Family❤️

498 19 0
                                    

Alhaji mukhtar shine mahaifin su zarah wanda yake haifaffan dan Nigeria ne ,su biyu ne a wajan mahaifiyarsu ,wato shida Hajia Bilkee .fararen bafulatanai ne,wadda yake mahaiyar tasu ce bafillatanar baban su kuma bahaushe ne ,kyaykykyawane ajin farko ,wanda harya kasance yan ubansu suna jin haushin hakan,maihifiyar su wadda ake cewa fulani (yar fulanin Adawa ce)mace ce mai hakuree da juriya,itace amarya agidan mahaifin mukhtar malam Ahmadu,yana tsananin son fulani saboda ita yarinya ce zuwan ta,domin kuwa alokacin ma yaran uwar gida lamee su Hudu ne maza 4 sai  mace mai suna lamratu.toh a haka fulani ta shigo,malam ahmadu ya samo tane sanadiyar wani iftila'i daya saukar musu na ruwa,wanda ruwa ya dinga shigowa garinsu saida ya kawowa manya har wiyansu,dabbobi kuwa duk saida suka halaka wasu ruwa ya tafi dasu,kananun yarama da yawa sun rasa rayukansu ,Dan haka fulani tana daya daga cikin wanda ta rasa iyayenta duka biyun sanadiyar faduwar gini su biyun duka suka rasu,sai yayarta hajjo,wadda bata san inda ta shiga Ba,Dan ita ko rasuwar iyayen nasu bata da lbri.Haka fulani ta dinga yawo a kyauyuka kala 2 domin garin nasu ma an tashe shi sabida duka gidaje sun rurushe ba wajen samun matsugunni agarin na jauro.Anan Allah ya kawota garin kano inda ta hadu da malam ahmadu a kasuwar ta kwari yaje siyayyar kayan sallar matar shi da yaransa,tym din yaga fulani kyakykyawar yarinya yar shekara 19yrs tana yawo kamar mahaukaciya,Daga nan malam ahamadu ya tambayeta lbarin ta,tana kuka ta fada masa,Aikuwa ya taho da ita anguwarsu ya bawaa abokinsa Malam kaila lbri,take ya bashi shawarar ya aureta kawai domin kuwa shine best solution,inba haka kamar yar aiki zata koma acikin gidan nashi,take ya gamsu da shawarar abokin nasa,bayan an fito daga sallar Azahar aka daura auren sa da fatimatul zarah(fulani)tare da Angonta Ahmadu.
Sai daga nan ya tina yadda fulani zataji wannan lbri dare da matar sa lamee.Da daddare kuwa Limamin anguwar suka rakashi gida domin yiwa matar sa bayani sanin sha'anin mata,bayan bayanin da liman yayi mata ba karamin tashin hankali lamee ta shiga ba,daga bayane malam ahmadu ya je ya taho da amaryarshi daga gidam aminin nashi bayan sun mata bayani auren da aka daura musu,tayi kuka sannan ta fawwala Allah komai domin wannan ma karamin rufin asirin ta bane,akan tana yawo acikin gari,Dakinsa ya kaita a mazaunin dakinta,wanda ya kasance dama daki uku ne a gidan,daya na samarin daya kuma na lamee saina ukun kuma na lamee.
Haka fulani ta fara rayuwa a wannan gida cikin tsangwama da kyara a wajan lamee,har so take malam ya dawo gida domin ta samu sukuni,duk wani aiki itace take yinsa inhar fice,idan ya dawo ne ma toh,lamee najin shakkarsa baza tasaa ta komai,yaran lamee kuwa,suma tasa sun rena ta domin baban danta kabiru sa'an fulani ne,Dan haka shiyasa yafi rainata,sai bello,,Yusuf da kuma lamratu .Bello da Yusuf sune wadandaa suka fi nutsuwa a yayan na lamee,domin kuwa su tausayin fulani suke ji,sune suka saka mata fulani sanadiyar mahaifiyar su ta ce bamai cewa da yar da ta haifa anti,Dan haka sabida Alkunya suke ce mata fulani.Bayan shekara daya ne da zuwan fulani,tym din lamratu tana da shekara 10,itama tsaurin ido ba wanda bata ita shi ,ahaka ma Yusuf da Bello  suna taka mata birki idan tana yiwa fulani,kabiru kuwa ba ruwanshi,waishi yana jin haushi an aurowa mamanshi sa'arshi.
