Part 5

535 28 1
                                    

*ABOKIN MIJINA*

    *Na*

*Aisha Alto*

*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*

*5*

*TUSHE..*

Alhaji Abubakar Ƙaraye shine cikakken sunan mahaifin Farooq, sai mahaifiyarsa Hajiya Nazifa mace mai kunya da kawaici wacce auren zumunci akayi musu.

Asalin su ƴan garin Ƙaraye ne wacce ke a jihar Kano, babansa Malam Umaru shine sarkin noman garin na Ƙaraye, yanzu haka duka danginsu suna can harkar kwangilarsa ce ta kawosa garin Kaduna ya gina tamfatsetsen gidansa a unguwar Rimi Gra ya tare da matarsa.

Alhaji Abubakar Ƙaraye ya kasance tun yana da rai babban ɗan kwangila ne, yayinda matarsa Hajiya Nazifa take rikakkiyar ƴar kasuwa, wacce take saida zannuwa, atamfofi, lesuna, shaddodi, da sauransu, wanda har ƙasashen waje take fita sarin kaya, a yanzu shagunanta huɗu a Central Market. Hajiya Nazifa ta kasance mace ce mai matuƙar kirki da zumunci tamkar mijinta, gashi bata da ɗagawa abunsu kwata kwata bai rufe musu ido ba, ko kaɗan basa taɓa nuna su wasu ne. Sun daɗe sosai da aure amma basu samu haihuwa, tun abun yana damunsu har suka haƙura suka fauwalawa Allah komai, sai dai duk tsakiyar dare su tashi suyi alwala suyi sallah sukai kukasu ga rabbi, har suka kai shekaru biyar da aure ko ɓatan wata Hajiya Nazifa bata taɓa yi ba, sosai abun yake damu Alhaji Abubakar kasancewarsa mutum ne shi mai tsananin son ƴaƴa, Amma haka nan yake dannewa baya taɓa nuna damuwarsa ko kaɗan saboda baya so hankalin Hajiya Nazifan ya tashi, ta ɗauka ko daga ita ne matsalar take. Haka yay ta danne abun a cikin ransa bai taɓa nunawa ba.

Tafi tafi haka rayuwa tai ta tafiya har suka cika shekara sha tara da aure babu wani labari. Kwatsam wata ranar juma'a tunda sassafe Hajiya Nazifa ta tashi da wani zazzafan zazzaɓi mai tsanani, sosai hankalin Alhaji Abubakar ya tashi yay bala'in ruɗewa, jiki na rawa ya kira likitansa yazo, gwajin farko da likitan yayi mata sakamako ya nuna tana ɗauke da ciki har na tsawon wata huɗu. Wannan kyakkyawan labari yay matuƙar faranta ran Alhaji Abubakar Ƙaraye da Hajiya Nazifa, wanda har sai da suka zubar da ƙwallar farin ciki, kafin yayi sujjada yana ƙara godewa ubangijin daya bashi wannan kyauta a lokacin daya gama cire tsammani da samunta, wacce tarin dukiyarsa ko wata kadara tashi basu isa susashi ya sameta ba. Wannan rana ta kasance babbar rana ce a gurin Alhaji Abubakar Ƙaraye da Hajiya Nazifa da danginsu gaba ɗaya, dan babu wanda bai yi farin ciki da samun wannan ciki ba. Tarairaya da nuna tsantsar kulawa su Alhaji Abubakar yake nunawa Hajiya Nazifa har zuwa lokacin da cikinta ya tsufa ta shiga watan haihuwarta.

Ranar da suka cika shekara ashirin dai-dai da aure ta haifi kyakkyawan ɗanta fari tas mai kama da mahaifinsa sak, aka sanya masa suna Omar Farooq. Farooq ya taso cikin tsananin gata da jin daɗin rayuwa, komai na duniyan nan ya samu, saboda ya taso cikin daula da tarin dukiya, ga tsantsar ƙaunar da iyayensa suke nuna masa. Shekarar Farooq ɗaya a duniya Allah yayiwa kakansa Malam Umaru rasuwa, sosai mutuwar ta girgiza Alhaji Abubakar Ƙaraye da Hajiya Nazifa da sauran danginsu, sun yi kuka sosai na rashin babban bango kuma jigo adalin tsoho mai dattako da sanin ya kamata, wanda basu kaɗai ba hatta da ƴan garin Ƙaraye sai da suma suka koka sakamakon rashin Malam Umaru. Satinsu Hajiya Nazifa da Alhaji Abubakar biyu a garin suka tattaro suka dawo Kaduna cike da kewa.

Tafi tafi dai haka rayuwa tai ta gangarawa, yayinda abubuwa suketa sauyawa, inda Alhaji Abubakar Ƙaraye ya sake zama shahararren mai arziki, wanda ya mallaki gidaje da filaye, da manya manyan kamfanoni.

Haɗuwar Farooq da Muhsin ta samo asali ne, wata rana direban Farooq ɗin ya ɗaukosa daga makaranta ya hango Muhsin tsaye a bakin titi sanye da uniform ɗinsa na makarantar gwamnati gashi rana ta ƙwallare fuskarsa duk tai faca faca da gumi sai gogewa yake, da sauri Farooq yasa direbansa ya tsaya suka ɗauki Muhsin ɗin suka kaishi har gidansu, ashe a bayan layinsu Farooq ɗin gidansu yake, ranar dai Hajiya Nazifa tasha labarin Muhsin a gurin Farooq kamar me, dan lokaci guda Farooq yaji Muhsin ya shigar masa rai yana tsananin jin tausayinsa kasancewarsa mai jin tausayi da son taimako irin na iyayensa, To tun daga wannan ranar Muhsin ya kasance aboki ga Farooq na ƙut da ƙut, sun shaƙu da juna sosai komai tare sukeyi, makaranta ce kaɗai ke rabasu, kasancewar shi Farooq makarantar kuɗi yake zuwa yayinda shi kuma Muhsin yake zuwa makarantar gwamnati.

ABOKIN MIJINAWhere stories live. Discover now