse wayar ta sake dialing numbernsa dan tace masa a'a ya barshi basai ya kira kowa yazo tayata zama ba, amma sai taji shi a call waiting alamar yana waya kuma ta tabbatarwa kanta da Muhsin ɗin ne yake wayar, yankewa tayi ta sake gwadawa amma taji still yana kan waya. Haƙura kawai tayi ta zauna a bakin gado riƙe da waya a hannu ta dafe kai yayinda lokaci ɗaya taji wani sabon ɓacin rai yana taso mata. Wannan wane irin abu ne..? Anya kuwa Farooq yasan darajarta..? Taya za'a ce komai baka isa kuyishi kaida mijinka ba sai an sako wani aboki aciki...? Gaskiya ta fara zargin ko dai Farooq baida lissafi ne ko baisan inda yake masa ciwo ba, taya namijin ƙwarai zaiyi wannan haukan..? Meyasa Farooq duk abinda zai yiwa matarsa ta sunnah sai ya riƙa dangantashi da abokinsa..? Wannan rayuwar ai ko a ƙasashen yahudawa bata taɓa jin anyi irin haka ba.

ABOKIN MIJINAWhere stories live. Discover now