The gift(muhammad mukhtar)

307 15 1
                                    

Shigowar ta dakin ta samu inna shafa zaune akusa da kanwartata,sallama ta yi,Jin voice nata yasa lamee kara hade fuska,inna shaface ta amsa mata cike da walwala dauke akan fuskarta dan tana mutukar ganin nutsuwar fulani da kuma tausayinta dan tasan ba karamin hakuri take yar uwar tata ba.Durkusawa tayi ta gaida su hawaye na kwaranya a idanuwanta,inna shafa ce ta amsa kawai,dago fuska tayi ta kalli saitin lamee tace maman ramlatu ya karin hakurinmu?...banza lamee tayi mata inbanda kallon tsana da take mata,ganin baza ta amsa ba yasa ta kalli gefen inna shafa wadda ta karbe gaisuwar ta amsa da Alhamdulillah Zara'u,kasan xuciyar fulani kuwa fal yake da rashin jin dadin kin amsawar da lamee tayi domin kuwa ta dauka wannan rasuwarr zai zama sanadiyar dena wani abun nata but saita ga akasin haka.
Shiru tayi na wasu mintina sannan ta mike ganin wasu na kokarin shigowa yiwa su lameen gaisuwa,ramlatu ta rako su,kara Kallon lamee tayi tace mamn ramlatu kabiru yace na gaida ku,jin ta ambaci kabir yasa ta kalleta,don ko ba komai tana son jin lfyar danta da kuma halin daya ke ciki,amma bakin hali bazai barta ta tambaya ba.
Inna shafa ce ta cafe tace,muna amsawa zara'u ,ya kuma jikin nasaa?amsawa tayi da da sauki,yanxu ma yana iya zama ayi. Zance  dashi.
Alhamdulillah inna shafa tace,sannan fulani ta kama hanyar fitowa,inda ramlatu ta watsa mata harara tace,mayya kawai.
Saida kowa na dakin ya kalli fulani,suna kuma mamakin furucin ramla.ficewa tayi jiki ba karfi ta tafi dakinta tana matsee kwalla.
Inna shafa ce ta yiwa ramlatun tatasss har saida tasa ta kuka,lamee kuwa ko fimmmm bata tofa ba.
Kwanciya fulani tayi tana mamakin Hali irin lamee.
Da daddare ne malam Ahmadu ya shigo gidan y shiga ban garen fulani,samunta yayi tana kwance amma dai ba bacci take ba,zama yayi a kusa da ita yasa ta ta juyo dan ganin wane.
Ganin mijinta yasa ta saki sassanyan Murmushi,y jiki yayi mata sannan itama kuma ta kara masa gaisuwa tana hawaye,hakuri ya bata yana me lallashinta.
Fitowa yayi daga dakin don isa dakin sa,kiran lamee yayi awaya yace mata tazo suje su dubo jikin kabiru ganin dare yayi babu masu xuwa gaisuwa yanxu.
Hijab ta dauko,ramlatu ta biyo bayanta tana rokonta domin taje,Baban ne ya ce su tafi,ai kuwa suka tafi gaba ki daya,bayan sun isa bakin asibitin ne suka tsaya suka saya masa fruits don tafi ya masa dashi.
A harabar asibiti suka tarar da doctor,shiya musu jagora har ya xuwa dakin da aka kwantar da kabiru.shigarsu a zaune yake jin gine da pillow da aka kara masa a bayan shi,da sauri lamee ta isa wajan shi ta kamo hannunsa kwalla na zubo mata,dago da fuska yayi ya kalle su yana mai baiyana farin cikinsa,y jiki suka masa sannan ya kara tambayar jikin su yusufa,Malam Ahmadu ne yace,da sauki jikin yan uwan naka,sun ce ama sannu,kallon baban yayi yace a hada su awaya,ce masa yayi dukaa an musu allurar bacci saide ko wani lokacin,Ahaka de aka shashantar masa da zancen.
Ganin dare nayi yasa suka masa sallama suka taho gida.
Iso warsu gida kuwa tym din fulani na toilet tana kakarin aman da ya taso ta daga baccin data samu ya dauketa.
Jin kakarin amai yasa malam Ahmadu ya gane cewa itace,ta hanzari ya bita toilet din dan ganin halin da take ciki,Ganin da take ciki.
Wani kulluntun bacin rai ne ta tsayewa lamee ta shige daki tana gogen hawayen daya ke bin fuskarta.
Dago fulani yayi ya wanke mata bakinta kafin nan suka fito ya kaita side dinshi,y koma dakinta ya dauko magungunan da aka bata yazo ya balla y taimaka mata tasha kafin nan ta samu bacci.
Washe gari kuwa Alhamdulillah ta dan samu karfin jikinta ba kamar jiya ba.
Haka aka cigaba da karbar gaisuwa har akayi 7 .
