His death

248 13 3
                                    

Kuka sosai lamee da ramlatu suka sha,dakyar kabeeru ya lallabasu suka tashi suka tafi part din lamee,dan ko shi mamansu ta bashi tausayi.
Fareeda ce suka dawo daga school ta shigo dakin da gudunta,ganin mamanta da ramlatu na kuka yasa itama ta fara,rike hannun maman tayi tace,mama me aka miki?dagowa lamee tayi ta kalleta tace "sanadiyar kishiya ne ya jawo min wulakanci fareeda,ina rokon Allah ya rabaki da kishiya,kar Allah yasa ku shiga tashin hankalin da nake gani,duk kuma ta dalilin kishiya "kallonta ramlatu tayi tana jijjiga kai ganin tana yiwa fareeda magana kamar da wata babba.
Shiru fareeda tayi tace "amen mama,kema Allah ya yaye miki damuwa "fita tayi da guduu,tace "na tafi wajen mukhy (sunan da take fadawa mukhtar kenan)y koya min assignment.
Shiru dakin ya dauka,sannan lamee ta dago fuska ta kalli ramlatu tace "wato cin mutunci da babanku yamin banta tunani ko a mafarki zai iya furtamin saki ba,amma ba komai.kema kuma ki tattara yau basai gobe ba ki koma gidan mijinki kafin ya rako ki takaddar kema tunda dai na warke "
Washe gari kuwa ramlatu ta tattara ta koma gidanta dan dama ta gaji da ganin bacin ran gidan.
Malam Ahmadu kuwa kullum ciwo ya tafi ya dawo sabida damuwar rashin lfyar mukhtar.
Haka rayuwa ta cigaba yau sauki gobe sauki,kabeeru ne yake dawainiya dashi,dan yace baya bukatar temakon lamee dukda itama daya kafar dingisa ta kawai take yi.
A yaune lamee tayi wata uku,wato ta gama iddarta kenan,ranar bakaramin kuka taci ba,ganin harta yi period uku amma malam baiyi zancan komenta ba,
Da professor yaji lbarin sakin awajen malam Ahmadu baiji dadi kwata kwata da hukincin da ya yanke ba.
Bayan kwana biyu da idda,ta isa dakin malam Ahmadu,ta same shi kadai yana amai,lokacin kabeeru ya dan leka gidansa.
Hankali tashi ta isa wajensa tana masa sannu,hannu ya daga mata alamun kada ta ta bashi.
Ja baya tayi tana kallonsa dan ya galabaita sosai,kallon shi tayi tace "Dan girman Allah malam ka yafe mini laifin dana maka,koda bazaka mayar dani dakina ba to kaya fe mini.
Kallonta yayi numfashi na fita dakyar yace "bani zaki nemi gafara ba lamee,dan karamin yaron da kika sa aranki shi zaki nemi gafara idan hankalinsa ya kawo,idan ya yafe miki to nima na yafe miki idan kuwa baiyi ba,nima ban yafe miki ba lamee,kuma a tambayar yafiyar da zaki masa saikin masa bayanin me kika masa,dan kuwa shi yaro ne yanxu,ko na masa bayani ba ganewa zaiba "kallonsa lamee tayi tana hawaye tace "shikkenan malam,amma ka tina koda Allah mu nayi wa lefi kuma ya yafe ballanta wannan "baki sake yake kallonta yace "dan wannan din da kike gani shi zai iya kaiki ga wuta,tunda hakkinsa ne,kuma ma gana uwarsa "
Gabanta ne ya fadi,ta xube awajan tace "in sha Allah zannemi ya fiyarsa malam,in kuma nima na rasu kamin ya mallaki hankalin sa zansa yayana su rokarmin shi,tunda har ka dauki abunda zafi haka "ko kallon inda take bai sake ba.
Wani ciwon girji ne ya taso masa,tuni ya fara amai again,😳gabanta ne ya fadi maimakon aman abinci saiya fara na jini,hankali tashe tayi hanyar waje dan kiran kabeeru ,sai gashi sunyi kicibis a hanya.
