*ABOKIN MIJINA*
*Wattpad: Aishaalto09*
*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*
_Wannan shafin nawa sadaukarwa ne a gareki Ƴa guda, wato Ɗiyar Ƙwarai irin Albarka Aisha Alto ta baki shi kyauta kiyi yadda kike so dashi. *RAHMA UMMU FAREESA* (Ladingo) Allah yayi miki albarka, Allah ya raya miki zuri'a rayuwa mai albarka, Allah ya tsaya miki ya iya miki abinda kika gaza, inai miki fatan alkhairi SON SO Domin ALLAH._
*19*
Wani irin mummunan faɗuwa gaban Fa'iza yayi a gefe guda na zuciyarta kuwa cewa take Wannan karon wallahi sai ta gayawa Farooq duk abinda yake ranta... Kawai sai ta zare jikinta a nasa ta miƙe ta sauka daga kan gadon ta kunna wutan ɗakin ta tsaya tana duban Farooq wanda ya ƙura mata ido cike da mamaki yake faɗin "Habeebti lafiya...?" Fa'iza tace "Gaskiya Habeebi abinda kake baka kyautawa..Habeebi na tabbata kana da ilimin addini dai-dai gwargwado ka kuma san illar mace ta dinga mu'amala da wani namijin da ba muharraminta ba amma..." Katseta Farooq yayi lokaci ɗaya yana watsa mata wani kallo akaikaice kafin yace "Ban gane me kike nufi ba...kina nufin cewa sanin addinina bai min amfani ba ne ko me...? Ai ba cewa nayi kuyi wani mu'amala ba tunda ba cewa nayi ku dinga riƙe hannun juna ko ku rungume juna ba, kawai cewa nayi ya rinƙa zuwa kullum yana kula dake saboda kar a barki ke kaɗai a gida kewa ta riƙa damunki..tsakani da Allah fa ba garin nan kike ba, na ɗauko amanarki kuma zan so in barki ne in tafi wata uwa duniya...?" Fa'iza tace "Ba wannan ba, ba haka ake bada amana ba...wace irin amana zaka bashi..? Ai ba wata amana da zaka bashi, aini a gurin Allah ka barni ba gurin kowa ba...kuma zaman aure nake dama kuma ya gaji haka, dan haka zanyi haƙuri duk daɗewar da zakayi zan iya jurewa tunda ba dawwama zakayi acan ba wata rana zaka dawo, amma gaskiya ni bana son kana turo min wani gardin banza yana zuwa gidana..." Ta ƙarashe maganar cike da takaici tana kumbura baki.
Ido Farooq ya zaro lokaci ɗaya yana faɗin "Ehh Fa'iza! Wa kike kira gardin..Muhsin ɗin..? Toh lallai idan kika kira Muhsin gardi zaki iya kirana da gardi nima..." Tace "Kai ba gardi bane, saboda kai mijina ne muharramina ne, shi kuma ba muharramina bane kuma babu abinda ya haɗani dashi...amma kana turoshi yana zuwa yana mu'amala da matarka, haba Farooq! Kai baka jin kishi ne!! Baka jin wani abu a ranka ne..ko ko baka jin damuwa ne...? Ban taɓa ganin namijin da yake yassarar da matarsa ba irinka..na gaji da irin abubuwan da kake min ya kamata in fito in gaya maka gaskiya koda bazaka ji ba...haba Farooq..wani idan yaji irin abinda kake ba sai a ɗauka kaman baka da ilimin addini ba ne..." Ta ƙarashe maganar tana ɗauke kanta gefe.
Wani mugun kallo Farooq yake watsa mata kafin ya sauko daga gadon ransa a mugun ɓace ya tsaya a gabanta yana faɗin "Yanzu Fa'iza ni kika tasa a gaba kike gayawa wannan maganar haka...? Look daman fa ba tun yau ba naga take takenki bar..." Saurin katsesa tayi da faɗin "Tsaya...Farooq ka tsaya in gama maganata..Muhsin ba mutumin ƙwarai bane, kai ka ɗaukesa a matsayin aboki amini, amma shi bai ɗaukeka aboki ba, so yake kawai yaci dunduniyar ka ya ha'inceka..." Cike da mamaki Farooq yake dubanta kafin yace "Wane irin yaci dunduniya ta ya ha'inceni...?" Fa'iza tace "Saboda Muhsin yasha nuna min alamun cewa yana sona..bana bashi fuska ne, amma duk da haka bai ƙyaleni ba, sai ma neman kusanci dani da yake ta yadda zai samu cikar burinsa a kaina...abokin ƙwarai ne zai nemi kusanci da matar abokinsa..bashi da mata ne...? Kuma ita kanta matar tasa ba complain take dashi akan neme nemen matan banzan da yake ba...?"
Yace "Ok ta nan kika ɓullo kuma...? Nasan tabbas Muhsin yana neman mata, amma nasan duk neme nemen matansa ba zai nemi matata ba, kuma abinda baki sani ba shine Muhsin ya daɗe yana neman mata kuma na mai faɗa ya tabbatar min daya daina kuma nasan tabbas ya daina ɗin..."
A fusace Fa'iza tace "Toh bai daina ba sannan kuma bai da niyyar dainawar, kai ubansa ne ma da zakayi masa faɗa yaji..? Toh ya ɗaukeka a wawa baka san me kakeyi ba, wallahi tallahi Jamila ta gaya min cewa neme nemen matansa bai daina ba, kuma ita kanta ba kallonta yake da kima da mutunci ba..."