*ABOKIN MIJINA*
*Na*
*Aisha Alto*
*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*
*7*
Sanyin asuba dake ratsowa cikin falon ne ya haɗu da sanyin tails ɗin dake ƙasan falon ya tashi Jamila wacce ta takure jikinta ta ƙudundune, da sauri ta tashi zaune jikinta na rawar sanyi ta juya tana kallon agogon dake maƙale a falon ƙarfe 5:45am. A zabure ta miƙe tana jin tsigar jikinta na tashi saboda tsabar sanyin da take ji yana shiga jikinta, a hankali ta ɗaga ƙafarta ta nufi ɗakin baccinsu ta tura ƙofar ta shige ciki. Da Muhsin ta fara cinkaro wanda yayi rashe rashe a tsakiyar gadonsu yana kwasar baccinsa hankali kwance, turus taja ta tsaya a bakin ƙofa cike da mamaki haɗe da al'ajabi take binsa da kallo kafin ta taka ta ƙarasa shiga cikin ɗakin ta tsaya a kansa cike da takaici, kenan ashe ya dawo gidan tun cikin dare shine ita ya tsalleta a falo yay wucewarsa ɗaki ya kwanta abunsa ita kuma ya barta acan ta ƙarata, wato duk abun ma da ya sameta babu ruwansa tunda bashi da asara, ƙwafa tayi cike da baƙin ciki kafin ta fara dukan katifar saboda tasan ya tsani idan yana bacci a tashesa har sai idan shine ya tashi dan kansa, shiyasa ta zage da iya ƙarfinta tana bugun katifar tace "Ka tashi kayi sallah asuba tayi..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana janye filon da kansa yake kai ta wurgar a ƙasa kafin ta kuma buɗe muryarta da ƙarfi tace "Ka tashi an kira sallah...lokaci zai wuce.." Wani irin juyowa yay idanunsa cike da bacci ya ɗan kalleta kafin ya sake gyara kwanciyarsa yaja bargo lokaci ɗaya ya juya mata baya zai ci gaba da baccinsa, fizge bargon tayi tana watsa masa harara ta sake cewa "Ai wlh saika tashi, dan nima yau saina ƙuntata maka kamar yadda kayi min..." Tashi zaune yay yana kallonta da idanuwansa wanda suka kaɗa jajir yace "Amma kinsan dai ba'a taɓa tashina idan ina bacci ko har sai idan nine na tashi da kaina..? Kuma na gaya miki kin sani...amma saboda ke kamar dabb..." Kallon da take watsa masa ne ya hanasa ƙarasa abinda yayi niyyar faɗa kawai ya ɗauke kansa. Ƙwafa ta sakeyi a karo na biyu tana harararsa tace "Wallahi karka sake koda wasa Muhsin kayi gigin kirana da kalmar da naji kana ƙoƙarin gaya min yanzu...saboda bazamu taɓa kwashewa da daɗi ba nida kai...domin zan iya jurar komai ciki kuwa har da wulaƙancinka amma bazan taɓa ɗaukar zagi da cin fuska ba, idan kuma kana tunanin da na ɗauka to yanzu bazan ɗauka ba..." Tana ƙarasa faɗar haka ta juya ba tare data sake tanka masa ba tayi shigewarta banɗaki ta barshi a nan.
Saukowa yay daga kan gadon shima yana saƙa abinda ya kamata yayi mata a zuciyarsa ya fice daga ɗakin zuwa ɗakin dake kusa da nasu.
★★★
Sosai taci baccinta ta gode Allah, dan sai gurin ƙarfe 11am. Dai-dai sannan ta tashi, a gurguje ta faɗa toilet tayo wanka ta fito ta shirya cikin wani leshi mara nauyi ɗinkin riga da siket ta fesa turare kaɗan a jikinta ta fito ta shiga kichin dan ta samar musu abinda zasu karya ita da Malam Garba.
Ta jima a tsaye tana tunanin abinda zata dafa musu mai sauƙi wanda bazai mata wuyar dahuwa ba, saboda tasan ta ɗauki alhakin bawan Allah tabarshi da yunwa, yanke shawarar dafa ruwan zafi tayi ta zuba kayan ƙamshi aciki da ya tafasa ta juye a filas, sannan ta fasa kwai ta soya ta kwashe ta haɗa tean a cikin babban jug ta ɗebarwa Malam Garba nasa ta haɗa masa da buredi, sai data koma bedroom ɗinsu ta ɗauko hijabin sallarta ta saka sannan ta ɗauka ta fita ta miƙa masa ta dawo ta kulle ƙofar, kafin itama ta shiga kichin ta ɗauko nata ta zauna a falo tana ci, data gama ta haɗa kayan ta kai kichin ta wanke sannan ta fito ta wuce bedroom ɗinsu ta ɗauko wayarta ta dawo falon ta zauna akan doguwar kujera ta ɗan kashingiɗa bayan ta kunna data ta hau WhatsApp ta shiga group ɗinsu wanda suka buɗe da ƙawayenta wanda suka gama makaranta tare suka soma hirar duniya wanda yawancinsu suma duk matan auren ne dan wasu har suna da ƴa'ƴa, ƴan matan cikinsu kwata kwata basu wuce uku ba, kuma suma duk an tsaida musu rana sun kusa auren.