Da gaggawa suka kaisa asibiti,tym din baisan inda kansa yake bama.
Dubawar farko ya ga xuciyarsa tana last stage na bugawa,professor hameesu kabeeru ya kira ta fada masa halin da ake ciki.
Lokacin suna fita shopping da fiddausy,daga nan suka zarto asibitin.
Ganin halin daya ke ciki shima hakalinsa ya tashi.
Sunzo zasu tafi ne,Allah ya bashi ikon farkawa yaga su professor,da bilkisu a hannun fiddausy wadda ta girma sosai,meko hannu yayi ya karbeta,aikwa yarinyar ba kiwa taje,shafa kanta yayi sannan yayi mata addu'a ya tofa mata,kallon fiddausy yayi yace "na gode da dawainiyar dakike da yata,saide ina kara neman alfarma daya awajanki,ina so mukhtar ko bayan raina shima ya dawo wajanki,ki kullan min dasu duka.hawaye fiddausy ta goge tace "in sha Allah ba komai malam,na gode da yarda da tarbiyyata da kayi.
Karbar bilkisu tayi sannan sukayi sallama suka tafi.
Bayan kwna biyar da zuwan su asibiti,yaran fiddausy suka isheta da sai anyi celebrating birthday day din billy na one year,cewa tayi baza'a yiba sai an sallamo malam Ahmadu daga asibiti.
Aranar ne kuma malam Ahmadu ya dage sai an sallamoshi dukdaa jikin nasa ba wani sauki yayi,amma haka suka dawo gida.
Mukhtar da murna ya fadawa momy wato fiddausy cewar an sallamo baban su.
Aranar kuwa da daddare suka je sukayi duk wata siyayyar da yaran suka bukata,aka siyowa bilkisu birthday gown dinta mai kyau.
Washe gari ya kasance Friday,ranar da fulani tayi shekara daya da rasuwa,aranar ne kuma ya kasance birthday din bilkisu.
Yaran nata murna zasu ci cake,bayan an gama birthday dinne,suka sha hotuna,sannan kowa ya koma gida,wato yan class din su mukhtar da suka gaiyaato.
Da daddarane bayan sallar isha jikin malam Ahmadu yaki dadi,kuka lamee ta dunga yi,dan ko iya magana baya yi sai salati kawai.
Mukhtar ne ya shigo dakin dan ya nuna masa hotunan da sukayi,ya tarar baban ba lafy, da hanzari yayi wajensa ya zauna,kamo hannunsa malam Ahmadu yayi yace,Allah yayi maka albarka,ya kare min kai daga sharrin masu sharrri,y buda maka,y kuma baka hakuri fin na mahaifiyarka. Ameen mukhtar ya amsa dashi yana share hawaye yace "baba mu tafi asibiti dan Allah "jiyowa yayi ya kalli lamee yace "mama mubar kuka akai baba asibiti " kuka lamee ta ci gaba dayi sanna tace "je ka kira professor ya kaimu asibitin,kabiru baya nan" da saurinsa ya tashi domin kiran professor.
Fitarsa da biyu kuwa malam Ahmadu fara salati,jin shirunsa yasa lamee ta matsa tana ta bashi ganin kamar baya numfashi,hankali tashe ta fita dan kiran professor da kanta,kicibis sukayi,nana yaxo kan malam Ahmadu ya tabbatar cewa,Allah ya karbii abunsa.
Ba karamin tashin hankali suka shiga ba,tuni aka sanar a masallaci cewa Allah yayiwa malam Ahmadu rasuwa ,gobe da safe za'ayi Jana'izarsa.
Fiddausy ba kadan tayi kuka ba,wato shekara daya tsakaninsa da fulani,wani tausayin yaransu takeji,suna yara zasu taso cikin rashin iyaye,amma tayi alkawari in sha Allah zata zamee musu uwa professor kuma uba.
