He's sick🥲

261 20 11
                                    

Tun bayan afkuwar abun,tunda ya koma gida ko part din momy bai leka ba,daki ya shiga ya rufe kansa aciki,sallah ce kawai ke tada shi daga kwance da yake.
Wannan karanma kiran sallar magaribar da aka kirane ya tasar dashi ya shiga toilet ta gabatar da alwala ya fito ya tada sallah.
Sosai yayi mitsatstsiyar sallar da ake bukata.
Bayan idar warsa carbi ya dauko ya ci gaba istigfarin daya kasance yake yi aranar tun bayan afukuwar incident din.
Sosai abun ya dame shi fin komai a duniya.
Awanni guda ya tsabga wata muguwar rama,kamar wanda yayi shekara yana jinya.
Kwankwasa kofar da ake yi ne karo na babu a kirga ya dawo dashi daga xurfin tunanin daya keyi.
Kallon kofar yayi ya sakar mata wani mugun kallo.
A yanayin daya ke ciki gani yakai idan har sukayi ido hudu da momy to ba karamin baci ranta zaiyi.
Gajiya akai da buga kofar aka kyaleta.
Tashi yayi daga zaunen daya ke ya isa kan lafiyayan gadonsa,dakyar ya iya karasawa sabida yunwa da kuma damuwa dake yawo dashi .
Kwanciya yayi ya rike kansa dake sara masa.
Take wasu zafafan tears suke fitowa daga idanuwansa.
Tun bayan faruwan abun bai samu yayi ishashshan kukan daya ke bukata.
Kukan ne ya fara xuwa masa mai yawa yanxu.
Take kuwa ya fashe da wani wahalallan kuka,sosai yake kukan kamar wani karamin yaro.
Tafi 30mint yanayi.
Karar wayar data cika dakin ce ta dawo dashi daga kukan daya ke .
Kallon wayar dake gefensa yayi yaga sunan layla na yawo akan screen din phone nashi ,dauke da pic dinta akai.
Take yaji wani bacin ran ya nunku fin nada.
Wani tsanar yarinyar ne yaji ya shigar masa ransa dukdaa yasan ba itace tamai wannan kullalliyar ba but ta sanadiyar ta ne hakan ya afku ta ketawa yarinya karama mutunci ta bata san hawaba bata san sauka ba.
Har wayar ta gama ringing bai dauka ba .
Saida ta kira saubiyar baiyi picking ba .
Tashi yayi ya shiga toilet ya sakarma kansa ruwa .
Saida ya dauki one hour sannan ya fito,idanuwansa snyi wani irin jaa sai kwayar idon ta zama kamar blue blue.
Shikansa daya kalli mirror saida yayi mamakin ganin halittarsa.
Kallon agogo yayi yaga 9:30
Daukan wayarsa yayi ya kira wata number .
Bayan anyi picking cikin tsadaddan English dinsa yace "guy ina zan same ka?ina so ka rakani airport ne na samu flight zuwa Nigeria exactly 10"
Daga daya bangaren akaima masa reply.
Katse kiran yayi sannan ya isa wardrobe ya bude ya dauko wallet dinsa ya rufe.
Komai yanayinsa ne cikin rashin kuzari fuska ba walwala.
Bude kofar dakin yayi ya fito,ya sauka parlourn da zai sada shi da waje.
Ya bude kofar zai fita yaji voice din mummy na cewa "where are going my boy?tun jiya nake buga kofa kaki budewa kuma na tabbata kana jina,ko wani abun layla tayi maka bansani ba?"
Jiyowa yayi ya watsa mata wani bansan kallon idanuwansa cike da kwalla,tsaki yayi ya bugo kofar palourn ya fice.
Isa bakin car dinsa yayi,ya bude ya shiga.
Gabansa ne yayi mugun faduwa jin kanshin turarenta daya cika motar tun jiya har yanxu kanshinta ya ki barin motar.
Kallon gefensa yayi,gani yake kamar idan ya juya zai sake ganinta agefensa kamar jiya.
