12

963 32 0
                                    

💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

          _MASIFAFFIYAR KAUNA_


✍🏾M SHAKUR

EPISODE 1️⃣2️⃣
_FREE PAGE_

Sauran yaranne sukahau dariya though not all dan wasuma sunyi shiru sun natsu daga gani suna kewan iyayensu, shikuma yaron wani hararan shi yayi yafaracin abincishi kawai, takai kusan 20min ahaka, sanan ta tashi tagoge fuskarta tas da idanunta tass, ahankali taduka tadau jakan budewa tayi tadauki takeaway ta tabude ahankali tashiga turama kanta abincin sanan ta ijiye acikin jaka duk suna zaune wajen su kadai sai hayaniya yaran suke har wajajen karfe uku sanan securities suka shigo sukace "kutashi kuyi layi masu son amfani da bayi suyi, ga bayi nan anbude muku night journey zakuyi so get ready, prepare use 10min to do everything" bayika hudu dake dankareren hall din suka bude musu, ahankali ta tashi ta goya jakanta tai hanyar bayin wasuma nabinta abaya, shiga daya daga cikin bayinka tayi tarufe harda key sanan ta tsaya ta kalli kanta really fa batada banbanci da namiji da sauri ta dauke idanunta daga madubi dan bataso tana kallon kanta, fitsari tayi kaman tasani ta soke wani pad a aljihun wando dudda bata wani heavy flow dan gobenema zata gama amman saida ta dauka wanan dataji night journey zasuyi yasa ta chanza ta gyara kanta tareda flushing old one din ta shirya tsaf sanan tafito goyeda jakanta, tana fitowa security yanunata yace "kai kagama?" Gyadamai kai yayi hakan yasa security yanuna mai kofa yace "jemota ajeraku" fita yayi ahankali ya sauka kasa tareda wasu yaran, wani babban luxurious bus tagani kaman irin nasu landstar wanan hadadden bala'i kaman ma sabo, security dake tsaye gaban mota yace "oya zoka shiga" karasawa tayi ahankali ta taka tahau motan wani sanyi ne taji motar ga dankareren tv a kunne ga sanyi ga labulaye, security dake tsaye a tsakiyan motarne yana nunama kowa inda zai zauna yanuna mata sit yace "jeka zauna achan" karasawa tayi ahankali ta zauna kusada window, wani yaro aka turo yazauna kusa da ita dan sit bibbiyune jere akowani side, kafin agama jerasu tass karfe hudu, sanan taga wanan babban lawyer dayasa mata bracelet yana magana da security dukansu su biyar yabasu kudi wrapper yan dubu guda biyu har kasa suka duka sunamai godiya suna Allah iso dasu lafiya gobe da alamu su flight zasubi sanan dukansu biyardin suka shigo motan, daya ya zauna mazaunin direba, daya adayan bangaren mataimakin direba, sai uku suka zauna a first row na bayan direba dabasu saka any of the children akaiba, sanan suka tada motar suna dagama Barrister hannu harsuka fita daga hotel din suka dauki hanyar barin kano motar yay tsit sai securities din dake hira abinsu.

Ahankali ta lumshe ido azuciyanta tace "ina zaki Fatima Zarah? Wani kasa ko gari za'a kaiki? Nazaci anan kano zanyi aikatau amman wanan damuke barin garin kano ina zamu? Yau nice nake rayuwa amatsayin namiji ina amsa sunan Khalid, yau nine nake wani wuri da babu halitta daya dana sani, nine bana tareda mahaifina ko kannaina, nine nake barin garin danake zuea wani wuri daban ma saniba, Ya Allah kaga zuciyata Alkhairi nake nufima mahaifina Ya Allah na fawwala maka al amarina da rayuwata gabaki daya Ya Allah ka kareni ka tsareni, I am so scared, har kasan zuciyana inaji dabanyi wanan abinba amman kuma har kasan zuciyana inaji zan iya mutuwa aka kullemin Baba" hawaye ta share ta kalli gefe tadan bude labulen window ta kadan tana kallon hanya, itadai tunda take da wayonta bata taba tafiya tabar kano ba amman wanan tafiyan da ake motarsu na famfala uban gudu tasan
Kano zasu bari,  idanunta biyu harsuka fita daga kano suka kai zaria suka isa kaduna harsuka  dauki hanyar Abuja lokacin dare yasoma yi, ganin tafarajin yunwa yasa tabude jakanta tasauki abincin taci takoshi tasha ruwa sanan ta ijiye ta gyara zama tadan saci kallon yaran dake gefenta taga shi yamayi bacci, hakan yasa ta zubama TV dake aiki a motar ido tana kallon film din da akeyi nafada, ahaka wuraren goma nadare bacci yay awon gaba da ita.


