Solution

291 11 4
                                    

Idar sallar isharsa kenan yaji muryar dadynshi dauke da sallama abakinsa,murmushin dole ya kirkiro don kauce damuwa a face dinsa tun kafin daddy ya dago shi.
Amsa sallamar daddy l yayi dauke da smile ,alamun ba abunda ke damunsa.
Son har ka farka ashe,dazu munyi waya da mukhtar yake cemin ai ka koma bacci "
"Eh daddy na farka nayi sallah yanxu "
Daddy yaji yana cewa "dama kanwar ka Na rako ta duba ka dan duk ta gallabi kanta akan ciwonka,hankalinta yaki kwanciya "
Shi baima lura da mutum bayan daddy ba saida ya dago idanuwan shi yaga layla dauke da ledonjin fruit a hannunta ta sukuyar da kai,dago da fuskarta tayi tana kallonsa.
Annurun da ya ke fuskarsa taga gabaki daya ya gushe,take gabanta ya fadi.
Zama kusa daddy tayi tana Yaya ina yini(haka take kiran shi whenever she notices that,he's not in a good mood)
Tun da yayi tozali da fuskarta yaji duk wani bakin cikinsa ya dawo,ta dalilinta ya keta mutunci yarinyar da baisanta ba kuma baisan inda zai kuma ganinta ba balle ya nemi gafararta.
Muryaar daddy ce ta dawo dashi daga dogon tunanin daya tafi"son baka ji tana gaida kai bane?"
Sorry daddy ya iya furtawa kawai sannan yace "kai na ke ciwo ne daddy,banji da kyauba "
Sorry layla ta furta tana mai jifanshi da Kallon tausayi "
Thank u ya furta ba tare daya kara Kallon side din da take ba.
Kallon ledar fruit din daddy yayi yace "ga fruit nan inji layla, Murmushi dauke da fuskarsa yake fadawa Abee hakan, sukuyar da kai layla tayi sabida tayi avoiding mugun kallon da yake tun karota da shi.
Murmushi dole yayi,yana kallon gefen ya furta "thank u "yana ya mutse fuska.
Gyaran murya Dady yayi sannan ya furta "layla let's go kinga brother naki bai son hayaniya mai yawa a wannan stage "
Murmushi ta mayarwa daddy,tace "ba matsala daddy mu tafi tunda na duba shi "
Tashi tsaye daddy yayi ya isa wajan Abee yana shafa kansa yace "toh son na zamu tafi,Allah ya kara lfy,sannan mom dinka na gaida kai "
Kama hannun daddy yayi yace "Ameen ameen daddy,thank u and good nyt "
Hanyar fita daddy yayi,Layla biye a bayan shi ta furta "Allah ya kara lfy Yaya " tana fadan hakan tana sunkiyar da kai.
Ciki ciki ya amsa da ameen " shima sabida daddy ne kawai.
Fitarsu kuwa suka isa mota suka kama hanyar gida.
Shiru motar ta kasance sabida gaba ki daya xuciyar layla adagulee take da yanayin da ta kalli Abee,adama yaya bare yanxu da taga alamun tsana acikin kwayar idanuwansa,kenan hakan na nufin ta masa wani abun kenan!
Toh ita me ta masa? Sabida a iya sanin ta tasan babu abunda ta masa, gaskiya zata cire duk wani tsoro da fargaba domin ta tambayeshi abunda yake damun shi da kuma abunda ta mishi.
Muryar daddy ce ta dawo da ita daga tambayoyin da takewa zuciyarta.
Daughter kuwa lfy ki? Tun dazu da muka dubo Abee naga damuwarki ya kara karuwa maimakon naga canji,fada min mene matsalarki.
Murmushi layla tayi,idanuwanta cike da hawaye ta furta "ba komai daddy "
Share hawayen daya biyo fuskarta tayi.
Jiki sanyaye daddy ya furta kuka kuma layla?
Kokarin samawa kanta nutsuwa ta fara yi
Sannan ta furta "Daddy ina son y sami lfy da wuri ne "
Murmushi daddy yayi yace "toh ai ba kuka zakiyi ba addu'a za ki masa dukda nasan kinayi "
"Toh daddy na daina kukan "
Murmushin dole ta sakarwa daddy dan ganin damuwa karara a fuskarsa.
"Yauwa yar Albarka ko kefa "
Sosai daddy yaji dadin furucinta sannan deep inside him yana mai kara jin tausayin layla,ganin tsantsan son da ke dawainiya da ita kan tilon dan nasa,da da akwai hali daya umarci Abee ya aureta kodan son da yarinyar ke masa,saide kash bazai iya yin abunda zai ta kurawa tilon dan nasa ba,kodan sabida larurar dake damunsa,baison abunda zai takura masa harya jawo tashin ciwonsa.dan ko last maganar da daddy ya masa akan soyayyarsu da laylan saida ya shiga damuwa dukda ya sanarwa daddy shifa ba sonta yake ba.
But tabbas da yana da hali
da sai ya aurawa layla Abee.

