Zarah❤️❤️

254 13 10
                                    

Tun dawowar ta wannan sabuwar rayuwa,komai na duniya ya fita araanta,a koda yaushe idan ta zauna bata da tunani saina yaushe zata hadu dadynta,ammynta sannan kuma da tilon yar uwarta sarah.
Hawayen daya ke fitowa daga saman fuskarta take gogewa da tissue din dake hannunta,a yaune ta cika sati guda a wannan gida,gidan da ba wanda yasan da zamanta acikinsa inba mama ba.
Koda yaushe tana jiyo hayaniyar mutane daga daya daga cikin sashe na gidan,harma da shewa da dariya duka tana iya jiyowa
Saide ta saki Murmushi kunci idan ta jiyo shewar dariyarsu,saisu tuna mata da tata rayuwar ta baya mai cike da farin ciki da annashiwa amma acikin yan awanni kalilan wannan farin ciki ya gushe,gushe ta har abada awajanta ,dan gani take koda zata koma cikin iyayenta da yan uwanta,tofa tabon kunar daya saka mata bazai taba tafiya ba.
Yanxu ma haka zaine take cikin Atamfa,wanda ta sake haskata,kyanta ya kara fitowa kamar shuwa arab.
Sosai take kuka akan 3seater din da take zaune.
Wannan ya kasance sabo awajanta.
Don tunda ta fuskanci mama bata son kukan da take,saiya kasance batayi idan tana nan,saide ta bari har saita fita wajan aikin sannan saitayi sana'ar kukan nata.
Ganin ranakun take kamar basa sauri,ta damu sati biyun nan ya cika domin su koma wajan wannan bayin Allah da sukayi tozali dasu airport su taimaka mata su maida ta wajan mahaifanta.
Kiran azahar din da aka kira ne ya sayar da ita domin gaba tar da sallah.
Yanxu Alhamdulillah ta samu lfy ba mai cewa anyi mata fyade ko anci mutuncinta saide idan itace ta fada maka,sabida duk wani alamun da za'agane sun gushe dan ba karamin gyarata mama tayi ba bayan magingunan da aka bata a asibiti,itama tayi mata mata da gargajiya,Wanda tuni hakan yayi tasiri ta samu lfy da wuri.
Bayan ta idar da sallah ta tashi domin daura girki kafin mama ta dawo,dan adan sati dayan nan da sukai tare da ta koyi abubuwa da dama da taga mama tana yi,yanxu ta dan iya kalilan daga cikin girkin Nigeria,musanman ma na hausawanmu,dan inhar mama zatai abincin dare to tare sukeyi,hakan kumaa ba karamin debe mata kewa yake yiba.
Wilgawar fitarta ta gani ajikin mirror,hakan yasa ta kallie kasa aikwa hango maya fin data rufe mirror din tayie a kasa.
Hakan ne ya nuna mata cewa mayafin ne ya fado ba tare data saniba.
Tun zuwanta gidan ta rufe madubin dakin nata don kwata 2 bata da muradin kallon kanta yanxu,tasan kanta ada ma'abociyar kallon madubi ce,tana kallon kanta tana jin farin ciki da nishadi barinma idan tayi kwalliya. Dan ada duk kukan da tayi agida tofa in har ta kalli mirror saitayi smiling,dan akwai kauna tsakaninsu da mirror.
Hakan ne yasa wani lokacin ammynta take tsokanarta wai tana da aljanu.
Haka zata sha shagwabarta ta more.
Wani siririn hawaye ne ya sauko mata daga face dinta tunawa da hakan datayi,dan ba karya tayi kewar ammynta,infact duka yan gidansu.
Dan ji take kamar tayi sheru masu yawa bata gansu ba,dan banda boarding ba abunda dake rbata dasu,shima kuma boarding dinsu duk sati sai an musu visiting.
Komawa tayi domin mayar da kyallen daya fado don ko da gwaji bata son tayi tozali da fuskarta,dan gani take kamar ta koma wani abun daban duba da kaddarar data afkar mata.
Rufe idanuwanta tayi ta tsugunna ta dauko kyallen,idonta rufe ta mayar ta rufe mirror din.
Bude idanuwanta tayi don ganin ta rufe.
Aikwa ras gaban ta ya fadi ganin cikakkiyar fuskarta a mudibin,dan koda ta rufe kara zamewa yayi sabida bata lan kaya shi da kyauba.
Samun kanta dayi da kara Kallon mudubin.
Tabbas kamanninta yana nan dan har gani tayi ta kara wani haskan fa yau alamun zaman waje dayan da take ya karbeta,saide ba karya ta rame dukda dama ita din ba mai kiba bace,but ga wanda yasan ta yana kallonta yasan ta fada.
Waje biyu ne basu fada ba ajinkinta,wanda ammynta tasha fada mata cewa gadon kakarta
Tayi inji mama fiddausy ,wato mai sunanta dan har ta rasu kirjinta da hips dinta basu ragu ba sunanan cas kamar yarda suke saide ma karuwa da sukayi.
Haka zalika ya kasance da zarah itama na shanunta da hips dinta suna nan kamar da,don ba gixo mirror din yayi mata bama har karuwa taga sunyi.
Ganin kokarin shagaltar da ita da madubin yake son yine yasa tayi maza ta durkusa ta dauki kyallen ta rufe mirror din da kyau.
Da hanzari ta fita daga dakin ta nufi kitchen,dan wannan ne karon farko da wani abu shagaltar da ita dahar ta danji sanyi aranta kalilan.
Tunkunya ta dauko ta dauraye ta sannan xuba ruwa ta daura kan cooker gas din.
Rasa mai zata dafa musu tayi,can ta tuna cewa kwana uku da suka wuce mama tayi dan wake agabanta dan haka yau shi zata gwada dan ya mata dadi a cikin ireiren abincin yan Nigeria.
Da hanzari ta harhada duk wani abu da ake bukata tayi abunta cikin kwarewa,kamar ta saba da abun.
Cikin sa'a kuwa komai ta gama shi ana kiran sallar la'asar.
Bayan ta gyara komai yarda ya kamata ta wuce daki domin gabatar da sallah.
Bayan ta idar ta dade tana addu'ointa sannan ta dawo kitchen din dan taji taste din abinci nata,saka danwaken tayi abaki ta fara taunawa,samun kanta tayi da sakin wani sihirtaccen Murmushi jin taste din dan waken ya fito.
Sosai abun ya mata dadi,dan taga kokarinta.
Fitowa tayi ta koma daki ta dauki qur'ani ta fara bita,after like 30mint ta'aje qur'anin ta nufi Telaphone din gidan ta fara dailing number,jin number yaki shiga yasa idanuwanta suka ciko da kwalla,dan wannan number dinne hope dinta shima kuma dakyar ta tuna shi dan wani tsohon layin daddy ne da take kiranshi da a makaranta,yawan kiran da yake samu daga yan siyasar Nigeria yasa ya sauke layin,gashi kuma har yanxu bai maida shi ba.
Jiki sabule ta koma kan gado ta kwanta hawaye na fita daga fuskarta har bacci ya dauke ta.
❤️Bonus ❤️
   
Dangyatin ❤️❤️

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now