The Unexpected Accident😔

241 12 0
                                    

Isar su lamee gida suka san cewa tabbas fulani ta rasu,dan mutane ne babu iyaka a wannan kofar gida nasu,da hsnzari suka samu suka shiga gidan.tym din malam Ahmadu yana mata wanka a toilet da shi da yayyinsa mata biyu,yana yi yna kuka,fiddausy ma tana dakin ta kasa kwance ta kasa tsaye,tym din har bilkisu ta fara kukan neman abinci.dan haka abun saiya hade mata bayu,ga rasuwar aminiyarta ga kuma tausayin jaririyar da aka barmata amana.
Bangaren su lamee kuwa samun kanta tayi da hawaye suna zubo mata,dan bata taba tunanin cewa fulani zata rasu ta hanyar haihuwa ba,ita dama burinta cikin karya samu damar rayuwa.
Take tayima kanta tambayar toh wai shin yarinyar ma ta rasu?
Nan take gabanta ya fadi,ji tayi an dafa kafadarta,juyawa tayi taga balaraba.
Hawayen face dinta ta goge sannan ta fuskanceta.
Balaraba jiki assnyaye tace ina kika shiga lamee ina ta neman ki tun dazu?
Sauke ajiyar heart tayi tace,ramlatu aka kwantar za'a mata aiki a asibiti,harma sun shiga aikin yanxu.
Wanda irin aiki kuma lamee?
Sukuyar dakai lamee tayi tace,cire mahaifarta za'a yi dan ta samu matsala.
Jiki assnyaye balaraba tace,Allah y bata lfy lamee,ita kuma fulani Allah y jikanta.
Jiki sanyaye lamee ta amsa da Ameen.
Bayan malam Ahmadu ya gama shirya ta tsaf,y kira fiddausy ta mata addu'a ,kiran lamee yayi,kuka ta fashe tace malam idan naga fulani akwance ba rai faduwa zanyi nasan awajan,jiyo wa malam Ahmadu yayi yaga mukhtar ya rike mashi bayan rigarshi idanuwanshi sunyi jawur dan tsabar kuka cewa yayi,baba ni bazan fadiba ka kaini nayiwa mama addu'ar,goge hawayen fuskarsa malam Ahmadu yayi yace muje,biyo su shima kabiru yayi yana goge kwalla dan sai yanxu abun ya bashi tausayi sosai.
Isarsu suka mata addu'oi,dakar aka cire mukhtar daga kanta sannan aka fitar da gawar waje aka sallaceta aka kaita gidan gaskiya .
Malam Ahmadu lokaci guda yayi wata uwar rama.
Bangaren ramlatu kuwa Alhamdulillah anyi aiki lfy farfadowa ne kawai y rage tayi.
Fiddausy kuwa jaririyar na fara kuka zata bata madara,kuma Alhamdulillah tana sha sosai.
Har ranar uku malam Ahmadu da fiddausy mutuwar fulani bata sake su ba,dan kullum sai sunyi kuka ,mukhtar kuwa yana ganin mama fiddausy ta fara shima sai ci gaba,dan yanxu rai da rai yana wajanta sai dare kuma ya tafi wajan babansa ya kwanta.
Bangaren ramlatu ba karamin rama Tainan wanda tunanin da take yine ya jawo mata wannan rama ,da taji lbrin rasuwar fulani kuwa ba karamin kuka tayi ba tare da nadamar tsaurin idon ta tayi mata tun tana yarinya.
Ahakaa de tayi kwana uku aka zallamota ta taho gidan su .
Bilkisu kuwa Alhamdulillah madara ta kar beta dan baza kace bata shan nono ba.
Komai nata ya koma wajan fiddausy,mijinta ma yana son yarinyar sosai.
Lamee kuwa ba karamin mamaki tasha ba jin cewa yar gidan fulani na nan kalau bata rasuba,gashi har an bama fiddausy rayinyar.
