Part 11

382 26 0
                                    

*ABOKIN MIJINA*

*Wattpad:Aishaalto09*

*DEDICATED TO: My Jikalle Aslamiyya Aliyu Usman (Tafisu)*

*11*

Farooq yana shiga layin gidansa ana kiran sallar la'asar, dan haka bai wuce gida ba yayi parking ɗin motarsa a nan bakin masallacin dake layin yayi alwala yayi Sallah sannan ya fito ya shiga motarsa ya nufi gidan.

Lokacin da Farooq ya isa gidan ya iske Fa'iza ta gama girkin har ta jera komai akan dinning tana zaune a falon cikin kwalliyarta mai kyau da burgewa, sai zuba ƙamshi take tana riƙe da wayarta a hannu tana ƙoƙarin danna numbernsa ta kira ya sawo kai cikin falon bakinsa ɗauke da sallama ya shigo, cak ya tsaya abakin ƙofa ya zuba mata ido yana ƙare mata kallo kafin ya ware hannayensa lokaci ɗaya ya gyaɗa mata kai alamar tazo garesa.

Miƙewa tayi tsam kafin ta fara takawa a hankali tana wata irin tafiya mai cike da jan hankali har ta isa garesa, Farooq wanda ya gaji da tsayuwa har ya ƙagara ta iso ya miƙa hannuwansa duka ya jawota ta faɗo saman ƙirjinsa lokaci ɗaya suka sauke ajiyar zuciya atare, a hankali ya ɗago kanta ya kai bakinsa saman goshinta ya sumbata kafin ya sake kwantar da kanta a ƙirjinsa ya tura kansa cikin wuyanta yana sunsunar ƙamshin jikinta yace "Gaskiya Habeebti ƙamshin nan yayi min...wane irin turare ne wannan...?" Ya faɗa yana ƙara tura kasa cikin wuyanta zuwa bayan kunnenta, a hankali ta ɗan janye daga jikinsa lokaci ɗaya tana maƙale kafaɗarta kafin tace "Nima bansan sunansa ba..." Ta faɗi cikin taushin murya tare da zagaye hannayenta a ƙugunsa. Bai ce komai ba ya kama hannunta bayan ya janyeta daga jikinsa suka nufi bedroom ɗinsu ta taimaka mai ya cire kayan jikinsa ta ɗauko mai tree kwata da wata ƙaramar riga ya saka kafin suka sake fitowa falo suka nufi dinning. Sai da suka gama cin abincin sannan suka tashi suka dawo cikin falon suka zauna bayan ta kunna musu tv ta kamo musu tashar MBC 2 inda ake haska wani American Film mai kyau suka fara kallo.

Ƙarfe 4:20pm. Dai-dai Fa'iza ta tashi ta shiga kichin dan ta ɗora abincin dare, yayinda da ta bar Farooq shi kaɗai a falon yana kallo. Da wanke farar shinkafa ta fara ta ɗora tuwo kafin ta buɗe frigde ta ɗauko naman kai da ya fara ƙanƙara sannan ta ɗebi kayan miya dai-dai yadda zai isheta ta wanke ta markaɗa a blander, sai data wanke naman tsaf sannan ta kunna gas ta ɗora tukunya ta zuba naman kan a ciki kafin ta juye kayan miyan data markaɗa akai ta zuba kayan ƙamshi ta rufe. Cikin lokaci ƙalilan ta gama tuƙe tuwon shinkafarta tsaf ta kwashe ta mulmula a farar leda ta zuba a kula ta ajiye. Kasancewar a gas ne yasa bata wani ɗauki dogon lokaci ba ta gama haɗa miyar ganyenta data ji naman rago zuƙu zuƙu sai tashin ƙamshi take sannan ta sauke farfesun naman kan shima ta juye a kula. Tana kammala komai ana kiran sallah Magriba, dan haka ta kashe gas ɗin ta ɗauki kulolin data zuba abincin a ciki ta ɗora a babban tire ta ɗauka ta kai dinning ta jera kafin ta dawo ta goge kichin ɗin ta fito ta wuce bedroom dan gabatar da sallar Magriba da ake kira.

Tana shiga Farooq yana fitowa daga toilet wanda shigarsa toilet ɗin kenan shima ya watso ruwa a gurguje ya haɗo da alwala ya fito ya goge jikinsa kana ya zira jallabiya ya fesa turare ya fice daga ɗakin zuwa masallaci. Itama tuɓe kayan jikinta tayi ta faɗa toilet ɗin ta watsa ruwa kafin ta ɗauro alwala ta fito, a gurguje ta shafa mai sama sama kafin ta zura doguwar riga haɗe da hijabi ta tayar da sallah, koda ta idar bata tashi daga gurin ba sai data sallaci sallar isha'i kana ta miƙe ta cire hijabin sannan ta ƙarasa gaban madubi ta zauna ta ƙara murza mai a jikinta kafin ta ɗan yi kwalliya kaɗan ta fesa turare ta miƙe ta ɗauki wata haɗaɗɗiyar doguwar rigarta mai kyau ƙirar Oman wacce tasha adon duwatsu a gabanta ta zira ta ƙara feshe jikinta da turare sannan ta ɗauki gyalen rigar ta yi rolling a kanta ta fice daga ɗakin ta nufi falo.

Tana zama a kujera Farooq da Muhsin suna shigowa cikin falon atare bakinsu ɗauke da sallama, wani irin faɗuwa gabanta yayi da sauri ta ɗauke kanta gefe tana addu'ar neman tsari a zuciyarta kafin ta miƙe a sanyaye zata wuce bedroom tayi kamar bata gansu ba, kiran sunanta Farooq yayi cike da mamaki kafin ya matsa kusa da ita yana faɗin "Ba kiga shigowar mu bane Habeebti kika tashi zaki wuce..." Ya faɗa yana riƙe hannunta lokaci ɗaya yana bin jikinta da kallo yace "Kai Masha Allah Habeebti na kullum kamar ƙara miki kyau akeyi, wai meye sirrin ne...?" Banza dashi Fa'iza tayi ta ɗauke kanta gefe ɗaya tana watsawa Muhsin wani irin kallon tsana kafin tace "Sirrin yana daga gareka ne ai Habeebi...dan duk wani canji da zaka gani a tattare da Fa'iza daga gurin Farooq ɗinta ne..saboda sinadarin a gareka yake mijina..." Ta ƙarashe maganar tare da aikawa Muhsin wani irin mugun kallo lokaci ɗaya tana taɓe baki. Saurin ɗauke kai Muhsin yayi daga kallonta dan bazai taɓa iya jurar wannan wulaƙantaccen kallon daga gareta ba, saboda bai san da wace irin kalma zai iya misalta ko fasalta yadda yake jin matsayin Fa'izan a zuciyarsa ba, amma yasan idan har zai iya jurar hango wannan muguwar tsanar da take yi masa a cikin ƙwayar idanunta da wuya ya iya cigaba da jin sha'awarta dan dole yasan wata rana gwiwarsa zatayi sanyi yaji gaba ɗaya ya sare da a'lamarin, shi kuma abinda baya so kenan ya faru. Yafi so kamar yadda ya ɗauki ƙudiri akanta ya kuma sha alwashin ganin ya samu cikar burinsa ya tabbatar hakan ta kasance idan kuwa ba haka ba baya jin zai iya ƙyaleta ba tare da ya samu biyan buƙatarsa ba, dan bai taɓa jin abinda ya tsaya mai a rai yaƙi wucewa ko dai dai da na second ɗaya ba irin sha'awar Fa'iza.

ABOKIN MIJINAWhere stories live. Discover now