Grieve

405 17 2
                                    

Take malam Ahmadu ya kara diriricewa ,shigar dasu ciki akayi Ana kokarin ceto rayukansu,hali da cikin da fulani take dauke dashi ga kuma rashin lfy da fargabar abinda ya faru shiyayi sanadiyar bata farfado da wuri,lamee kuwa ba'a fi mintina da daura mta ruwa ba ta bude idanuwanta tana salati tana ihun kuka,kallon dakin ta farayi ta hango shi zaune yana hawaye agaban fulani,yana jimamin kaddarar data fado musu,harara lamee ta watsa mashi dan ganin bama wajanta malam yazo ba,wannan wanda irin masiface ga rasuwar Yusuf ga bata san halinda sauran yayan suke ciki ba.
Jin kukan farkawar da lamee tayi shi ya ankarar dashi cewa ta farka,da sauri ya taso ya iso wajanta ya kamo hannhunta yana mata sannu,sanin rasuwa akai mata shi kadai ne zai sa baza ta sauke masa kwandon bala'i ba yanxu,hayewa ta goge ta na kokarin cire ruwan da aka daura mata,rike hannu ta malam Ahmadu yayi sanin ba iya cirewar tayi ba,kuka ta fashe dashi tace,cika ni malam naje naga Yusufa na,yanxu fa yake min magana kuma acemin ya rasu!rufe mata baki malam yayi yana jijjiga mata kai gudun kar tayi sabo,yana mai sake tausaya mata rasuwa har biyu da aka mata sannan ahakan ma daya take da masaniya akai.
Likita ne ya shigo ya iso wajansu ya cire mata drip din da aka daura mata,kallon malam Ahmadu yayi yace malam sai hakuri,ya kamata ku tafi gida yanxu a sallacesu sauran biyun kuma ka barsu za'a kula dasu yarda ya kamata kafin su dawo hayyacinsu (kabiru da fulani)tashi tsaye lamee tayi tafko rigar doctor da yake kokarin fita tace,har mutum nawa kake nufin suka rasu?kuka ta fara tana bige bige,duk kukanta ya karade asibitin riketa malam yayi yana kokarin lallashinta yana kukan shima,dan yasan saita fishi jin zafin sosai ta take mahaifiyar su balle har su biyu,hakuri yake bata yana cewa Bello ne ya fara rasuwa sannan Yusufa ,kabiru kuma yana nan da ranshi,hakuri zamuyi lamee haka a
Allah y aiko mana,sannan ki godewa Allah Ranar juma'a suka rasu in sha Allah suna cikin rahamar Allah.
Lameee kuwa me take in banda kuka ,Dakar suka fita suka hau motar asibitin suka taho gida,gawarwakin kuma suna bayan mota.tun a hanya malam ya kira abokin nasa ya fada masa,take shima ya fara kiran jama'a da yan anguwa yana gaya musu rasuwar,tini jama'a suka jijji lbri,masu kuka nayi masu sanyin jiki nayi,domin kuwa kowa yasan yaran da hankali da tarbiyya.
Tuni jama'a suka fara cika gidan,sai ramla gani tayi mata suna shush shigowa suna zama ana ta gumi,tambaya ta fara yi me ya faru?shiru kowa yayi mata yana tsoran sanar da ita,aikuwa saita fice ta samu aminin baban nasu take tambayarshi,shiru yayi yana share hawaye yace,kiyi hakuri ramlatu yayyin kine sukayi accident,Yusuf da Bello suka rasu shima kuma kabiru an kwantar dashi,ihu ramlatu ta farayi tana faduwa kasa tana bigima,malam kailan ne ya dago ta yana bata baki,motar su Malam Ahmadu ce ta doso anguwar tasu,take jama'a suke bin motar tun kafin a karaso kofar gidan,kowa kokarinsa yaga ya dauko gawarwakin.(Allah ubangiji kajikan iyayenmu 😭🙏🙏🙏da dukkan wadanda suka rasu,Allah kajikan Babana ka kai rahama kabrinsa 🙏Ameen Ameen,dan Allah duk wanda ya karanta,yayi masa addu'a plsss 😭😭🙏🙏)
Tuni aka sauko dasu a ka shiga cikin gidan dasou domin yi musu wanka,sannan aka ba bada umarni kowa ya tafi masallaci bayan sallar juma'a sai ayi jana'izar,Ahaka kowa ya tafi masallaci cikin mutuwar jiki.
Ramlatu kuwa rungume uwarta tayi sukai ta kukan tare sai dangin lamee ne sukai ta basu baki,lamee ce ta shiga wajan da ake wankan yayan nata taje ta bubbudesu kamar sayi magana sun wani kara kyau,ciwon da suka ji ajikinsu ba wani ciyo bane saide ba'asan cikin ba,kuka takeyi gwanin ban tausayi sai yanxu tasan cewa ashe garin kaiwa fulani abincin suka yi accident din,jin malam Ahmadu yana fadawa malam kaila,yace wlh malam abincin ma ko kaiwa basuyi yiba abakin asibitin abun ya faru.
Jin hakan yasa lamee ta kara fashewa da wani sabon kukan jin ko abincin ma fulani bataga idan saba balle ta ci cikin ya xube,wannan shine asara biyu ga burin kashe dan wani bai yiwu ba ga rasuwar yayan ta har guda biyu,wani bakin cikine ya kara ka ruwa fin na dazu,dama ance inzaka gina ramin mugunta ka gina shi daidai,Sanin cewa haka Allah ya rubuta tun kafin taxo duniya,to amma fa wannan ma wata ishara ce ga mai hankali.maganar da ake mata shiya dawo da ita taga tunanin da take,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta lura ashe har an gama suturtasu fuska ce kawai yayi sauran a rufe,addu'a aka umarcesu suyi musu,addu'a da tazo bakinta ta yi musu tana zubda kwalla,bayan ta gama ne malam Ahmadu da amininsa suma suka musu suka feshesu da turare sannan aka rufe musu face.
Jin alamun za'a shiga sallah an gama huduba yasa suka tashi suka tafi domin samun sallar.

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now