Who is layla?

200 17 1
                                    

Layla ba zaki fadamin abunda ya faru ba,wato ni zaki maida yar iska ko?
momy ce ke waya a daki tana faman yiwa tilon kanwar tata fada.
Tsaki taja sannan ta kashe wayar ta jefata akan gado.
Tafiya take cikin dakin tana hucin bacin rai tana zagaya dakin tana cewa "amma yaranan sun raina min hankali,taya za'aima suce babu abunda ya shiga tsakaninsu,sabida ina da tabbacin yaron nan ya fita hayyacinsa jiya,bugu da kari ga a yanayin daya dawo amma layla tace min ko ganin shi bata yi ba jiya,to wlh zata gamu dani inma yar iska take so ta mai dani.
Jin ana buga kofar dakin yasa ta fara saka annuri a fuskarta sabida da tasan daddy ne.
Isa tayi ta bude kofar,daddy dake jikin kofar ne ya shigo yana Kallonta yace "lfy kika rufe?"
Murmushi tayi tace,wlh wasu yan gyare gyare nake yi ne,shiyasa na rufe domin nafi samun nutsuwa kada karar tv din can ta dauke min hankali.
Zama yayi kan gadon dauke da salati a bakinsa.
Kallonsa tayi tace "ba yau kace za'a sallamo shi?"
"Eh an sallamoshi ma but yayi deciding ya zauna ne tare da abokinsa sabida ya dauke mishi kewa "
Daddy ya fadin hakan ne kawai sabida bai son wani dogon zance sabida idan yace mata yana wancan gidan to damunshi zatayi da complain .
Shiru tayi tana sauraran shi,sannan ta furta "Allah y bashi lfy,gobe maje ma duba shi da layla dan bata san bashi da lfy bama sai dana fada mata yanxu,har take cemin kalau suka rabu ranar dayaje mata.
"
Jijjiga kai daddy yayi sannan yace "ai basai kunje ba coz doctor yace kada yana jin hayaniya,sannan Nigeria ma zai koma "
Sanin daddy baison musu yasa kawai tace "Toh Allah y bashi lfy "
Ameen y amsa sannan ya tashi y shiga wanka kafin yaci abinci.
Jin budewar kofa yasa momy ta fita don ta leka wane,
Ganin layla zaune kan kojera fuju fuju da ita alamun tashin hankali tattare da ita yasa momy ta saki baki tana kallonta.
Layla is 23 kyakykyawa ce ajin farko half c ne su din mamansu balarabiya sai kuma baban dan Nigeria amma bafulatani,kanwar momy ce uwa daya uba daya saide tafi momy kyau nesa ba kusa ba,tun tana karama momy take riketa,sakamknku iyayensu sun rasu sannan momy bata taba haihuwa ba wannan ya kasance momy take kamar uwa awajan layla dan tare suka sha duk wata gwagwarmayar rayuwa dana aurarrakin da momy tayi tare har suka kawo yanxu da momy ta auri daddy.
Saidee yanxu bata cika zama agidan ba sosai sabida da karatun da takeyi kuma university da nisa daga nan,shiyasa take zama hostel ,weekend ne ke kawota gida.
Layla wani irin so take yiwa Abee(dude,son)"duka suna shi ne "
Son ya faro ne tun lokacin data fara tozali dashi,taji duk duniya ba wanda take muradi kamarsa,tuni ta fara shishshige masa,tun baya kulata har yazo ta fara bashi tausaya yake dan sakar mata suna dan hira sabida dashi yarinyar ma tausayi take bashi dan duk me zai mata bata taba zuciya dashi saide ma ta biyo shi ta bashi hakura,hakan yasa take dan bashi tausayi danshi ko burgeshi bata taba yiba balle yakai da yana sonta,kai shi ko soyayya ma zaiyi bazai taba son Layla ba ballantana kuma ya aureta,sabida rawarkan Layla ya mata yawa ga yawan kawaye,sannan bugu da kari shi bai yarda ta tarbiyyar da momy ta daura ta akaiba,dan Kallon makira yakewa momy kuma marar jin tsoron Allah,dan momy akwai son abun duniya.
Kai shi inbanda daddy da dadan shi ma ba wanda ya yarda shi,gwara mukhtar yana ganin hankalin sa shima but shi dama naturally baida saurin yarda mutane,sabida Dadan shi tasha bashi lbrin gwagwarmayar rayuwa,bugu da kari kuma yarda mahaifiyar shi tasha wahala wajan kishiyar uwa.
Wanda wannan wahalar saida yayi affecting nata da kuma yayan dake cikinta kafin ta koma ga Allah.
Wannan yasa kwata 2 bai yarda mutane sosai.
Momy kuwa bakaramin kishin Abee dake jiba duba da irin soyayyar da daddy ke nuna masa,bugu da kari kuma ba haihuwa take ba,dan haka yau ko da daddy ne ya fadi y mutu to fa iya tumunin takaba ne nata tunda bata haihu dashi ba,wannan yasa take goyon bayan layla ta auri Abee,duk banza tasan zata iya juya layla su samu yarda suke so.
Shiyasa kullum burin momy shine Abee ya auri layla amma abun yaci tura dan nunawa ma yake baisan me suke ba,hakan ne yasa momy ta fara yiwa daddy maganar abun,daddy yayi farin ciki da hakan dan ko banza ya dauki Layla a matsa yin yarsa itama.
Tashin farko da daddy ya yiwa Abee maganar,nunawa yayi shifa bayanxu zaiyi aure ba sannan ko zai yima shi bazai auri layla ba.
Ganin hankalin shi ya tashi yasa,daddy yace a hakura tunda son baya so sannan shiya dauka ma son ne yayi zancan yana so shiyasa har yayi masa zancan.
Wannan abu ba karamin tada hankalin momy yayiba haka zalika itama Laylar,hakan yasa momy take neman duk wata hanya dazaisa yiwuwar auren nasu ba tare da Laylan ta saniba,bangaren layla kuwa tana nan tana kara cusa kanta sabida ta samu ko Abee zai hakura ya karkato kanta.
Wannan yasa momy ta shirya masa wannan makirci dan ta samu yayiwa layla fyade ko sau daya ne daga nan ta samu hujjar dazai auri kanwartata ,hakan kuma bai yiwu ba,sai tsautsayi ya fada kan Zarah wanda momy batasan da hakan ba,haka zalika layla.""

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now