2

1.7K 38 1
                                    

💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

           _MASIFAFFIYAR KAUNA_


✍🏾M SHAKUR

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_

EPISODE 2️⃣
_FREE PAGE_
Ganin yanda ya maida ita kaman  TV yana kallo yasa tacigaba tace "Inda kaga kayan dana saya dabakai korafi ba Baban Habib Mom Afreen Pre-order collection na shiga fa, nabiya kankanin kudi tayomana order gangariyan kaya tundaga kasan waje, wallahi bantaba ganin irin design din tukwanen da flask din dana sayaba har yanzu, wasu irin designs ne nadaban dan kayan danama Abida order babu irinsu agarin nan sai agidan masu kudi, ko masu kudin ma sai daidaiku, babu abinda zancema Maman Afreen sai Allah ya sakamata da alkhairi, gashi order kaya awajenta babu tsada, farashinta nada mugun rahusa kaga kaya kaman baka akayi kyauta, jira nakema wasu kudin su shigomana mukara yo order kaya daga kasan waje daga wajenta inyaso saimu bude shago ko Rabinraina mudinga saidawa" tunda tafara maganan kallonta kawai yake cikeda takaici matarnan tasashi amatsala Babba amman kuma ko ajikinta, ita batasan rigiman dasuke cikiba sai surutun banza takemai, abinda ke kara cimai rai yanda bai iya mata fada kaman an kullemai baki. Ganin yanda yake kallonta bayako kyaftawa idanunshi sun cikada hawaye sosai yasa sai jikinta yay mugun sanyi, ahankali tadaura kanta kan kirjinshi tana shafa kan nonon shi da hannunta tace "kayakuri Baban Habibu kaji, komi lokacine zaizo ya wuce kaman ba'a yiba, kudi zaizo In sha Allahu kaji zamu biya bashin nan kanka farau, ai ba'a kanka aka faraci ba, nidai kawai na hanaka karka sake kaje kana dako salon yan gidan nan sugano mekakeyi sudinga min gori, karka damu zan maka tunanin abu kaji" gyadamata kai kawai yayi sanan yadan tureta yatashi ya zauna yana mika hannu yana daukan jallabiya shi dake gefen gadon yasaka sanan yasauka daga kan gadon, dogone fari fat kana ganinshi kasan duka yaran falon nan dashi sukai kama, Maman cema baka, binshi da kallo tayi dudda taji haushin yanda baimata abinda takesoba amman saita share tace "muje naraka bayin daganan naduba yarinyar nan naga girkin" baice mata komiba Hijabi tadaura kan daurin kirjin dake jikinta suka fito tare, matan gidan na tsakar gida tana fitowa tawani dagakai kaman bata gansu ba tabi bayanshi da sauri dan yamata nisa kanshi akasa bai masan ko akwai mata a tsakar gidan ba danshi baya kallon matan wasu yay hanyar bayi itakuma kawai sai tai kitchen koda ta shiga gani tayi Abida ma tayi bacci itakuma Fatima na fifita wutan wutan daya kama dan har sanwan ma natafasa bama tasan an shigo kitchen dinba sai fama takeda wutan idanunta sunyi jajir sabida hayaki, balla mata harara tayi tace "inkin gama ki fifita wutan kije ki kwantar da ita adaki" kai kawai ta gyadama Maman nasu dan batason tace wani abu takara kwafta mata zagi, juyawa tayi zata tafi saikuma kawai tai tsaki tazo ta bayanta tace "bani y'ata" takai hannunta zuwa saman kirjinta zata kwance zanin runtse idanunta tayi amugun firgice hakan yasa Mama ta tsaya tana kallonta da mugun ban haushi saikuma ta dakamata tsawa tace "dalla kwantomin y'ata kina rurrufe idanu kaman mai surkulle" har wani ajiyan zuciya ta sauke tace "uhn to" sanan ta kwance Mama ta karbeta suka fita itakuma tacigaba da girkin.

_MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP, SHAHARAREN GROUP NE DASUKA KWARE KAN HARKAN ORDER, IMPORTATION DIN KAYA DAGA KASASHE DABAN DABAN NA DUNIYA AKAN KUDI DAN CINGILI, INDAI A MOM AFREEN PRE-ORDER GROUP NE KARKAI FARGABAN YIN ORDER DA ITA DAN AIKINTA NE, TA KWARE A BANGAREN TANA HARKA DA AGENT DABAN DABAN DAGA KASASHE DABAN DABAN, ZAKU IYA TUNTUBARTA AWANAN NUMBER 08069493528, DAZARAN KUNYI SAVING ZAKU GANTA A WATSAPP KUMATA MAGANA, KARKU BARI WANAN GARABASAR TA WUCEKU_