Handbag din data bari yayi ido biyu da ita,samun kansa yayi da daukan handbag din ya fara xugewa,ajiyeta kawai yayi jikinsa na karkarwa ya kasa karasa xugewar.Bude safe din dake cikin motar yayi ya ajiye jakar aciki ya rufe wajan.
Tada motar yayi ya fice daga gidan hankali tashe.
Wani babban anguwa ya isa ya isa gaban gidan farkon layin daya shiga,parking yayi bai iya shiga cikin gidan ba.
Daukan wayarsa yayi yayi kiran friend dinsa,take yayi picking yace masa "I'm waiting for u outside d get "
Kashe wayar yayi sannan ya dafe kansa daya ke sara masa har yanxu.
Ji yayi ana kwankwasa glass din window shi.
Dago dakansa yayi ya kalli best friend din nasa.Unlocking motar yayi,shi kuma ya zagayo ta baya ya bude ya shiga ya rufe.
Kallon shi yayi yace "dude what happened,zaka bar gari haka babu wani shiri and without informing me "
Tada mota yayi kawai ya hau titi ya fara tafiya ba tare daya kalli friend din nashi ba "
Tabo shi yayi yace "dude I'm talking to u fah,why are u avoiding me?ko wani mummunan abu ya faru ne?
Jin yanayin questions din friend din nasa yasa gabansa yayi mugun faduwa ,wannan wani sirri ne ya bazai taba gigin fadawa wani ba,koda kuwa haifin daya haife shine,dan haka dole ya samawa fuskarsa nutsuwa kodan kada ana tunanin wani mummunan abune yayi causing hakan.
Juyowa yayi karo na farko ya kalli friend din nasa da idanuwanshi wasu kala dasu ya furta "nothing mukhtar "
Take hankalin mukhtar ya kara tashi domin kuwa rabon da dude ya kira shi da ainahin sunansa tun tym din da grandma dinsa tayi wani tashin lfy kamar zata rasu,toh wannan tym dinne da yaje dubata dude ya furta "in Dada ta rasu bansan yaya zanyi ba mukhtar "
That's d only tym dazai iya tunawa ya kira ainahin sunanshi tun fara kawancensu.
Kallon friend din nasa yayi yace "dude yanxu na kara tabbatar da cewa wani abun nadamunka,karka min karya ka fada min,yaushe rabon daka kirani da mukhtar ?to nan na kara tabbatarwa kana cikin damuwa "
Xuciyarshi ce ta fara bugawa da sauri da sauri,ya kalli mukhtar hankali tashe ya fara magana cikin daga murya "nace maka lfy na kalau mukhtar ko kana son nayi karyan........"
Take numfashinsa ya fara yin sama yana kokarin daukewa.
Hankalin mukhtar ba karamin tashi yayi ba,sauri yayi ya rike sitiyarin motar sannan yayi controlling nata ta tsaya.
Hankali tashi ya kalli friend din nasa,nan ya tabbatar cewa he's already unconscious.
Da sauri ya fito da ga motar ya zagayo mazaunin da yake ya ciccibeshi da sauri ya mayar dashi baya.
Dawowa yayi gaban motar sannan ya tada ta ya nufi wani asibitin dake anguwarsu a guje.
Isarsa ssibitin ya kira wani family doctor nasu dake duba yan gidan su ya sanar dashi halin da friend dinsa ke ciki.
Cikin gaggawa aka shigar dashi ciki,doctor ya fara duba shi don a bashi temakon gaggawa.
Duba number dad yayi awarshi da yayi saving dad din dude,take dad yayi picking,gaisawa sukayi da dad sannan mukhtar ya tambayeshi ya nageria .
Sanar dashi halin da ake ciki yayi cewa,friend din shi bashi da lfy.
Sosai hankalin daddy ya tashi,cewa yayi gobe sassafe zai iso saudiya sannan kads mukhtar yayi gigin fadawa Dada coz idan taji za'a iya kwantar da dukansu a asibitin.
