9

1.2K 27 1
                                    

💫 _DISASTROUS LOVE_💫


      _MASIFAFFIYAR SOYAYYA_

_THIS BOOK IS 500 IDAN KINASO PAY TO 3107021073 AISHA MUHAMMAD FIRST BANK, SAIKI TURO EVIDENCE OF PAYMENT TO MY WATSAPP NUMBER 07012181461_

        ✍🏾M SHAKUR

_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number 07010439656 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._


EPISODE 9️⃣

_FREE PAGE_

*****
Gidan nan babu wanda bai shigo yamata yajiki ba Maman Dady har wara takawo mata ma sabida ranan wara tayi ta karba cikeda kunya tamata godiya, Mama ma ba yabo ba fallasa tamata yajiki agaban Baba hakan yasa Baba yaji dadi, sanan yace taje ta kwanta adaki tahuta babu abinda zatayi yau shikuma Baba yawuce uwardaka wajen matarshi.

Da sallamaya shiga dakin zaune yaganta bakin gado tana fifita Abida datai bacci da mafici dan babu wuta tayi kyau sosai taci gayu tasa atamfarta mai kyau harda sarka awuya kaman wacce taje biki wanda abune dayasan bata sabayiba, zama yayi kusada ita tareda washe baki yace "wanan kwalliyan fa ni akamawa ne"? Wani banzan kallo ta jefeshi dashi sanan tace "kai asuwa, ni kaga dan Allah kabarni damuwan dake kaina daban Baban Habib" binta yayi da kallo yay shiru, dan yatsine fuska tayi saikuma ta nisa tace "uhm gwara ma nagaya maka, daga gidan Madam nake" yanda ya kalleta da sauri tareda sake natsuwa yasa ta gyadamai kai tace "gwarama kai salatin da kyau kaji, kirana tayi awaya tace nazo, nashirya naje nasameta tace min yaya ake ciki taji mijinta da mutanen nan namagana awaya ranan lahadi jibi kenan dan yau ai Jumma'a zasuzo, wai ya mun shirya mun gama hada kudin nace mata ko asi bakada shi balle chasi" wani gumi Baba yashare ahankali yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, wlh inda nasan haka abin nan zai kasance daban karba ba dukkece kika sani awanan ukuban" wani irin zaremai ido tayi tace "nice mene kace"? Kasa maimaita maganan yayi daya kalli kwayan idanunta saikuma ya saukar da murya ahankali yace "kiyakuri badake nakeba" kwafa tayi tace "Allah yasoka wlh dasaika raina kanka wlh mtswww" taja tsaki, ahankali yadafa kanshi saikuma ya buga tagumi saikuma ya kalleta cikeda damuwa yace "yaya zanyi yanzu Ruka kifadamin abinyi"? Shiru tayi tana kallonshi saikuma ta nisa tace "Mijin Madam yariga ya sanarda mu duk wasu ka'idoji da sharuddai na wanan lamarin ko kaje still maganardai itace zai sake maimaita maka, amman dudda haka yanzu katashi kaje kai wanka ka chanza kayan nan kasa wanan giznar danasa kasaya, ka feshe kanka da turare katafi chan sakateria office dinshi kasame shi kaje kuyi magana mai kyau, yafada maka idan dawata hanya dazakabi kome yagaya maka kadawo kasanar dani daga A zuwa Z sabida nasan yanda zamu bulloma lamarin daganan in lokacin Jumma'a yayi saika wuce kadawo gida karka biya ko'ina kadai jini ko" gyadamata kai yayi ta tashi tace "bari naje naduba ruwan dake murhu inyay sanyi kayi wanka da ruwan sanyi dan gaskiya sabida kai bazan hura wuta naci gayun nanba" tawuce tafita yabita da kallo yaji zafin yanda take gasamai magana amman yakasa cemata kala, kayan yacire yasa jallabiya yabi bayanta takaimai ruwan tadawo daki.

Fitowa yayi yadawo daki ya shirya tsaf yay mugun kyau kaganshi zaka dauka wani alhajine harda fesamai turare sanan tace "saura ka kalli wata mace" dan dariya yayi yaja hancinta yace "inada mace har mace irinki mezanyi da wata Ruka Baban Habib sai Maman Habib" murmushi tayi cikeda sonshi tace "nidai wuce katafi" tai maganan tana bashi key machine dinshi ta tasashi agaba har waje dudda yaso yama Fatima sallama dan taga yanda yake  kallon dakin but bata bashi damaba haka yaja machine yatafi, murmushi tace "kwanaki kadan yarage kurabu" tawuce takoma daki,  hijabi ta dauka tasaka sanan tafito ta shiga dakinsu Fatima, akwance ta ganta tana bacci, da kafa tasa  ta hambareta da sauri ta farka harara ta balla mata tace "tashi kifita falo kizauna kimin gadin Abida tana bacci nikuma zan fita, in yarana sun dawo daga boko ki basu abincin dana dafa yana kula" gyadamata kai tayi ahankali Mama taja tsaki tawuce tafice daga gidan.

MASIFAFFIYAR KAUNAWhere stories live. Discover now