*ABOKIN MIJINA*
*Wattpad: Aishaalto09*
*DEDICATED TO: Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*
*22*
Ta daɗe durƙushe a gurin tana kuka ga cikinta yana ta murɗawa gashi tana bleeding sosai. Numfashinta sai sama sama yake kamar zai ɗauke tana ta dafe cikinta tana ƙoƙarin daidaita kanta, sai data ci kukanta sosai ta gode Allah kafin ta samu ta rarrafa ciki ta sakarwa kanta shower a daddafe tayi wanka ta rarrafo ta fito tazo ta buɗe wardrobe ta ɗauko pant da pad ta shirya ta zura doguwar rigar abaya ta haye gado. Har ta kwanta sai tayi tunanin to wa zata kira yazo ya taimaketa..? Wa take dashi a nan yanzu wanda zata kira domin yazo ya kawo mata ɗauki..? Momy bata nan gashi tana jin azabar ciwo kar tazo ta mutu ita kaɗai a cikin gida ba'a sani ba, bari ta rarrafa ta kai kanta asibiti. A hankali ta miƙe ta sauka daga kan gadon ta ɗauki hijabin sallarta ta saka sannan ta buɗe drower ta ɗauki kuɗi da porse ɗinta da wayarta ta fita. A hankali a hankali take iya ɗaga ƙafarta tana tafiya tana ɗan duƙewa sakamakon murɗar da cikinta yake yi.
Maigadi na ganin fitowarta ya taso da sauri ya nufota yana faɗin "Hajiya lafiya ina zaki je haka...?"
A hankali tace "Zanje asibiti ne bana jin daɗi Baba..."
Cikin tsananin tausayawa yace "Subhanallahi sannu Hajiya sannu Allah ya sawaƙe. Amma ɗazu naga abokin Alhaji ya shigo kuma ya daɗe da kin gaya masa ai da sai ya kaiki asibitin..."Wani kallon ashe baka da hankali Fa'iza ta ɗago da hanzari ta watsa masa kafin ta girgiza kai cike da takaici ta fice daga gidan ta tari Napep tace ya kaita asibitin Garkuwa.
Koda suka isa asibitin lokacin jinin ya fara zubar mata sosai, dan har wani jiri jiri take gani a idanunta, da ƙyar ta iya ɗaga ƙafarta ta fito daga napep ɗin bayan ta bashi kuɗinsa ta juya a hankali ta fara takawa zuwa cikin asibitin.
Wani irin jiri ne ya ɗebeta tayi baya zata faɗi da gudu wata nurse dake tsaye a pharmacy tazo amsar allura tayo kanta ta riƙeta tana faɗin "Subhanallahi sannu baiwar Allah..." Ta faɗa tana tarota jikinta. Kafin ta taimaka mata ta miƙe tsaye suka fara tafiya a hankali suka ƙarasa kan wani benci ta zaunar da ita tace "Zauna meye sunanki..ko lambar katinki inje in dubo miki...?"
Tuni Fa'iza ta soma fita a hayyacinta dan haka ta kasa bata amsa sai wani irin nishi take tana dafe cikinta ga jini sai zuba yake yana bin ƙafafuwanta, jikinta sai kakkarwa yake tana numfarfashi. Ganin yadda jini ke zubar mata yasa nan da nan nurse ɗin ta ruɗe ta kira wata abokiyar aikinta tace tazo da gadon ɗaukar marasa lafiya. Kai tsaye ɗakin ƴan ɓari suka nufa da ita dan zuwa lokacin Fa'iza bata iya gane komai kawai dai tana kwance ne idanuwanta a rufe amma haka hawaye suke gangarowa ta gefe da gefen idanunta suna gangarawa cikin kunnenta.
Da sauri nurse ɗin ta fita taje office ɗin likitan ta kirata suka dawo ɗakin tare. Likitan na fara dubata tace zasu riƙeta sakamakon bleeding ɗin da take sosai gashi tana da ƙaramin ciki. Cikin ƙwarewa da sanin kan aikinta ta duƙufa ta shiga bata taimakon gaggawa kafin ta samu numfashinta ya daidaita tayi mata allurar tsaida jini data bacci sannan tasa nurse ɗin ta ɗaura mata drip kana ta fice bayan tasa nurse ɗin ta kula da ita.
Bata farfaɗo ba sai gurin ƙarfe 8:20pm. Na dare lokacin data farfaɗo nurse ɗin taje ta kira likitan tazo ta sake dubata tace "Ya kike jin jikin naki yanzu..? Ina ke miki ciwo...?" Fa'iza ta girgiza mata kai a hankali tace "Alhamdulillahi ba inda yake min ciwo naji sauƙi..."
Likitan tace "Ya kamata ki kira ƴan uwanki ko mijinki ki gaya musu kina asibiti..." Nan take gaya mata cewa tana da ciki har na tsawon wata biyu tayi bleeding sosai ne wanda da ba dan tazo asibiti da wuri ba da ta rasa cikinta, amma yanzu sun samu sun tsaida jinin kuma Alhamdulillahi cikin yana nan bai fita ba. Kana ta ɗora da cewa "Ki kiyaye duk wani abun da zai ruɗaki ya firgitaki dan akwai abinda kika ganine wanda ya gigitaki kika fita a hayyacinki har yasa kika fara zubar da jini. Yanzu kina da wani ɗan uwanki da zaki kira a kusa a sanar masa da halin da kike ciki...?" Fa'iza tace "Eh..bari in kira Momyna..." Ta faɗa tana karɓan wayarta da nurse ɗin take miƙa mata, ta kira lambar Hajiya Nazifa ta gaya mata cewa tana asibiti.