Isowarsu gida kenan daddy yayi parking,itama ta bude kofa ta fito,tana mai kallon daddy ta furta "saida safe daddy "
Allah ya tashe mu lfy daughter "
Tafiya tayi direct ta wuce dakinta ,tana shiga ta datso shi,dan ko bukatar ganin momy batayi dan wani haushi take tunanin kara cusa mata.
Kwanciya tayi akan gado ta fashe da wani wahalallan kuka,wanda tun asabon gidan daddy ta ke kun she dashi.
Ita yanxu damuwanta ba komai illa fushin da tahango bestynta yana yi da ita,shin ina zata sa kanta da wannan wahalalliyar soyayya tasa,kullum abu sake baci yake maimakon cigaba.
Ita bata da wani wanda yasan matsalarta inba momy ba,momy ba kasafai take understanding nata ba,kawayenta kuwa sunsan lbr Besty but basusan matsalar dake tsakaninsu ba.
Tabbas dole ta samu mafita,inba haka ba kuwa,nan gaba ma daina kulata zaiyi.
Ire ire abubuwan da layla take ayyanawa aranta kenan ,furtawa tayi "to ya zanyi ni layla,Ya Allah ka kawo mun mafita "
Sake fashewa da wani kukan tayi,
Bugun kofar momy taji,
Ko kallan kofar layla bataiba dan a yanxu bata da kuzarin tafiya ma.
Gajiya momy tayi ta koma dakinta,dama kukan layla ta jiyo time din daza ta tafi part din daddy.
Sleeping dress ta saka sannan tayi tafiyar ta side din daddy,cike da mamakin abunda yasa layla kuka?

Kuka layla ta ci gaba dayi har kanta ya fara ciwo,daga haka bacci ya dauke ta.
Isar momy dakin daddy ta iske kwance da laptop a gabansa sannan yana making call da mukhtar.
Tunatar dashi yake akan cewa ya kara da tilon dan nasa.
Shiru momy tayi tana sauraran sa,harya gama.
Ba karamin haushin Abee takeyi ba akan mahimmanci da damuwar da daddy yake dashi.
Sannu da zuwa ta masa sannan ta zauna akan gadon.
Jikin Abee ta tambayarshi,yace da "sauki "
Sannan ta daura da cewa "wani abunne ya faru da layla ne ta rufe daki take kuka ko kuwa ita da Abee?
Kallon ta daddy yayi yace "Ai dama daughter bata daina kukan ba? Na tambayeta tun a mota tace min wai,ita so take ya warke da wuri,ashe kinga yarinyar nan bata hakura ba"
Wani bacin rai nee ya kama momy ganin cewa akan Abee layla Keyin wannan shirmen kukan.
Cikin kissa momy ta furta "dole ta damu kasan cewa da soyayya tsakanin yaran saide fata Allah ya hade kawunansu "
Da ameen daddy kawai ya furta sannan ya ci gaba da aikin da yake.
Kwanciya momy tayi tana faman sake sake aranta,jin daddy ya banzatar da zancen yasa ta kwanta.