Bangaren ramlatu da kabeeru ma sunsha kuka,lamee kuwa kafin washe gari ma bata san inda kanta yake ba,har aka kai shi makwancinsa.ya rasu juma'a aka kaishi asabar kowa yana yabon kyawawan halinsa.
Bayan bakwai kuwa,komai na mukhtar ya koma gidan professor hameesu,haka zalika rabon gado ma da akayi shi aka dankawa komai dan ya rike musu.
Lamee kuwa taci kuka har hawayeenta ya daina xuba.
Haka akayi rabon gado babu ita.
Haka rayuwa taci gaba mukhtar yana jin da din zaman gidan professor babu ta kura babu komai,idan ya tina da babansa fiddausy tana kokarin kwantar masa da hankali,sannan tun dawowar shi suka ci gaba da neman masa maganin sanmu,kuma Alhamdulillah acikin 100 na ciwon 40 ya ragu.
**************^^^^^^*************************
A gurguje,bayan wasu shekaru,mukhtar ya samu scholarship ya tafi uk karatu,agidan yayar fiddausy yake zama,wadda suka koma uk  da zama ta dalilin aikin mijinta.  Mijinta ya kasance balaraban egypt sai yazo uk karatu,suka hadu da hajiya rahama wadda tazo karatu daga Nigerian,anan fa Allah ya hada su harta kai ga aure,suke zama kuma a uk din dalilin daukar shi mijin nata aiki da akayi a university din da suka gama.wannan yasa yayan su suka kasance half cast.
Jikin mukhtar kuwa Alhamdulillah tunda professor hameesu ya kai shi saudiya aka masa addu'oi sosai ya samu saukin abun a month baifi ya tashi sau daya ba shikkenan.amma dai a matsayinsa na saurayi baisan wani abu waishi feelings ba,dukda ansanar dashi cewa ,inhar ya dage dashan magani to in sha Allah,zai dawo normal kamar ko wanda namiji,sannan professor hameesu yana kaisu yola atimes su gaisa da yan uwa,dukda duk zuwan da suke basu taba jin lbarin yayar fulani ba,sabida kowa yayi neman harya gaji,sannan har yanxu mukhtar bai fasa addu'ar Allah ya baiyana musu ita sabida and yasan mamanshi da ita ta rasu aranta.
Agidan hajiya rahama,wato yayar fiddausy,Allah sai ya azirtasu da mata biyu kawai,daga nan haihuwar ta tsaya.
Zuwan mukhtar gidan saiya zame musu kamar yaya,zainab ce babba and shes 22 sai kuma ummukhultum 18 wadda ta kasance yar auta.
Rayuwar uk agidan su khultum na masa dadi sosai dan sun dauke shi kamar yaron da suka haifa,idan ciwonsa ya tashi to tare suke jinyar da khultum dan itama kwana zata yi tana kuka,dan yafi shiri da ita sosai.
Jin irin larurar dake damun mukhtar da babansu khultum yaji ,bakaramin tausaya masa yayi ba,sannan shima yasa aka fara bashi magunguna,tuni ya fara samun lafiya,lafiyarsa ta fara samuwa kamar ko wanda da namiji,daga nan nan ya samu ya kammala karatunsa na engineering,ya fara aiki uk din,Allah ya hada su soyayya da khultum wanda itace tun farko ta nuna hakan,kuma yayi accepting,tuni aka saka ranar auransu tare dana yar uwarta zainab.
Bangaren gida Nigerian kuwa fiddausy ba karamin dadi ta jiba jin hadin mukhtar da yar yayarta.
Nan ma bilkisu ta girma ta fara zama yan mata,sabida kokarin ta akayi mataa jumping din class har biyu yanxu haka tana sss1 tana gamawa kuwa fiddausy tace zata hadata aure da yusuf ta cikawa fulani burinta,dan shima yanxu haka aiki sukeyi da shi da manyan yayan balaraba.
Ita kawai yake jira tayi graduating dan yana son billynsa sosai.