Har awanni biyu suka wuce amma doctor akashh basu fito ba.
Hankalin mukhtar ya tashi sosai ganin haka,kin fadawa mamanshi da babanshi yayi ganin dare yayi yanxu ana kikarin 12am.
Wayarsa ce ta fara ringing,ganin abbanshi ne yasa kawai yayi picking.
Fada ya fara masa cewa bai dawo gida ba har yanxu.
Shiru mukhtar yayi sannan yace "Abba na tafi na raka dude airport ne,a hanya kuma kawai ya zama unconscious "
Hankali tashe abba yace "kamarya ya zama unconscious?dama bashi da lfy ne?ko kuwa wani abune ya hada ku "
Hankali tashe mukhtar yace "ko daya abba amma bansa ba ko dama baida lfy dinne but nidai nasan ko fada bazaisa dude ya zama unconscious ba saide ko rashin lfy ,tambayarshi kawai nayi abunda yake damunsa ganin yanayinsa ya sauya,daga wannan ya fara yimin fada "
Sauke ajiyan xuciya abba yayi yace "I'm coming right now "
Zama mukhtar yayi bayan gama wayar da sukayi da abbansa.
Ba'afi minti 10 ba saiga abba ya shigo cikin asibitin yazo ya sami mukhtar zaune ya zauna shima akusa dashi yace "har yanxu basu fito bane?"
"Haryanxuw basu fito ba abba,ni harna fara jin tsoro ma wlh " hawaye ne suka cicciko idanuwan mukhtar din.
Dafa shi abbansa yayi yace "be strong my boy in sha Allah babu wata matsala,ina zargin ciwon sa ne na shekara da shekaru ya tashi "
Zaro ido mukhtar yayi ya kalla abba yace "dama dude nada wani ciwo daban san yana dauke dashi ba abba?"
Kallon yaronsa nasa abba yayi yace "kwarai kuwa yana dauke da wani ciwo da tun yana yaro Allah ya hallicesa dashi yayi ta rashin lfy,har mahaifinsa ya fidda rai dashi,a hankali dai ana kaishi asibiti kala kala har saida yakai shekaru 10 sannan aka gano ciwon.babanshi yasha kashe makudan kudi akan wannan ciwon nasa,hakanne yasa ya karbo shi awajan kakarsa domin kula dashi sosai,har ta dalilin ciwonsa ne ma ya dawo nan saudiya da zama sabida doctor din da yake kula shi dashi sau daya yake xuwa Nigeria a wata ,dan haka wannan dalilin ne yasa harya kara aure a lokacin da baiyi niyyar hakan ba don kawai ya samu mai kula masa dansa idan ya tafi Nigeria kan harkar business dinsa ,sai da doctor ya dage da basa treatment har akayi masa aiki a  xuciyansa, sannan aka samu ya samu sauki amma da sharadin cewa,baza a na bata masa ransa ba da har abun zai kasance damuwa aransa. Inba haka ba kuma ciwon zaike tashi ne wanda hakan zai iya jawo ya rasa ransa idan har xuciyarsa ta buga "
Wani gumi mukhtar ya goge jin abunda abbansa yake fada masa yace "abba kana nufin cewa dude yana da ciwon xuciya ne?"
Sauke ajiyan xuciya abba yayi sannan ya furta "kwarai kuwa mukhtar larurar abokinka kenan,abunda yasa baka sani ba shine, mahaifinsa ya gargade shi akan kada ya taba fadawa kowa inba haka ba wani da niyyama zai masa abunda zai bashi hau shi dan yayi hurting feelings nasa,sabida ya kasance yaro mai jin magana wannan yasa baya taba fadar larursa ,kuma ba wanda yasan da wannan ciwon inbanda kamar shi dani kuma aminin mahaifinsa,hakan ne yasa bayayin kawaye inbanda kai da alhaji ya yaba da tarbiyyar da muka baka nida mahaifiyarka."
Sosai xuciyar mukhtar tayi sanyi ya kuma kara son abokin nashi da kuma sake tausaya masa jin larurar da yake da ita.