Tun bayan barin daddy da layla gidan,bai tashi daga inda yake ba,tunanint matakin da zai dauka akan layla yake,dan dukda ba ita ce tasa masa abu yaci ba,toh ai dan sabida itane momy tasa masa,dan su cika wani mummunan burin su, sosai hankalinsa ya kara karkata da cewa,dasa hannun layla aka sa masaa abunda yaci,wanda besanma mene shiba,dan shi dai kawai yasan ya tsinci kansa be da kasa rike kansa sabida masifaffan feelings din daya kamashi.
Ganin yanayin layla yanxu,wannan shiya kara dasawa zuciyarsa cewa da saninta aka shirya masa wannan abun,sabida yanayin tsoro da yaga ya wadatu a fuskarta.maybe sabida hakanma ta kwanta rashin flyar karya dan plan dinsu ya tafi yarda suka so,tunda zaije dubata ,wanda yake tunanin duk acikin shirin su ne.Ire ire abubuwan daya dunga sakawa aransa ke nan,wanda daga karshe ya yarda da dukkan abunda zuciyarsa ta raya masa.
And he came up with a very good solution.
Dukda ba wani farin ciki abunda ya yanke zai sa masa but at least he came up with a very good solution kodan karuwar jama'a baki daya dashi kanshi.
,sannan bazai ma iya ci gaba da zama da mutanen da suka sashi cikin mummunan hali,wanda harya kai ya alakanta hakan da cewa tsana ce wannan ba so
bane ba.

Sannan nan gaba gani yake tsaf zasu iya sa masa wani abun still dan yayi raping layla,wanda yake tunanin hakan zaisa su samu chance din aurenta,And God forbid that,dan baya tunanin koda taba hannun layla ko a mafarki balle a reality,kai wannan tsaf za su iya sa masaa guba ya mutu.
Iren iren abunda yayi ta sakawa kenen aransa.

Ganin yazo da babban idea yasa ya saki wani Murmushi ,aljihun rigarsa ya fara lalubawa dan dauko wayarsa ,jin babu ita yasa ya tashi tsaye ya isa kan gado domin dubataa danshi rabon shi da ita ma tun lokacin daya fara rashin lfy.
Mukhtar ne ya shigo dakin dauke da sallama abakinsa ,jiyowa Abee yayi ya amsa da "W salam @
Dude ina ka ajiymun wayana?"

Sosai mukhtar yayi mamakin abokinnasa ganin a yan awanni guda ya fara canzawa,ko dai daddy ne yayi masa wani abun?
Murmushi mukhtar yayi yace, ma sha Allah yaron daddy,wato daddy ya sa mana kai farin ciki da alamu.
Kallon sa yayi yana smirking
Fita mukhtar yayi ya dauko masa wayarsa ya bashi.
Da hanzari ya amsa ya kunna,ganin yana da charge yasa ya fara danne danne,mukhtar na zaune yana kallonsa dan har cikin ransa yaji dadin ganinsa haka.
Ya dade yana danne danne,dan akalla yayi spending 45 minutes yan abu daya.
Dago kansa yayi yana mai sauke ajiyar xuciya,sannan ya furta "it's the best solution in sha Allah "
Hada ido sukayi da mukhtar dan tundaa ya fara danne dannen wayarsa bai fita ba .
Murmushi mukhtar yayi yace,dude ko dai new catch ka samu ne dan naga wannan Murmushin na yau daban yake.
Kallon gefe yayi sannan ya furta,Ba damuwanka bane.
Dariya mukhtar ya kwashe dashi yace,idan tayi tayi tsami naji.
Smirk yayi sannan ya tashi ya fita palour yabar mukhtar yana dariya .

Kece Rayuwata(my Jann❤️)Where stories live. Discover now