Ranar da akayi bakwai ne,ranar wanda ya bige su yusufa suka bukaci magana da malam Ahmadu domin kuwa har bawai tare akayi dasu,yaune suke da muhimmiyar magana dashi.
Bayan sun gaisa suna kara jajantawa juna rashin da aka yi,daga nan ne Alhaji Alto ya fara maganar da take tafe dashi,  Malam Ahmadu kasan cewae tsautsayun daya afku ,duba da halin kwarai irin naka da kuma hakuri har ka dauki komai cikin sauki,kuma mukaddari,ina so zan baka wata kyauta,wannan kyauta ina fata baza ka dauketaa amatsayin biyan bashin abunda ya afku ba,Aa saide kawai na kwatanta jin dadin da nayi,Da Allah y hada ni da kai.
Dan haka malamm Ahmadu na baka kyautar miliyan 5 da kuma gida dake nasarawa GRA kyauta ka koma da kai da iyalanka.Sanan kabiru zan dauki nauyinsa har Allah y bashi lfy,sauran yaran suma zan komar dasu school din dana gina ta waccan shekaran ana koya musu da sauran dalibai.
Rasa bakin magana malam Ahmadu yayi sanin kudi da kuma kyan hali irin Alhaji Alto wanda duk fadin kano kalilanne basu san shi ba,kai idan ma baka sanshi ba to kasan wata kadara tashi.
Dago da kansa Malam Ahmadu yayi yace,bawai musu zanma.......
Kafin y karasa Alhaji Alto ya dakatar dashi yace,bana son jin wata wata magana daga bakinka malam Ahmadu inba kuma so kake ka nuna min ban isa da kaibane.
Ba haka malam Ahmadu yaso ba,Amma haka ya kura ya mika godiyarsa suka yi sallama ya raka su har bakin mota.
Ba'a jima ba kuwa Alhaji Alto yamai transfer din 5mil.
Amininsa yayiwa zancen wannan Alheri da aka masa,sa masa Albarka malam kaila yayi sannan suka yi shawarwarin abun ya dace yayi da wannan kudin,ciki kuwa harda 1mil din dazai bawa lamee ita kuma fulani 500k wanda bazai bata a hannunta ba kasancewarta yarinya saide zaike juya mata su harta mallaki hankalinta sosai.sai malam kaila da ya bawa 200k.
Bangaren kabiru kuwa jiki Alhamdulillah saide har ya gaji da hanya hanyar da ake masa na hada shi da yan uwansa.
Ayaune Malam Ahmadu ya yi taurin ran sanar dashi ta sigar lallashi da bata hakuri.
Inda kabiru yaci kuka har ya godewa Allah,dakar aka bashi baki ya koma kokan xuci.
Lamee kuwa ba karamin farin ciki tayi da wannan kudi da malam Ahmadu y bata ba,inda kuma ya kara sanar mata da gidan daza su koma nan da wasu lokutan amma dai bai yanke rana ba.
Ramlatu kuwa ta koma sabuwar makarantar ta,wadda kullum school bus ce take kaita ta kuma dawo da ita,tsaurin ido kuwa babu abinda ta fasa inbanda ci gabama da yiyi.
Fulani kuwa harta saba dukda tana jin ciwon abun,wanda da malam Ahmadu ya sani da tuni yayi tufkar hanci.
Haka rayuwa ta ci gaba inda cokin lamee har ya Kai wata 5 wanda ba karamin kyau ya kara mata ba gashi ya fito das dashi ,lamee kuwa babu wata hanya daba ta sake bi amma da yake zakaran da Allah ya nufa da yayi cara dole sai yayi,haka ta hakura ta xubawa sarautar Allah ido duk da bawai ta hakura bane don har yau tana ganin fulani da laifin cewa itace silar rasuwar yayan ta samari har biyu.
Malam Ahmadu kuwa Alhamdulillah business din daya fara a kasuwa yayi Albarka sosai ,hanyoyin arxiki sai sake budewa suke .
Kabiru ma Alhamdulillah jiki yayi sauki dan yanxu ya fara takawa sosai,amma idan ta fiya mai nisa ce to fa saiya dan to kara da sanda,a wannan dawowar da yayi gida ne bayan an sallama shi daga asibiti,mahaifiyarshi lamee ta sake cusa matsaa tsanar fulani da abunda daza ta haifa inda ta sake baiyana mishi cewa itace silar mutuwar kannansa da kuma dingisawar da yakeyi da sanda.a haka harta rinjayi zuciyar shi ta dasa masa kin ta da abunda daza ta haifa.inda lamee ta ke juya kudin da malam Ahmadu ya bata,wanda Alhamdulillah tana samu sosai.Dan kayan da take sarowa da wuri suke karewa.yanxu ma haka so take kabiru y karasa warkewa ta bude masa shigo kusa da babanshi yana zama.dan bata son ya koma wani karatu tunda ga hanyar samu nan.