Ahka har akayi sadakar bakwai inda daga nan kowa ya watsae.
Malam ahmadu kuwa har yanxu ankasa gane kanshi sabida yawan damuwar da tayi masa yawa,wannan ya jawo har juninsa yahau
Mukhtar kuwa komai nasa ya koma wajan babansa hatta kayanshi duka yayi parking dinsu a dakin babanshi,kulum kuwa awajen fiddasy yake yini yana faman yiwa bilkisu wasa dan yana son yarinyar sosai kuma ko da yaushe wasiyar maman su na ransa shiyasa koda yaushe yarinyar ke kara shiga ransa .

Kabeeru kuwa tun banyan rasuwar fulani abubuwan kasuwancinsu da sukeyi da lamee ya fara tabarbarewa,yau ayi asara gobe ma asara,shikanshi abun ya daure masa kai,ya rasa da ina Matsalar ta faro,har yanxu kuma yaki fadawa kowa,ga yasa yaransa duka a makaranta mai tsada,a haka dai ya ya ci gaba da abubuwansa.
*************************************************
Lamee abubuwan ma sun mata yawa dan ta kasa gane kan ahmadu dan tun bayan rasuwar fulani ya kasa dawowa daidai,kullun baida lamiya,ta kasa gane kansa,inbanda yasa mukhtar a gaba suna hiraa.
Dan haka wani tsanar yaron ne ma ya kara darsuwa aranta,dan sai yanxu taga ma cewa ba komai da yake nuna masa da fulani na raye kan yanxu,dan ko fareeda baya bata kulawa kan mukhtar,komai shidai mukhtar.
Haka xuciyzrsa ta dinga ingizata har ta kira balaraba tace mata taxo suna da maganar yi.
Da yamma balaraba ta shigo ta sameta ta fada damuwarta sannan ta kara da cewa,so nake mu koma wajan boka assn yarda za'ayi,sauke ajiyar heart balaraba tayi tace,aike inaga naki mai sauki ne lamee,domin kuwa ni yanxu gaba ki daya na kasa gane kan alhaji sai wulakanci yake min,da alamun wannan shigiyar a garin neman mata magani aka karyamin asirin gaba ki daya,dan haka dole mu koma wajanshi.
Lamee ce ta ce,ammafa gaskiya ina tsoron abunda ya faru ya sake afkuwa dan kuwa abundda boka ya fada na cewa aiki zai yiwu amma nima zai shafe ni,gashi ya afku.
Kallonta balaraba tayi tace kamar yaya?
Kamar yadda ramlatuna ta daina haihuwa gaba daya ,hakan ya nuna cewa yana da nasaba da asirin da nasa aka aikatawa fulani,sai gashi nima Allah ya jarabci tawa yar.
Murmushi balaraba tayi tace ,ashe kema kin fuskanta,ai shiru nayi naji ko kinyi nadama ne ko kuma Aa.
Anan suka saka ranar xuwan nasu.
Bangaren fiddausy kuwa ba karamin kulawa suke bawa bilkisu ba,yarinyar gaba daya kamanninta da mahaifiyarta ya fito gashi sai kara girma da wayau take yi.
*************************************************
Bayan wata biyar abubuwa da dama sun faru inda mukhtar ya kamu da wani matsanancin ciwon mara mai karfi wanda idan ya tashi mishi,tofa kwana za suyi babu bacci ,hakan kuwa yana da nasaba ne da asirin da lamee tasa aka yi mishi dan kwatakwata bazai iyayin tarayyar aure da mace ba ballanta ya samu damar aure har kuma ya haihu nan gama tunda ta sanadiyyar cikin sa tane ta rasa har yayan guda biyu,dan haka shi kuma tasa amasa asirin da zaman auren ma da mace bazai iya ba ballantana ya samu har ya haihu,tanan kawai take ganin zata iya rama abun da ya faru tunda har yanxu babu wata kiyayya da malam Ahmadu yake nuna masa dukda boka yayi iya bakin kokarinsa dan yaga cewa ya raba tsakanin mukhtar da babanshi kuma amma hakan bai yiwuba.