Jin abbansa yayi yana cewa "mukhtar bana so ka taba nuna masa cewa kasan lalurarsa sabida nima na fada maka ne sabida bana so wani abun fada ko hayaniya ya kuma shiga tsakaninku gudun irin wannan ta faru "
Jijjiga kai mukhtar yayi ya goge kwallar data fito masa yace "in sha Allah abba he will never know of it "
Dago da kansu sukayi suka ga doctor akash ya taho fuska dauke da damuwa .
Sun tsorata sosai da yanayinsa ,abba ne ya karasa wajansa yana tambayarshi yanayin jikin nasa
Shiru doctor yayi sannan ya kalla tym yaga har one tayi,umarta abba yayi daya biyo shi office dinsa.
Binsa yayi abaya,mukhtar tahowa shima yayi but abba ya masa alamu daya koma ya jira shi.
Shigarsu office din doctor yace " how comes aka bari yaron nan yasa damuwa aranshi har haka,at first na dauka hawan jini ne but saida na duba naga cewa yana dauke da ciwon xuciya for long wanda naga har aikin an masa,but me yasa yanxu akeso a bata aikin baya,ya kamata a magance masa abunda yasa shi wannan damuwar if not gaskiya da matsala "
Sauke ajiyar xuciya abba yayi hankali tashi ya furta "sorry doctor but bamu san abunda yake damunsa ba but in sha Allah very soon zamu magance matsalar,yanxu baban yaron baya nan "
Ringing wayar abba ta fara,yana dubawa yaga dad ne ke kiransa.
Picking yayi ya kara wayar a kunnansa.
Dad ne yace "how's my son doing abdullahie? Ciwonsa ne ko kuwa?"
Shiru abba yayi dan daga ji yasan hankalin abokinnasa a tashe yake.
"Da sauki friend karka wani damu kanka plss,inaji kobe kace zaka taho?"
"In sha Allah by 2 ina saudiya harna gama arranging komai,ka hadani da doctor yanxu "
Kallon doctor abba yayi sannan ya tura bashi wayar ya amsa "
Tambayarshi yayi jikin dansa.
Doctor akashh ne ya furta masa cewa "da sauki yanxu haka bacci ma yake yi "
Hankalin dad ba wani kwanciya yayi ba dan baiji abba ya bashi cikakkiyar amsar daya ke ambaya ba inbanda sharar da zancen dayayi ma.dukda haka but babu yarda ya iya sukayi sallama ahakan .
Tambayarshi yayi ko zai iya ganin dangidan aminin nashi,amsa masa yayi da to but ko ya shiga ba zaiyi magana ba sabida saida suka sha wahala kafin ya dawo hayyacinsa kuma numfashinsa ya daidai ta suka masa allurori suka samu bacci ya dauke shi.
Sosai abba ya tausaya masa.
Doctor akashh ne yayi masa jagora suka tafi dakin daya ke,shigarsu suka tarar da mukhtar a gabansa yana share kwalla.
Isa wajan abba yayi,ya na Kallonsa kwance abun tausayi,lokaci daya harya canza kamaninsa yayi wata muguwar rama.
Dafa mukhtar abba yayi sannan yayi masa alamu  da su fita kada su tashe shi. Fita sukayi abba ya bama mukhtar baki,dskyar yayi shiru.Kallon tym din wayarsa yayi,yaga 2har ta wuce.
Kallon mukhtar yayi yace masa,"kai ka kwana ana ni kuma zan wuce gida yanxu zan fadawa mamanka abinda ake ciki gobe sai mu daawo sassafe tare da ita.
Tafiya abba yayi ,doctor akashh ya nunawa mukhtar dakin dazai kwana in yaso da asuba saiya koma f
Dakin da dude dinsa yake sabida ya samu ishashshan bacci kafin y farka.
Tafiya yayi ya kwanta ,baccinma kun xuwa yayi babu abunda yake tunani inbanda larurar abokin nasa sabida wannan babban matsala ce coz baza'ace wai a matsayinka na dan adam baza ka samu jarrabawa.