Ana haka ne kwatsam lamee ta samu juna biyu wanda ba tayi aune ba har ya Kai wata uku,ba karamin farin ciki tayi da wanna ciki ba ,tunda ta riga ta fitar da rai da sake haihuwa,ko banza dai zata ajiye kwanta a gidan ba iya fulani ba.
Tym din cikin fulani nada wata 8 ,wanda ba karamin girma yayi ba Dan har tunani take kan cewa ko yan buyu zata haifa,sabida maman ta taba basu lbri ita da da yayarta cewa ta tabayin barin yan biyu,kafin ta haifi yayarta hajjo.a wancan lokacin tayi  ta tsalle da murnar cewa zata  iya haifan yan biyu nan gaba idan tayi aure ,inda ita kuma hajjo tayi ta addu'ar Allah kar bata yan biyu dan ganin cewa wahalar raino za suyi.
Share hawaye fulani tayi tuna shirmen yarin tartasu da yar uwata kwalli daya data rage mata wadda bataa san inda take ba har yau.
Shigowar malam Ahmadu ne ya dawo da ita da ga tunani da take,wanda dawowar su kenan daga asibiti shida lamee zuwa gwajin jini dan haihuwar ta ja mata yanxu,shiysa tazo mata ralular karin jini.
Kallonta face dinta yayi ya gane cewa kuka tayi.
Tambayarta yayi dalilin kukan nata tace masa,yayarta hajjo ta tuna,hakuri y bata sannan ya bata assurance din sake komawa kyauyen nasu da zarar ta haihu ta xubda wanka,anan ko sayi dacen ko ta koma sannan su sake gaisawa da yan uwan da suka rage.
Ba karamin dadi fulani taji ba,wanda harta kasa boye farin cikin nata.godiya ta masa sannan ta tashi ta kawo masa abinci suka fara ci suna hira duk dan ya kara debe mata kewar data ke ciki.
Haka rayuwa ta ci gaba inda fulani ta shiga watan haihuwarta,cikin lamee kuma nada wata 4cif cif.
A ranar juma'a ne fulani ta tashi da nakuda ,wanda tun dare take abu daya har gari ya fara haske sannan Malam Ahmadu y jiyo nishinta sabida a dakin lamee yake.
Da hanzari ya iso dakin ya sameta,duba ga halin da take ciki yasa yayi hanzari ya dauko mota suka nufi asibiti,
Lmee najin duk abunda yake wakana amma bakin ciki ya hanata fitowa.
Ban garan su fulani kuwa,isarsu keda wiya haihuwa tazo ganga ganga ta haifo danta namiji kyakykyawan gaske kuma kato,wanda su kanxu Malaman asibitin sun taba da baiwar kyawun jaririn,komai na jikin shi irin na mahaifinshi fuskarce y dauko ta fulani wanda ya kara kere fulani kyau duk kyau irin nata.
Malam Ahmadu yayi farin ciki sosai da wannan kyauta da Allah y bashi.tun a asibitin yayi masa huduba da Muhammadu(mukhtar)wanda ya yiwa kansa takwara kenan .Duba da cikakkiyar lafiyar da suke dashi yasa aka sallamosu.bai zarce ko ina ba sai sabon gidansu na GRA wanda yayi kansa Alkawari ranar da fulani ta haihu to ranar zasu tare a wannan sabon gidan nasu.
Tayi farin ciki sosai kodan kasan cewar kowa part dinsa daban wani baizai kalli wani bama saide shi yayi niyar da ya xutarci dan uwansa.ka komai gidan ya hada tun daga kayan sawa har ta xuwa kayan daki dana baby mukhtar dinta.godiya ta masa harda sauran kwallarta.
Ficewa yayi domin sanar da lamee da yara su shira sumaa zuwa dare su tare.
Bayan fitar tane ta kura nurse amira ta sanar mata haihuwar tata.
Bada jimawa ba kuwa tazo suka sha hirar su tana santin gidan nasu,bata bar gidan ba sai 9 mijin dazata aura yazo daukan ta.
Ban garen lamee kuwa ba karamin kona mataa rai malam Ahmadu yayi ba,wato sabida da farin cikin an haifa masa da namiji shine ya Kai shi daukin tarewa a sabon gida ba tare daya basu notice ba.haka ta daure ta ki ta nuna bacin ranta duba da xurfin tunani irin na maza kar ya gano cewa bakin cikin haihuwar dansaa da aka haifa take .Dan haka ta shanye duk wani bacin rai suka yi parking suka koma sabon gidan a daren.
Hankalin lamee bai sake tashi ba saida taji lbrin cewa sunansa malam Ahmadu ya mayar da kuma kyau irin na wannan jariri,dakyar ta tofa masa fatiha shima ganin malam Ahmadu a dakin ne.

Vote and comment plss 👏🏼👏🏼
♥️♥️Dangyatin ♥️♥️♥️

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now