She's heartless

265 19 1
                                    

Bayan tafiyar su lamee  saudiyam ba karamin addu'oi fulani tayi ba,Na Allah y bata haihuwa karo na biyu,sannan malam Ahmadu ma na mata addu'a yasa kuma anma mata,da haka suka dawo gida bayan sati biyu,sunyi niyyar yin sati uku ne amma sabida larurar da suka ji professor hameesu ya fada musu cewa,fiddausy bata da lfy sosai abunma yana so ya kada mata hauka.domin har fita waje take da gudu,nan fa hankalin fulani ya tashi dan suna shiri sosai da fiddausy,awajanta ma tabar mata mukhtar ta howarsu aikin hajjin.
Bayan dawowarsu ne suka tarar cewa fa abun na fiddausy harya koma hauka ma,bakaramin kuka fulani tayi ba. Daga nan ne yaran fiddausy guda hudu babban sunansa Yusuf sai amir da Aisha sai auta elham,duk fulani ta tattaro su suka dawo wajanta ,yan uwan fiddausy kuma da suka ga halin da take ciki sai suka dauke ta suka tafi da ita gida domin gwada maganin su,Bayan wasu wata biyu kuwa,kwatsam sai ga fiddausy ta dawo cikin koshin lfy kamar batayi wannan jinya  ba.u
Dawowar fiddausy ne take bama fulani lbrin cewa balaraba ce tayi mata asiri,dan har bibiyarta sunyi sun gano cewa suna xuwa wajan boka a wani kyauye tare da lamee.Dan haka itama ta dagee da addu'ar da kuma magani,dan zai iya yuwuwa itama asirin lamee tayi mata itama.
Ba karamin shocked fulani ta shiga ba,dan harda kukanta itama.
Take fiddausy ta bata shwarar cewa,ba kuka zakiyi ba fulani tashi zakiyi da addu'a da kuma magani kina yi,dan wannan zubewar cikin naki ba'a banza kike yinsa ba,yanxu ga wasu daga cikin maganin sanmu na taho miki dashi ki fara using munga abunda Allah zaiyi.Na'am fulani tayi da shawarar fiddausy sannan tayi mata godiya,daga nan alaka mai kyau ta kara shiga tsakanin su.
♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️
Haka rayuwa ta ci gaba bayan shekara 3 aka budewa fulani mahaifarta a bisa ga shawarar doctor da suka bi.
Cikin ikon Allah kuwa bayan wata biyar da bude mahaifa fulani ta samu ciki,ba wanda ta fadawa sai fiddausy.har saida akayi wata 5 sannan cikin ya fara nunawa,amma duk da haka bata bari lamee ta fuskanta ba,Dan cewa tayi da malam Ahmadu Dan Allah kada t fadawa kowa harsai cikin y girma,shi kuwa yabar zancen a haka.
Ana haka kuma har yau Allah baiba ramlatu haihuwa,ba inda lamee ba taje nemon taimako ba amma shiru.
Saida cikin fulani ya shiga wata 8 sannan lamee ta gane,shima sanadiyyar shiga part din fulani da tayi neman Fareeda,ta ganta a tsakar gida tana koya wa yaran karatu.
Ba karamin firgici ta shiga ba da ganin wannan abu,kallan kallo suka tsaya yi,har fulani ta gane yanayin da lamee ta shiga ganin wannan ciki.
Ficewa tayi afusace ko tsayawa kiran Fareedan batayi ba.
Fita ta kira balaraba a waya tana sintiri a daki,take t fada mata halin da ake ciki,itama ba karamin mamaki ta shiga ba,kwantar mata da hankali tayi,kuma ta bata shawarar gobe sassafe zasu tafi wajan boka.
Hakan ce kuwa ta faru washe garin ranar suka kaiwa boka kukan cewa duk yadda za'ai kada ya bari cikin nan yazo duniya,abubuwan tsibbace 2 sa yayi,sannan y kalle su yace,wannan karan za'a iya samun matsala tunda har saida cikin y girma,amma bazaice ga matsalan ba,hankalin lamee ne ya tashi tace,boka ayi hakan ba matsala.