Tashi yayi yake ta nafilfilinsa yana nemawa abokin nasa sauki awajan ubangiji.
Har aka kura asuba bai rintsa ba.
Bayan ya idar da sallah asuba ne ya fito ya nufi dakin abkinnasa.
Isarsa dakin kwance yake kamar jiya,numfashinsa na fita slowly face dinsa ya dan fada but hasken fatarshi ya sake bayyana sosai.
Tsura masa idanuwa mukhtar yayi yana kallinsa,shi kansa baisan tym din daya saki smile ba,ganin irin kyan abokinnasa.
Zama yayi a gujerar gaban gadon ya dauke kansa daga kallan daya ke masa ya ci gaba da lazimi.
Kiran abba ne ya shigo wayar tasa,picking yayi suka gaisa.
Abba ne ya tambaeshi jikin abokin nasa,amsawa yayi da "da sauki abba but har yanxu bai farkaba " daga daya bangaran ne abba ya amsa masa da "muma muna nan kan hanya jira nake mamanka ta gama abuncin mu taho "
Da "to" mukhtar ya amsa sannan sukayi sallama.

Su abba basu shigo asibitinba sai 7:30,shigowa dakin dasu mukhtar sukayi dauke da kulolin abinci ahannunsu,tashi mukhtar yayi ya tare su.
Karban abincin yayi daya bayan daya ya ajiye su. Isa bakin gadon mama tayi ta tsura masa ido tana masa addu'a tana tofa masa,dan sosai take son yaran,tun tasowarsa da mukhtar ta yaba da hankalinsa sosai.
Dan ko su da suke larabawa amma sosai yafi yayan yan uwanta hankali da nutsuwa shiyasa ta kara yaba abotar danta mukhtar dashi.
Goge hawaye daya xubo mata tayi,dan itama akwai saurin hawaye,dan ita mukhtar ya dauko.
Fita abba yayi dan ya kira doctor akashh ganin har 7:30 bai karasa office dinsa ya ganshi yana shirin fitowa dauke da kayan aikinsa.
Murmushi ya sakarwa abba sannan suka gaisa,suka karasa dakin yana tambayarshi ko ya tashi daga baccin daya ke "Aa "abba yace masa sannan suka bude kofa suka isa dakin.
Zuwansu har tym din mama da mukhtar na zaune a gabansa.
Doctor akashh ne ya isa gabansa sannan ya fara yan gwaje gwajensa.
Sauke ajiyan xuciya yayi sannan ya kalli abba yace "komai ya koma yadda ake bukata saboda ishashshan baccin daya samu,rashin tashinsa yanxu yana da nasaba da daidaitawar da xuciyar sa takeyi,and pls maje sure an magance masa matsalarsa idan ya farka if not tunani da damuwar daya ke idan harya ci gaba zai iya samun matsala fin wadda ya ssmu yanxu "
Sosai suke jin bayanin doctor harya gama sukayi masa godiya ya fita domin duba sauran patient din.

Bayan awa guda ne hannunsa ya fara motsi,mukhtar ne ya lura da hakan,da hanzari ya isa wajansa ya zauna gefensa ya kama hannunsa.
Jin hannun mutum a nasa hannun yasa ya damke hannun mukhtar sosai yana motsi da bakinsa,ba'ajin abunda yake fada but da alamu mags yake furtawa.
Kunnansa mukhtar yakai bakinsa yaji kamar yana furta "plss I'm sorry,forgive me pls,it wasn't my fault,it's a set up "
Haka yake ta furtawa.
Sosai mukhtar ya tsorata jin abunda dude dinsa yake furtawa,nan ya sake tabbatarwa da tabbas damuwa ce ke damun abokin nasa.
Hankali abba da mama ne ya dawo kansu,tasowa sukai abba yana cewa "ya farka ne "
Jijjiga kai kawai mukhtar ya samu dayi.