Wannan lamarine ya kara tashin hankalin malam Ahmadu harya kwanta rashin lfy,zuwan farko kuwa da yayi asibiti akace mugun hawan jini ne ya kamashi,saida sukayi sati daya sannan aka sallamosu.
Kabiru kuwa yanxu har lamee ta fuskanci halin da yake ciki domin kudin da yake yawan kawomata yanxu babu shi,bayan sun zauna ne yayi mata bayanin matsalar da ake ciki,ta shiga damuwa sosai amma saita kwantar masa da hankali tace karya damu komai zai daidaita nan ba da dadewa ba,amsawa yayi da Allah yasa sannan ya kama hanya zai tafi.
Bayan fitarsa daga dakinne ta kira balaraba ta fada mata halin da suke ciki,dan haka zata rakata wajan boka dan yayi wani abu akai dan kuwa da wannnan business din take rufawa kanta asiri,saka ranar xuwa sikayi sannan ta kashe kiran.

Hankalin fiddausy kuwa yanxu ba'a kwance yake ba ganin wulakancin da mijinsu yake mata,ga kuma larurar mukhtar wanda take kyautata zaton da hannun lamee aciki,dan haka tana bukatar kudee awajan mijin nasu dan tasa ayiwa mukhtar addu'oi,gashi kuma ko saurarenta baya yi,wannan ne yasa har yar rama tayi yanxu,amma bilkisu kuwa Alhamdulillah ta kara girma sosai da wayau.
Dan haka ta kara dagewa da addua kan Allah ya saukaka mata.
************************************************
Malam Ahmadu kuwa babban damuwarsa yanxu bai wuce mukhtar ya zamu saiki ba,sannan har yau yana mamakin abubuwan turan da aka yiwa fulani tym din da aka mata cs,danshi har yau bai taba zargin cewa lamee ba,dan asaninsa bata xuwa wajan boka,Dan haka ya ajiye abun da cewa mayu ne suka kama masa fulani lokacin da tana raye har suka mata wannan tureen,kuma har yau baiyiwa kowa wannan zancen turenba inbanda fiddausy data sani.
Dan haka wannan ciwon marar na mukhtar ya fara dan gan tashi da kodai mayunne still suka dawo masa kan mukhtar,dan haka tuni ya fara bashi adduoi yana sha kullum bayan an sallamosu daga asibiti,kuma Alhamdulillah ciwon cikin na lafa dan yanxu har ya koma school ,sai dare ciwon take tashi,shima kuma da zarar ya tofa masa addua zai samu yayi bacci.
Dan haka wannan saiya kara sa malam Ahmadu yayi zaton ko mayunne,sabida haka yasa aka karbo masa maganin mayu ya fara turara masa.
Aranar da su lamee suka je wajan boka ranar ne malam Ahmadu ya shiga part dinta yana nemanta ya tarar bata nan,dan haka ya kirata a waya lokacin suna hanyar dawowa,kuma ita take driving don kuwa balaraba ta koya mata,picking tayi tace masa gatanan ahanya dawowa,fada ya farai mata akan me yasa zata fita bata tambateshi ba,Jin horn din da ake yi mata yasa tayi sauri ta kashe wayar,aikwa kafin ta ajiye  wayar motar dake bayanzu ta bigi tasu,suka cikin daji,nan fa suka fara ihu a cikin motar,
Motar ta bigi wata katuwar bishiya,take balaraba ta kwalla wata kara sabida buguwar da tayi,jin karar balaraban shiyayi sanadiyar firgicewar lamee itama.
Take duka suka suma,sai asannan jama'a suka taro aka fara kokarin foto dasu ganin motan ta fara kamawa da wuta.
