4

1.4K 25 0
                                    

💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

          _MASIFAFFIYAR KAUNA_

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&GNaturals_


✍🏾 M SHAKUR

EPISODE 4️⃣

_FREE PAGE_
Wuraren karfe uku wani mugun azababben ciwon ciki yatadata, da farko tazaci mafarki take amman sai taga ba mafarki bane, wani irin murda wa da cikinta da maranta sukeyi kaman ana murda hanjinta kanta na shegen sarawa, kokarin tashi tayi daga kwancen datake amman takasa sabida komi najikinta wani irin ciwo yake mata, ahankali tasaki wani wahalallan kuka mara sauti..... cikin bacci kaman daga sama Habib yaji sheshekan kuka tashi yayi yabude idanunshi, dayake yanada wata yar karaman tocula hakan yasa ya kunna ya haska Fatima dake kwance idanunta sun kumbura sunyi jajir sabida kukan datasha jiyada daddare gakuma bacci, karasawa yayi kan katifarta da sauri, murya chan kasa gudun kar Mama tajisu yace "Ya Faty menene kike kuka"? Yay maganan yana kai hannunshi saman goshinta wani irin zafi dayaji yasa da sauri yadauke hannunshi yace "innalillahi Ya Faty bakida lpy in tada Baba"? Girgizamai kai tayi, cikin muryanta da ba'aji sosai tace "dagani na zauna" hannunta datake mikamai yakama yadagata ta zauna da kyar tana share hawaye tana cizan baki, sosai yaji tabashi tausayi, yanason Ya Faty kaman ba gobe dan tamafi kulada su kan uwarda tahaifesu, tun suna yara itane komi nasu, duk in yanajin yunwa saidai in Ya  Faty batada kudi amman saita bashi yaje yasai wani abin, idan basuda lpy, Mama nafita kome sukeso saita dafa musu suna gamawa su wanke tukunya ta yanda Mama bazata saniba, ganin yanda hawaye yakasa dena zuba daga idanunta yasa yakoma kusada ita ya zauna kanshi ya daura kan hannunta yafashe da kuka ahankali gudun kar ajisu murya chan kasa yace "Ya Faty kiyakuri kinji Allah na sama yana kallo wata rana sai labari, Mama batada kirki kuma batason ki amman kinga duk ranan dana girma zan daukeki daga gidan nan nasai miki wani gida nasai miki mota nasa police nace musu karsu bari Mama ta shigo balle ta dakeki kota saki kuka, I promise idan na girma ko maganan banza babu wanda ya isa yafada miki kinji, kidena kuka, bari na girma kiga abinda zai faru kidena kuka" yay maganan yana share hawayen dake zubomata, danne kukan tayi takai hannunta ta sharemai hawayen shi shima tana murmushi tace "ninasan kanina soja ne, Habib dina, nasan idan Habib ya girma ko kallon banza babu wanda ya isa yamin, Habib dina sojana toko tubambale mayen abinci" dariya yahauyi kaman bashine ke kukaba, murmushi tamai tace "jeka koma baccin ka kaji" da sauri yace "kinji sauki"? Gyadamai kai tayi alamun eh, tashi yayi yawuce ya kwanta awajen shi yace "dazaran yacigaba ki kirani kinji" Tom ta amsashi ahankali, kwanciya yayi tareda kashe toculan, sai alokacin taji ashema hiranshi rahama ne agareta wani mahaukacin ciwone yakamata dayasa taji kaman zata kurma ihu amman ta daure tarasa inda zata saka kanta taji dadi, har aka kira asubahi idanunta biyu, har aka tashi tanaji Baba yabude kofa yafita yadawo amman takasa koda motsi.
**

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_

MASIFAFFIYAR KAUNAWhere stories live. Discover now