********
Wajajen takwas nasafe tafarka ahankali take bude idanunta saitaga kaman all that happen jiya amafarki ne Baba yay biyan bashi da ita xataje aikatau, tarr tabude idanun nata tana kara kallon inda take ganin tana cikin motar har lokacin yasa taga ba dream bane, ganin har lokacin suna cikin mota ana gudu yasa tafara mamakin ina zasu kafafunta taji sun mata tsami sosai cikin kambas din da suke ganin yanda taketa motsi da kafar tana yatsine fuska yasa yaron kusada ita yace "kacire takalmin kafafunka susha iska inba hakaba zasu fara maka ciwo" kallon yaron tayi yananan shima kaman ita baida jiki sosai shima kuma dan farine, dauke kai tayi tashiga cire kambas din yaron na kallonta fararen kafafunta taciro dasukadan kumbura yaron yace "jibi kafarka mai kyau kaman kafar mace"! Faduwa gabanta yayi da sauri ta maida kafar cikin takalmi, dariya yaron yayi yace "kunya kakeji akira kafarka irin na mace to kafarne ba kaushi gashi batada wani girma daga gani baka aiki agida daman gaka shagwababbe sai kiran Baba kake cikin dare dakana bacci" da sauri ta kallai, dariya yayi yace "sunana Anas Abdulmalik kaifa" ahankali batare data kalleshi ba tace "Khalid" murmushi Anas yayi yace "aiman kai dan fulanine ko dan wlh kanada kyau inda kai mace ce da anga rububi gurin maza" wani irin mugun harara tamai tace "kadenamin irin maganganun nan banso" da sauri Anas yace "kai wlh kacika masifa me awanan maganan, by the way naji kasan ina muke yanzu?" Girgiza maikai yayi tace "kaika sani"? Girgizamai kai shima yayi yace "bansani ba wlh ni bantaba zuwa nan arayuwata ba amman kuma kaman garin yarbawa muke sabida naga signboard dinsu anata rubutun yarbawa akai" shiru tayi saikuma ta kalli window tai shiru, ajiyan zuciya Anas yasauke yace "irin wajen nan yakamata mutun yasami aboki dan we are all on our own, zaka zama abokina Khalid" yanda yay maganan ahankali yasa tajuyo ta kallai shima ita yake kallo, dan murmushi yayi yace "tunda baka sona da aboki shikenan amman still zan bada labarin dake cimin zuciya, kasan menene wlh na tsani Abba na sosai, bansan ina zaniba kawai yazo yacemin nahada kayana ya kalli Maman mu yacemata zai turani biyan bashi, saida mukazo wajen nagane ashe kudin dayaci kwanakin baya yakaro aure duk kudin bashine saikace yabani anini aciki dazai kama yadauken yabiya bashin dani, aikin shekara biyu da rabi fa zanyi ni bana makaranta ni inachan wata duniyan ina aikatau Mama na kewana" duka maganganun nan dasuke ahankali suke babu mai jinsu, ganin yanda hawaye yataru a idanunshi sosai yasa yabata tausayi ahankali tace "kayakuri wata rana sai labari, duk abinda d'a zaima iyayenshi koda cutanshi sukayi bai fadiba watarana zaka gane hakan kayakuri kaji" ahankali ya goge fuskarshi da bayan hannu sanan yamata murmushi ya kalli window ganin signboard na WELCOME TO LAGOS yasa da sauri yamata pointing da hannu yace "Khalid kalla" da sauri Fatima tajuya zata kalla amman sun wuce bata ganiba tace "menene" da sauri yace "naga welcome to lagos muna Lagos" dasauri tace "Lagos, Lagos din dana sabaji ana kira" gyadamata kai yayi ajiyan zuciya ta sauke, Anas nata mata hira hakan yasa tadan saki jikinta dashi kadan, saikuma daga baya sukai shiru ganin sun shiga asalin cikin garin lagos ga titina manya dake daukan kusan motoci kusan biyar a jere, ga dogayen buildings, ga hayaniga, ga yellow danfo buses, sukahau wani titi dake kan ruwa, ga jiragen ruwa manya manya irin wanda take gani a films su titanic akan ruwa, ga boat na gudu, sunyi kusan 20min sunabin bridge din chan ta hango wani babban UBA bank building tacema Anas "kalli UBA bank, banki su Baba yanada account awajen har number account dinshi nasani" dariya Anas yayi, garin yazamema yaran abin kallo securities duk suna jinsu sai murmushi kawai suke, sanan suka shigo wani hadaden kayataccen anguwa dake dauke dawani dankareren babban gida dagawani dankareren statue din mutum akofar gidan tsaye rikeda sandar girma, gaban gidan anyi wasu rubutu manya an rubuta ILE OTUN OBA LAGOS (GIDAN WAZIRIN SARKIN LAGOS).

_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._

MASIFAFFIYAR KAUNAWhere stories live. Discover now