Dakar aka samu damar fito dasu,akayi asibiti dasu.
Hankalin malam Ahmadu bai kwanta ba jin kashewar wayar da lamee tayi,nan kuwa ya kara kiranta,yaji tana ringing ba'a dauka ba,nan kawai ya hakura ya koma part dinsa.
Bangaren su lamee kuwa ba karamin ciyuka suka jiba,dan balaraba ma tayi kara ya har tara ajikinta gashi duka fuskarta ta canza kamar ba itaba,lamee ita tayi karaya biyu a kafarta.
Haryanxu kuwa basu farka ba,
Ana haka ne sai ga number kabiru yana kiran maman tashi,doctor ne yayi picking ya sanar dasu abun da ake ciki,take hankalinsa ya tashi ya taho asibitin,ganin halin da suke ciki yasa kabeeru kawai ya fara kuka,dan gani yayi raunikan sunyi yawa kamar mutuwa za suyi,anan ya kira malam Ahmadu ya sanar dashi halin da ake ciki.
Hankali tashe malam Ahmadu ya taho asibitin sannan ya sanar da hameesu halin da ake ciki,da mamaki yake tambayar malam Ahmadu ina suka je har sukayi accident din?shiru malam Ahmadu yayi sannan yace wlh nima bata fada min zata fita ba sai shigo nayi na riske bata nan,ashe kaima bata sanar da kai ba,eh professor hameesu yace sannan suka kashe kiran.
Professor hameesu da fiddausy tare suka tafi asibitin hankali tashe,lokacin da suka isa suka tarar ramlatu tana kuka a harabar dakunan,dan itama kabiru ya kirata yasanar da ita.
Hakuri firdausy take bata tana rarrashinta.
Jin ihun da balaraba take shiya ankarar dasu suka nufi dakin da sauri,ganin halin da take ciki yasa kawai fiddausy ta fashe da kuka ta isa wajanta tana mata sannu.
Ihu take iya karfinta,hawaye professor ya fara shima sanin cewa ba karamar azaba take shaba,doctor ne ya shigo dakin ya nufi wajanta yana mata sannu dan har yanxu basu gama daura taba,daurin kara biyar sukai yanxu,hudun jira sukai ta tashi suga yana yin jikin nata kafinnan suyi mata.
Ramlatu ma tsayawa tayi tana kuka dan saita ga cewa gwara jikin mamansu akan jikin balaraba.
Ife ife balaraba ta fara kamar zararriya tana mutuwa zanyi 😭😭😭wayyo ku kyaleni,lamee kin cuceni kin kaini ga halaka,gashi karshena ya zo,wayyo jikina ba'a jukina yake ba,Ya Allah ka bani lfy,Allah na tubba,bazan sake xuwa gurin boka Ya  Allah,Ya ka dawo min da lfy ta!!!
Haka taringa surutai tana kuka.
Shiru professor ,fiddausy da ramlatu sukayi,suna mamakin abunda balara take furtawa da bakin.
Nan gaban ramlatu ya fadi,jin maganganun da balaraba ta fada kan lamee,ficewa tayi hankali tashe tayi dakin da lameen take,dan she can't believe mamanta na xuwa wajan boka,dukda ba zancen zata mata ba yanxu,amma tana fatan cewa tsanin ciwon da balaraba take jine yasa ta fara surutai irin wadannan.
Jiki ba kwari ta bude dakin ta shiga,tararwa tayi babanta da kabeeru zaune kusa da ita suna mata sannu,dan sai yanxu ta samu farkawa.
Kallon uwar tayi jiki asanyaye tayi mata sannu da jiki,yauwa ta amsa mata sannan doctor ya shigo ya duddubata yaga cewa bata sauran karaya biyun da suka gani kawai sune,takadda ya bayar ta siyan magani,fita kabeeru yayi yaje domin siyowa maganin.

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now