Bangaren lamee ma abubuwa da dama sun faru bayan rasuwar malam Ahmadu,kabeeru kasuwancinsa yaki dadi,daga karshe sai mukhtar ne yake temakaa masa da wasu abubuwan,ramlatu dai Alhamdulillah tana saune agidan mijinta,ta kuma rungumi kaddarar ta rashin haihuwa tana zaune kalau da kishiyarta.
Lamee ta aurar da fareeda,wadda da farko ta fara fuskantar matsala agidan mijin,inda yaranta biyu tana haifa suna rasuwa aranar da aka haifesu,kuka lamee tayi tayi,dan kawai tayi zaton itama alhakin fulani ne yake bin yaranta.
Dan haka take ta kira mukhtar tayi masa bayanin abubuwan data mashi shida mahaifiyarsa,tana kuka tana neman gafararsa akan ya yafe mata,dan kuwa malam Ahmadu yace inhar bai yafe mata ba to shima bai yafe ba .
Jikin mukhtar asanyaye dan shi dama fiddausy ta bashi lbarin silar ciwon cikin da ya ke,tuna nasihar mahaifiyarshi kuma ya karasa ya yafe wa lamee abunda ta masa.
Daga nan ne mukhtar ya budi baki yace "na yafe miki mama,Allah ya yafe mana tare "kuka lamee tayi sannan kuma ta masa godiya.
Dan haka bayan komawar fareeda gidanta daga asibiti sirikarta  ta kafa warning cewa ,wlh inhar ta kara haihuwa ba'a samu jaririn ya rayu ba to gaskiya saita aura masa wata yarinyar a family dan ita jikokinta take son gani kafin ta rasu.
Nan fa hankalin lamee ya tashi,dan duk yarda za'ayi bazata bari ayi yarta kishiya,dankwa ita tasan zafin kishiya,da kuma abubuwan da ta aikata kuma take nadama sabida kishiya.
Dan haka tuni ta dage da addu'a,Allah yasa next cikinda fareeda zatayi jaririn ya rayu,dan kuwa ita tayi hannun riga da zuwa wajan boka ballantana taje ayiwa sirikar fareedan asiri.
Haka suka ci gaba da addu'a daga ita har fareedan.
Cikin ikon Allah kuwa fareeda ta sake samun cikin na uku,sunyi farin ciki sosai.
Likacin da cikin yakai wata 8 lamee ta daukota tace zata ci gaba da bata kulawar daya dace,aikwa nan take suka taho gida lamee ta ci gaba da kula da ita.
Dan tace rashin cikakkiyar kulawa ne yasa wadancanma suka rasu,da kuma rashin tafiya asibiti dazarar nakudar ta taso,sai harta galabaita ita da dan.
Nan dai fareeda ta ci gaba da zama a gida har watan haihuwarta yaxo,ranar data fara nakuda da safe suka tafi asibitin da wata kawar lamee take aiki acan,dan tace saita fi bata kulawa.
Xuwansu asibitin kuwa Dr hinde tana kan karbar haihuwar wata yarinya da bazata wuce sa'ar fareedan ba,yan biyu zata haifa daya ya fito daya kuma bai fito ba,dan kokarin shigar da ita cs suke,yarinyar abun tausayi gashi haihuwar farii ta galabaita sosai,dan bata san inda kanta yake bama.sai kuma ga yar kawarta still an kawo ta haihuwa wajanta,umartar nurses din tayi da su shigo da fareeda kafin yan uwar yarinyar su cike paper din cs din.

Wajan fareeda ta nufa ta fara karbar haihuwar fareedan,aikwa cikin ikon Allah itama daya yarinyar daza ayiwa cs din ta saki wani nishi,tuni suka haihu tare da fareedan.cikin  ikon Allah itama fareedan ta haihu,wanda bakaramin galabaita tayi ba.
Hankali lamee a professor a tashe,tana jiran ganin jariri.