A shekarar ne Allah ya bawa fulani juna biyu harna wata uku,wanda ta fara rashin lfy sosai,daga nan ne malam ahmadu ta dauketa a wata yar karamar motarsa daya siya suka tafi asibiti,aunawar farko sukace tana da juna biyu,sannan tana bukatar jinni domin kuwa bata da shi,farin ciki awajan ahmadu ba ya misaltu ba,daga nan ne ya kira kabiru yace ya siyo mashi maltina ya kawo masa domin yasa kafin a dauka jininsa a karawa fulaninsa,bayan kabiru ya kawo mashine ya umarce sa da yaje ya kawo abinci daga gida kafin a sallamesu in an jima su tafi bayan karin jinin,key din motar shi kabirun ya tambayeshi don ba laifi yanxu kabirun ya iya motar,dakar malam Ahmadin ya bashi dan bai cika son yana jan motar a ko da yaushe ba,Bayan tafiyarsa a cira junin aka fara karawa fulani wanda tuni bacci ya dauketa
Can gida kuma dawowar su harun daga makaranta bada jimawa ba,kabiru ya zo karbar abincin fulani,daga nan ne suka ji lbarin rashin lfyar ta ta,ga kuma iya babanne a awajanta,Dan haka suka ga dacewar su dubota.
Lamee kuwa tun da taga fulani ba lfy ta fara sake 2 aranta,domin inda abin da zaifi bakanta mata shine ace fulani nada ciki,ga kuma taga dukannin alamu sun nuna,Dan haka tuni shedan ya runjayeta ta zuba mata maganin subar da ciki acikin abincin da kabiru zai kai mata asibiti,tym din Yusuf lekowar shi kitchen yaga abin da take sauri take zuba,tuni ya yi sauri ya koma da baya domin kada ta ganshi,nan hawaye suka wanke masa fuska yana mamakin bakin kishin irin na mahaifiyar tasu.
Aikuwa nan take ya zo ya samu kabiru yace masa an basu assignment a biology zai bishi ya siyo cardboard domin yin drawing,sannan yaje wajan Bello ya ce masa shima ya fadawa maman tasu haka domin su dubo fulani inba haka taji ba  baza ta yarda ba.fita Bello  yayi ya tafi wajan maman tasu,domin fada mata,labewa wa Yusuf yayi domin yaji reply din maman tasu,sannan yana kiyastawa aranshi cewa,in sha Allah sai yayi yarda yayi fulani bata ci abincin da mahaifiyar su taci ba,bayan Bello yaje bata da batun fitar tasune ta yi shiro sannan ta kwallawa Yusuf kira,atake ya fito daga dakinsu yana addu'ar ta barsu,tambayarshi tayi shin abinda Bello y fada da gaske ne?Na'am yace mata,daga nan ta kira kabiru ta meka masa abincin,su Yusuf suka bi bayan shi domin tafiya,har sunje bakin kofa ta kira Yusuf ya jiyo tace masa,yusufa ku siyo abun da wurifa ku dawo tare da dan uwanku,Murmushi Bello yayi tace mata tare zamu dawo ummanmu,lamratu da ta fito daga wanka tace ,yaya Bello Allah ya kiyaye,Ameen ya amsa ,sannan Yusuf yace uwar yan rashin kunya adai rage,dariya tayi sannan suka fice suka shiga mota kabiru yaja suka tafi.
Can asibiti kuwa malam ahmadu ya zaune gaban fulani wadda take yin bacci ta har yanxu,fanin shirun yayi yawa ne yasa ya fito da wayarsa daga aljihunsa yayi kiran number kabirun domin ya kawo abincin kafin ta tashi daga baccin.
Bangaren su kabiru kuwa driving yake,bayann yaga sun yi nisa ne shine yake tambayar su wajan da zai sauke su,sosa Kai Yusuf yayi yace,yaya kawai mu wuce asibitin Dama mun dade bamu zaga garin ba,in yaso ko akofar asibitin nasarawa ne ma tsallaka mu saya,shiru yayi yana jinsu sannan ya wuce.
Sunzo shan kwanar asibitin ne wata babbar mota tazo ta bige motar da kabirun ke driving,take suka fara salati.buguwa tayi a jikin wani bangare na asibitin,take jama'a suka taru domin ceto rayukansu,da kar driver babbar motar ya tsayar da ita ya fito hankali tashe yayi wajan motar su kabirun wanda already an fito daa Bello da ko numfashi baya yi,ga raunika ajikinsa da yawa dashi da Yusuf,kabiru ma hakan ta kansance dashi shima duk kafafuwanshi ciwo ne,da sauri aka dauke su aka shigar dasu asibitin.
Bangaran malam Ahmadu kuwa fitowa yayi harabar asibitin yana kara gwada number kabiru,ringing ta fara,gefensa ya kalla yaga ana shigowa da wasu ,ganin jinin dake wajan yasa ya kawar da idauwansa daga wajan,suka take suka shigar da Yusuf da Bello ciki.