Dawowa gida sukayi daga nan suna jiran abunda zai kasance.
Fulani ta lura da cewa walwalar lamee da dan dawo,nanfa hankalin ta ya tashi,dan tasan na haka ta kyaleta ba.
Take taje ta bawa fiddausy lbrin duk abunda yake ciki,addu'a suka karbo ta sihiri fulani take sha,
Bayan wata daya,wato watan haihuwar fulani shiru shiru bata ga wani alamun haihuwa ba.
Malam Ahmadu ma yasha mamaki dan gashi ciki yana neman shiga wata na goma,Asibiti suka je aka duba,doctor yace lfyan baby kalau yake kawai de haihuwar ce bata zo ba kuma irin haka yakan iya faruwa har akai wata sha daya ma,balle kuma su da suka sami matsalan zubewar ciki abaya.
Da wannan hankalin fulani ya dan kwanta suka dawo gida.
Bayan wata daya saiya kasance fulani ta fara wani mugun ciwon ciki da baya,ga cikin ya kara wani irin girma,kullum ciwo,before ta dauka na nakuda ne ma,amma daga baya taga akasin haka,koda suka je asibitin ma haka suka ce ba haihuwar bace.
Kafin sati biyu tayi wani irin baki da rama duk ta fita haiyacinta,daga nan abun ya fara bawa malam Ahmadu da fiddausy tsoro,dan har sun dawo asibiti ma,fiddausy tana zama a wajanta.
Take malam Ahmadu yace ,da wannan wahala da take sha kawai gwara an maata cs an ciro da baby,na'am doctor yayi da wannan shawarar dan shima yaga cewa dakyar indan zata iya hsihuwar da kanta.
Ranar cs aka saka nan da kwana 3 ,kuka fiddausy da fulani sukai tayi ,fulani tana ta fada mata abubuwan da take ganin kamar na bakwana ne,Dan harce mata tayi idan mukhtar ya girma ya nemi yar uwarta tilo hajjo,dan ita kawai ta rage masa amatsayin mahaifiya,rufe mata baki fiddausy tayi tana ce mata in sha Allah zata ma tashi da kafafuwanta.
A bangaren lamee kuwa,dadi kamar me ya isheta dan gani take jaririyar cikin fulani tuni ta mutu,ko dan irin turun kule kulen da boka yasa aljanunsa suka yi acikin fulani.
A rana ta biyun ne wata irin nakuda ta zowa fulani bayan wasu addu'oi da fiddausy tasa aka tofo mata,take doctors suka tsaya akanta,ba karamar wahala tasha ba kafin kyakyakyawar yarinyar ta ta fado duniya ba,saide yarinyar ko kuka bata yiba,take doctors suka fara bata taimakon gaggawa,Fulani kuwa tana cikin wani mawuyacin hali,dan sun dauka ko yan biyu zata haifa ganin cikin ko alamun komawa baiyiba bayan fitowar jaririyar,ga wani irin motsi da cikin yake yi.
Nan suka shigar da ita operation room dan su fito da daya babyn,dan azaton su ko kasa fito babyn yayi,koda suka farka mata cikin abun da suka gani ta basu mamaki,dan kuwa kayan tarkacen kayan ledoji da wata katuwar leda da ruwa aciki daidai saitin mahaifarta nan suka fito da wadannan tarkace,likitocin ba karamin mamaki suka shaba,wato dai dagaske ana yiwa mutum turo abubuwa acikinsa,ko ta hanyar jinnu ko kuma mayu.
Bayan sun gama operation ne din suka kai fulani dakin hutu dan har yanxu bata farfado ba.
Malam Ahmadu kuwa kuka kawai ya fashe dashi lokacin da doctor uzairu ya nuna masa abunda aka ciro acikin matarsa,mamakin mugun da yayiwa fulani wannan turan yake,Allah Allah yake kawai ya ganta.
Bayan 30min kuwa ta farka tana a kira mata baban mukhtar,take kuwa ya shigo dakin cikin wani irin yanayi,yanayin daya tarar da ita shiya kara bashi tsoro.

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now