Bayan awaya daya aikwa saiga dr hinde,da kyakykyawan jariri fari sol,ta dankawa lamee ,da hanzari ta am shi yaron ta kalleshi tana hawaye tana nuna farin ciki sosai,godiya tayiwa hinde sosai,sannan ta tofe shi da addu'a Allah ya raya shi.
Fareeda kuwa saida taci baccin gajiya ta koshi sannan ta farka.

Me ko mata jaririn lamee tayi cikin farin ciki tace,kalli yaron nan harya ninka ki kyau.
Rufe fuska fareeda tayi cikin jin kunyw tanawa Allah godiya daya raya mata wannan.
Tuni aka kira mujinta aka sanar dashi zancan haihuwar.
Yayi murna sosai,mama (sirikarrta)harda kukan fareen ciki,tuni kuwa ta manta da batun wani kara auren data ke so yayi.
Ranar suna aka sawa yaro Muhammad,yaci sunan kakansa kamar yarda fareeda ta bukataa.
Da lamee taji sunan da aka sa masa batayi farin ciki ba,cewa tayi,da ta bari mijin fareedan yasa sunan nashi baban da farko tunda shima ya rasu,in yaso daga baya idan taa sake haifar namiji saita saka sunan mahaifinta.
Haka lamee ta hakuri tunda dai har an riga da an yiwa yaro huduba.
Haka rayuww ta ci gaba,Muhammad dan gidan fareeda  yana da shekara 10 akayi auren mukhtar da khultum,sanin girman mace da na miji ba daya ba ,shiyasa fareeda ta rigashi aure da wuri.
Lokacin da mukhtar yayi aure yana shekara 35 khultum kuma 18 ,tana 19 ta haifi sarah first born,and after 3 years Allah ya azurtasu da zarah wadda yasa sunan mahaifiyarshi wato fatimatul zarah (fulani)  ,Atare suke haihuwa da khultum tym din da zata haifi sarah shine  ita yarinyar tata ta rasu,and second haihuwar ma da khultum zata haifi zarah,tare suka haihu,ta sake haifar mace .tun daga nan bata sake haihuwa ba sai bayan 2yrs ta sake samun wani cikin daga nan ta haifi namiji ,daga wannan kuma haihuwa ta tsaya mata.
Khultum ma tun daga kan zarah bata sake ba.
Bangaren bilkisu da yusuf kuwa yaron su daya.
Wannan kenan.
Yanxu haka mukhtar da khultum suna zama a uk da yaransu sarah da zarah,basu cika cuwa Nigerian sabida school din yara.zarah kuwa bama tasan Nigerian ba,coz tun bata da wayau data je bata sake xuwa ba.

Saikuma bilkisu da yusuf suma na kano suna zaune da yaronsu dan 8yrs .
Sai kuma fareeda da mijinta sun dawo Saudi da zama da yaransu 3.
Ramlatu ma na gidan mijinta,kabiru kuwa yanxu yaransa 7.
Allah yayiwa lamee rasuwa sanadiyar ciwon kafar daya tasan mata,wanda mukhtar ne ya dauki dawainiyar kula da ita har Allah yayi mata rasuwa,tym din su fareeda satinsu 4 da komawa saudiya Allah yayi mata rasuwa.
Taso su gamu  da fareeda amma Allah baiyiba,harta cika tana kiran sunan fareedan.ramlatu taci kuka sosai,ta hakura.
Bayan fareeda taji labarin rasuwar lamee bakaramin kuka itama tasha ba,sunxo gaisuwa Nigerian,nan ramlatu ta bata lbrin irin nadamar abubuwan da lamee tayi da kuma son ganawa da fareedan da tayi.taci kukanta ta shafe sannan suka tattaro suka dawo saudiyya.
Fiddausy da professor hameesu duka suna zaune agida nageria yanxu ba kowa agabansu sunyi wa kowa aure,sai jikoki dake xuwa hutu.
************************************
Anan na kawo karshen lbrin asalin su zarah.
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️Toh yanxu wasan zai fara ,KECE RAYUWA Ta,zai xo muku da salo daban daban,u guys will enjoy it for sure.

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now