Ana kokarin shigar da kabiru ne sukaji wayar jikin shi tana kara,kwantar dashi duka yi awajan suna lalubar aljihunsa domin fito da wayar tashi,jin karar ringtone ya karade wajan again yasa malam Ahmadu kara kallon wajan da wayar shi a kunne yana jiran kabiru yayi picking,kallon wajan da yayi ne yaga irin kayan da kabiru ya saka yau,ga kuma mutum a kwance kamar marar rai ana dauko waya a aljihun wandonsa.
Nan take gaban malam Ahmadu ya fadi,gaba yayi ganin wannan bawan Allah,kara sawarshi kenan aka dago da kabiru don karasawa dashi ciki,Take Malam Ahmadu yaa fara salati yana cewa,Dana ne ,wlh dana ne,shi nake kira ma yanxu,yana nuna wayar hannunsa.
Wasu daga cikin lokitocinne suka zaunar dashi suna bashi baki,Dakyar ya dawo haitacinsa.
Nan daya daga cikin likitocin ya fito,da sauri malam Ahmadu ya tashi ya isa wajansa.
Kallon sauran ma'aikatan yayi yace,kunemo yan uwan wadan nan yaran,kallon shi malam Ahmadu yayi yace nine ubansu,sun suyar da kai doctor yayi sannan yace ya biyo shi office dinshi.
Isowar su office dinne,doctor ya umarci shi daya zauna,nan take ya zauna,doctor ya fara bashi hakuri da kuma daukan kaddara mai kyau da marar kyau.
Malam Ahmadu abin da na keso dakai shine kayi hakuri,daya daga cikin yaran ya rasu,Da sauri malam Ahmadu ya tashi tsaye idanuwansa suka yi jazir yayi hanyar fitowa.
Biyo bayanshi doctor yayi,yaga ya shiga dakin da aka kai su kabiru,bin bayansa yayi suka shiga dakin tare.
Shigowar shi yayi daidai da farkawar Yusuf dauke da salati a bakinsa,Kallon gawar da aka rufe da farin kyalke yayi ,isa wajan yayi ya yaye.take ya zube a kasa ganin bello kwance kamar mai bacci,karasowa doctor yayi yana kokarin tasar dashi wanda take ya jike sharkaf da gumi.
Jin kiran Baba da akeyi shiya dauke hankalinsu wajan kallon Yusuf,da sassarfa ya isa wajansa,kama hannunsa Yusuf yayi yace,Baba Bello ya rasu ko?nima binshi zanyi,amma kafin nan ka kira min umma Dan Allah,kuka malam Ahmadu ya fashe dashi yana kara rike hannun dan nasa.
Take ya kira lamee yace ta taho asibiti ba lafiya.
Shiru tayi tace wani abunne ya samu fulani?Aa malam Ahmadu yace mata,kashe wayar tayi ganin kamar gurin fulanin yake so ta xo sanadiyar xubewar cikin nata.
Kara kira yayi tace lamee kixo nace ko!ceewa ta iya ita sai ta daura sanwar daree baza ta iya zaman jinya ba.
Murmyshin dole Yusuf yayi ya mekowa baban nasa hannunsa domin ya bashi wayar,meka masa wayar yayi.
Dakar maganar take fitowa yace,Umma ki yafe min duk abunda na yi miki wanda ban sani ba,sannan Kada ki kara kokarin cutarwa da .........Nan tari ya turnikeshi ya fara kakarin amai ,Daga nan ne ya fara jerowa salati yayi shiru daya kai karShe.
Malam Ahmadu ne ya matso kusa ya taba shi yaji baya numfashi,salati ya fara,Nan gaban lamee yaa fadi domin kuwa duk abun da ake bata kashe wayarba,doctor ne ya tabbar daya rasu shima din ya rufe masa fuska,sannan ya jawo malam Ahmadu yana biga bayansa domin kuwa rasa yara biyu a kokaci daya bakaramar jarrabawa ce.
Fitowa sukayi harabar asibitin don shirye shiryen kai gawarwakinsu gida .
Bangaren fulani kuwa ganin Ahmadu baya dakin lokacin data tashi yasa tayo waje domin duba shi,dan ba laifi ta samu karfi ajikinta.
Kicibis suka yi dashi cikin wani irin hali,take taji banta ya fadi,ta riko hannunsa tana tambayarshi meya faru?jijjiga mata kai ya farayi yana wasu zafafan hawaye.
Ihun kukan lamee ne ya ankarar dasu suka juya suna kallonta.
Wajansu ta taho da sauri tana ina yusufana yake,fito da gawar su aka fara yi daga dakin,Nan take ta fadi ta suma.Hankalin fulani ne ya kara tashi tace,Baban lamratu wai meke faruwa ne?sukuyar dakai yayi yace,ZARA'U bello da Yusuf sun riga mu gidan gasskiya sanadiyar accident.
Nan take fulani ta fadi itama.

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now