Part 29

297 27 4
                                    

*ABOKIN MIJINA*

*Wattpad: Aishaalto09*

*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*

*29*

Tun daga wannan ranar Muhsin ya ƙara shiga cikin wani irin yanayi na tsantsar son kasancewa da Fa'iza, ga wata masifaffiyar sha'awarta dake addabar ruhi da zuciyarsa.
Har ta kai zuwa yanzu kwata kwata matarsa Jamila ko burgesa ba tayi ballantana yaji sha'awarta gabaki ɗaya hankali da tunani da natsuwarsa kacokan ya tattara su ne ya dora su akan Fa'iza, a kullum idan ya kwanta sai yayi mafarkin gasu a kwance yana saduwa da ita abun har ya soma bashi tsoro da al'ajabi.

Ita kanta Jamilan zuwa yanzu abun nasa har mamaki yake bata, dan sosai tasan halinsa baya taɓa shareta a shimfiɗa komai girman laifin da tayi masa kuwa amma yanzu har ta kai sai sufi sati bai waiwayeta ba, idan ita ta matsa masa kuma ya bata hakkinta babu abinda yake iya mata ƙarshe ma sai dai ranta yazo ya ɓaci ko yayi ta kiranta da sunan Fa'iza yana mata magiyar cewa ta amince dashi.

Tun abun yana bata mamaki har ya dawo yana bata tsoro tayi iya hasashe da tunaninta ta rasa wace Fa'iza yake magana akai dan ita koda wasa bata taɓa kawo Fa'iza matar abokinsa Farooq yake maganarta ba, ita duk a zatonta ta ɗauka dai acan ne gurin yawon neman matansa ya haɗu da wata mai irin sunan ta tsaya mai a wuya ya kasa rabuwa da ita shine sonta ya zautasa yake abu kamar wani taɓaɓɓe.

***********

_Bayan Wata Biyar_

Cikin Fa'iza ya ƙara fitowa sosai yayi girma dan a lokacin ya shiga wata na bakwai kenan, tun yana wata huɗu ta fara zuwa awo.
Kuma har zuwa lokacin Farooq bai taɓa kwatanta kiranta a waya ba ko sau ɗaya tun bayan faruwar abun wanda shi a nashi haukan kullum garin Allah idan ya waye jira yake yaga ta kirasa tana bashi haƙuri kan yazo ya maida ita ɗakinta sannan ta roƙesa yaba Muhsin haƙuri ko tace ya bata numbern Muhsin ɗin ta kirasa ta bashi haƙuri amma har yanzu shiru ko flashing ɗinta bai taɓa gani ba ballantana har yasa a ransa cewa wata rana zata kirasa.

Kuma shi baya ji a ransa cewa zai iya ɗaga waya ya kirata dan har yanzu yana jin haushinta akan abinda ta yiwa amininsa agaban iyayenta, ta tozartasa ta zubar masa da kima da mutunci sannan kuma yace ta roƙesa gafara amma taƙi ta nuna mai bai isa da ita ba a gaban kowa ta nuna masa iyakarsa.

          ********

A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya wani lokacin aji daɗi yayinda wani lokacin kuma aji akasin haka.
Tafi tafi har cikin Fa'iza ya isa haihuwa Farooq bai san a wane hali take ciki ba.
Kuma bai taɓa nemanta ba, haka suma iyayenta babu wanda yabi ta kansa balle suyi tunanin tuntuɓarsa akan zancen cikin da yake jikinta ko a nemi ya kawo abinda za'a dinga kula dasu ita da abinda ke cikinta.

Shima kuma Farooq ɗin bai taɓa wannan tunanin ba balle ya duba rashin kyautawarsa akan hakan kawai sha'anin gabansa yake yi, duk da tarin kewa da tsananin tausayin Fa'izan da yake ji danƙare a ƙasan ransa baisa ya sauko daga dokin fushi da jin haushinta da yake yi a zuciyarsa ba ballantana ya sassauta mata ko nemanta ne a waya yayi yaji ya lafiyarta data babynsa ba, sai ma wani girman kai da isa da yake ji na cewa meyasa ita bazata nemesa ba idan shi bai taɓa nemanta ba ai kamata yayi ace ita da take a ƙarƙashinsa sannan tasan tayi masa laifi ta kirasa tana mai kwantar da kanta ta rokesa ko zai yafe mata amman sai yaji shiru ko bi ta kansa Fa'iza bata taɓa yi ba har yau.
Aiko sosai kuwa hakan ya ƙara hasala zuciyar Farooq ya ƙara jin haushinta fiye da farko.

Ita kuwa Fa'iza a ɓangarenta babu abinda ya dameta da wani Farooq, gabaki ɗaya ta tattarasa ta watsar gefe rayuwarta kawai take gudanarwa cikin kwanciyar hankali da natsuwa babu abinda yake damunta dan haka ko tunanin meyasa baya kiranta ma bata taɓa yi ba, ita ta rainon cikinta kawai take dan shi tasa gaba burinta kawai shine taga ta haihu lafiya ta raini jaririnta cikin kwanciyar hankali.

ABOKIN MIJINAWhere stories live. Discover now