*ABOKIN MIJINA*
*Wattpad: Aishaalto09*
*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*
*17*
Wani irin rawa jikin Jamila yake yi wanda yasa da ƙyar ta iya ɗora hannu akan ƙofar ta tura da duka ƙarfinta ta buɗe ta shiga, cak taja ta tsaya a bakin ƙofar tana kallonsu yayinda take jin wani sabon ɓacin rai yana taso mata.
Da sauri Muhsin dake tsaye daga shi sai gajeren wando ajikinsa yana rungume da Rashida wacce ke tsaye a gabansa itama daga ita sai ɗan pant da bra a jikinta tana shafa ƙirjinsa ya waigo cike da mamaki ya kalli Jamila data daskare a bakin ƙofa tana kallonsu kafin ya ɗauke kansa lokaci ɗaya yana faɗin "Lafiya kika wani tsaya mana a bakin ƙofa kina ƙare mana kallo...? Idan shigowa zakiyi ki shigo ciki mana..." Ɗagowa Rashida tayi ta watsa mata wani banzan kallo kafin ta juya a yatsine tana faɗin "Ita kuma wannan ɗin wacece...?" A harzuƙe Jamila ta bata amsa da faɗin "Matarsa ce ta sunnah ba irin ki ba karuwa gilli wacce bata san ciwon kanta ba..."
Wata irin dariyar rainin wayau Rashida ta bushe da ita kafin tace "Lallai kuwa matarsa ta sunnah..ni kuwa naga matar sunnah...Baby ashe dama kana da wata matar amma ka ɗauko karuwa...?" Ta faɗa tana kallon Muhsin wanda ya zubawa Jamila ido yana aikawa mata da wani mugun kallo na jin haushin shigowar da tayi ta katse masa hanzari, kafin ya girgiza kai lokaci ɗaya yana faɗin "Ina da mata Baby amma bata da wani muhimmanci a gurina...shiyasa na kiraki saboda kizo ki kawar min da ƙishirwa ta...amma kinsan ni babu abinda zanci da wannan abar..." Ya faɗa yana nuna Jamila sama da ƙasa lokaci ɗaya yana taɓe bakinsa.
Rashida tace "To zaman me take yi maka a gida...Ka sallameta mana ta koma gidan ubanta tunda bata da wani amfani...?" Ta faɗa tana kallon Jamilan itama. Muhsin yace "A'a ina tausaya mata ne saboda zawarci kinsan bashi da daɗi..." Rashida ta fashe da dariya tana kallon Jamila kana ta sake rungumosa jikinta tana faɗin "Kuma fa haka ne Baby, gwara ka riƙeta dan ko banza ka samu ladan ciyarwa...." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannunsa ta ɗora akan ƙirjinta tana wani lumshe idanu.
Baki a hangame Jamila take kallon Muhsin da Rashida, kasa haƙuri tayi ta taka har gabansu ta tsaya tana duban Muhsin wanda ya ɗauke kai yayi kamar bai ganta ba tace "Yanzu karuwa kake cewa ta fini a gurinka Muhsin kuma kake faɗi agabanta...?" Ta faɗa lokaci ɗaya ƙwalla na taruwa a idanunta. Uffan babu wanda yace mata a cikinsu, sai ma ƙara shigewa jikin Muhsin da Rashidan tayi ta haɗe bakinta da nashi lokaci ɗaya ta fara shasshafasa tana wani sauke numfashi cike da bariki kafin ta ɗago tana watsawa Jamila wani kallo tace "Kin takura mana ki fita ki bamu guri dan Allah..." Banza Jamila tayi da ita tace "Kana jin abinda take faɗa fa, ka koreta dan Allah karuwa ce fa bai kamata ace har ka nuna mata ta fini daraja da muhimmanci a gurinka ba Muhsin...dan Allah ka daina cewa ta fini a gurinka saboda ni ɗin matarka ce ta sunnah kaji..? Ka daina haɗa darajata da karuwa..." Gyaɗa mata kai yayi cike da tabbatarwa kana yace "Sosai kuwa zan ƙara faɗi tafi min ke sau dubun dubata..."
Wani mugun kallo Jamila take aika masa mai cike da baƙin ciki da ɓacin rai, kafin cikin ƙunar rai ta ɗaga hannu ta ɗauke Rashida da wani gigitaccen mari wanda yasa Rashidan ta ƙwalla wata ƙarar azaba kana ta dafe kumatunta tana kallon Muhsin lokaci ɗaya tace "Baby kana kallo wannan abar ta ɗaga hannu ta mareni a gabanka...?" Jamila tace "Ai ba iya marinki kaɗai ma zanyi ba dukan tsiya zan miki inci ubanki..." Ta ƙarashe maganar tare da fincike ta daga jikinsa ta hankaɗeta ta faɗa can gefe kana ta nuna ta da yatsa lokaci ɗaya zuciyarta na tafarfasa tace "Ki tashi tun muna shaidar juna ki fice min daga gida tun kafin in sauya miki kamanni dan gidana ba irin gidan da za'ayi kuskuren shigo da irinku bane ku fita lafiya...ki bari ku haɗu acan inda kuka saba haɗuwa kuyi iskancinku sai..." Marin da Muhsin ya ɗauketa dashi ne yasa sauran maganar tata maƙalewa a kan harshenta, da sauri ta dafe kumatunta ta ɗago a tsorace tana kallonsa lokaci ɗaya tana tsiyayar hawaye tace "Nika mara Muhsin...? Akan wannan abar har ka iya ɗaga hannunka ka mareni Muhsin akan karuwa...?" Cike da rashin mutunci yace "Sosai kuwa...kuma ko yanzu kika ƙara gigin taɓata sai na ninka miki wanda yafi wannan...banza kawai shashasha wacce bata san abinda take yi ba...." Ya ƙarashe maganar tare da miƙa hannunsa ya ɗago Rashida da tayi wani warwas a ƙasan ɗakin ta dafe kumatunta lokaci ɗaya tana sauke numfashin azafa saboda buguwar da ƙugunta yayi.