Abba ne ya matso kusa yace "son are u awake?open ur ayes plss we are here for u"
Jin maganganu akansa yasa ya fara budewa idanuwansa da suka canza kala,kwayar idonsa ta kara blue blue,wanda hakan nada nasaba da ciwonsa,inhar abu na damunsa to kwayar idanuwansa za su kasance haka.
Fess ya sauke idanuwan akan abba.
Murmushi abba ya sakar masa sannan ya furta "sorry son,how are feeling now "
Cikin muryar marasa lfy ya furta "Alhamdulillah abba "
Mama ce ta matso kusa tana masa sannu.
Kallon mukhtar yayi ya sakar mashi wani sihir taccen Murmushi cikin cola ya yace "buddy u are not at fault fah naga kaki kulani kana shirin yiimin kuka "
Harar wasa mukhtar ya sakar masa yace "naga kana shirin barina ba dole nayi kuka ba "
Dariya abba da mama sukayi cikin jin dadyn yadda suka ga yadan ware dukda abba ya gane cewa kawai dauriya yakeyi sabida yasan dauriyarsa sosai tun yana karami.
"Dude daure kaci abinci plss kafin kasha magunguna nka plss "
Kallonsa yayi yadan yamutse fuska sannan ya furta "ina ka rakani toilet nayi sallah before that "
Matsowa mukhtar yayi ya kamasa,sannan suka isa toilet yana dingisawa dan gaba daya babu karfi ajikinsa.
Alwala yayi sannan mukhtar ya sske temaka masa suka dawo ya shimfida masa sallaya ya tada sallar asuban da ake binsa.
Mama ce ta hada masa tea sannan ta xuba masa chips and egg din data taho masa dashi dan tasan favorite dinsa ne su.
Mukhtar ne ya karfa ya zauna yana jiransa ya idar ya bashi.
Bayan ya idar mukhtar ya temaka masa ya dawo kan gadon.
Dauko abincin yayi ya fara bashi tea din,ganin idanuwan abba akansa yasa ya fara kurbar tea din yana runtse ido.
Rabi yadansha sannan ya ce ya koshi.
Chips din mukhtar yakai masa bakinsa,kawar da fuska yayi alamu baya so.
Mama ce ta matso kusa dashi ta dafa kansa cikin lallashi tace "haba babana daure kaci koda kadanne,favorite dinka ne fa,ko baka son ka warke da wuri?"
Shiru yayi yana sauranta badan yaso ba yayiwa mukhtar alamun daya bashi.
Saka masa chips din yayi a bakinsa ya fara taunawa dakyar ya iya hadiyewa.
Ruwa ya bukata a bashi,take mama ta isa ta dauko ya bawa mukhtar ya bashi .
Tarine ya taho masa,take ya fara tarin yana mai rike kirginsa idanuwansa sukayi wata kala dan tsabar wahalar dake dawainiya dashi.
Take wani a mai ya taho masa,sai kawai jini ya fara fitowa maimakon abinci.
Shikansa hankalinsa ya tashi ganin jini ya xubo ta bakinsa,nan ya tabbar da ciwonsa ne ya tashi ashe tunda.
Hankali tashi mama ta fara salati tana shafa kansa,fita abba yayi da hanzari domin kiran doctor akashh.
Budewarsa kofar sukayi kicibis da daddy tare da doctor akashh.
Hankali tashe abba ya kalli akashh yace,ur attention in needed doctor "
Kallon direction din da abba daddy ya kalla yayi.
Ganin kwallin dannasa cikin wani irin hali yasa ya isa wajansa hankali tashe yana furta "son me ya sameka,I'm right here ka fadamin matsalanka na magance maka plss "
Hugging din dannasa daddy yayi yana shafa kansa,daka gansu kasan akwai kyakykyawar sha kuwa hadi da soyayya tsakanin su.

Dangyatin ❤️❤️❤️❤️

The luv saga is about to start i think 😊😊😊😊

Just continue following me u will find what d story contains 😎

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now