Wuraren 3 tagama girkin tadauki tukunyar a wata tray tafito tai dakinsu dashi Babansu tasamu zaune kan kujera yana rikeda remote Mama zaune gefenshi da alamu abincin duk suke jira tana ganin Babanta tasake sakin murmushi da kana ganinta kasan daga zuciyanta yake, harara Mama ta watsa mata tace "Malama ajiye tukunyar ki kwaso kwano na zubama Baban ki" da sauri Baba ya watsa mata mugun kallo yace "bazaki bar yarinya ta hutaba" ya kalli Habib daya shigo yayi kini kini da rai sabida yunwa yace "wuce ka kwaso kwanuka azuba abinci" da sauri Mama tace "wai sai insa abu kanuna agaban yara ban isaba" ahankali Baba ta hanyar rage murya yace "tagaji ne tahuta, tanada kannai intai girki sai asaka kannan suyi wani abu ko" Mama zata kara magana ya kalli Fatima datake tsaye inda take kanta akasa sai zufa take yace "Zahra'un Baba ya jarabawan andubo"? Da sauri tadagamai kai tana murmushi tana kallonshi kana ganin yanda take kasan yarinyar na mugun son mahaifinta, shima murmushi ya sakin mata cikeda sonta yace "dauko takardan nagani" da sauri tai uwar dakin su Mama tabi bayanta da harara daidai lokacin Habib yakawo plates karba tayi ta zuzzuba musu abinci tazuba na Fatima kadan ta ijiye agefe har Baba zaiyi magana saikuma yayi shiru kawai baice mata komiba, yadau nashi yasa cokali ya shiga ci murmushi kawai yayi shi kanshi yana alfahari da Fatima wajen girki danko Ruka bazata nunama yar karaman yarinyar nan yanda ake girki ba. Fitowa tayi daga dakin hakan yasa tun kafin ma takaraso ya ijiye abincin shi agefe yamika mata hannu tasamai takardan wajen kafanshi yanuna mata yace "zauna ga abincin chan dauko kici" kallon abincin tayi saikuma ta kalli na kannenta ba tace komiba Allah ma ya taimaketa batada wani cin hauka data mutu da yunwa, daukowa tayi tazo ta zauna kusada mahaifinta shikuma yana duba takardan murmushi kawai yayi ya gyadakai yace "uhmm Masha Allah wanda baida Fatima baida mene....."  dan murmushi tayi murya chan kasa mai shegen zaki tace "sa'a" bata fada da karfi ba sabida mamansu, murmushi Baban yasakeyi ya kalli Maman su yace "yarmu tacinye waec tass" sanan ya kalli Habib dake kallon takardan yanacin abincin yace "kagani haka nakeso kaima kadinga kokari a makaranta kaine namijin gidan nan, babanmu amman kullum na bayan kashi kake, abu daya kawai ka iya shine son abinci" daure fuska tamau yayi baice komiba Baba yataba kan Fatima dakecin abinci tana murmushi yace "yanzu sai kwaleji ko Zara'un Baba, lawyer gidan nan, Allah shi albarka, Allah ya sanya ma certificate din albarka yanzu dazaran wani tsayayye yafito sai aure ko" wani irin kunya ne yakamata da sauri ta tashi tadau abincin ta tai dakinsu, kyalkyacewa da dariya Baba yayi Habib natayashi, Baba ya girgiza kai kawai, tabe baki Mama tayi tace "yartaka da Batada mashinshini gwarama kadena tunanin aurenta yanzu dan ko almajiri batada shi ballema mutumin arziki" sosai maganan ya sosama Baba rai hakan yasa yace "aure lokaci ne Rukayya, yana zuwa akeyi kodako kana coma ne, dududu ma shekarun nata nawane? Ko ashirin bataiba dan haka kisha kurumin ki mijin Zara'una na nan tafe ko Habibun Babanshi" da sauri Habib ya gyadama Baba kai yana murmushi yace "eh Baba wlh inaso inga muma munyi biki kaman gidansu Mansur yayar su tai aure, nima inaso Ya Faty tai aure" murmushi Baba yayi yakai abincin shi baki yana sauraran labarin da Habib ke basu na bikin yayar abokin shi. Saida yagama tsaf sanan yatashi yakalli Mama dake bama Abida data tashi nono yace "bari nafita nema saina dawo" yataba kafan Abida dakeshan nono yace "Yan Matan Baban ta yauko kallona ba'ayi sabida an sami Mama" ture hanunshi tayi dagakan kafanta dan bata kaunar abinda zau hanata shan nonon nan, dan dariya yayi yace "au abun na fadane, zanga mai kawo miki cizi anjima kiyita shan nonon ki" ya kalli Mama yace "natafi" cikeda kuncin rai Mama tace "a dawo lpy" fita yayi rikeda takardan a hannunshi yana gungura machine dinshi ya kwalamata kira. "Zara'u" daga daki ta amsa "na'am Baba" cigaba da gungura machine dinshi yayi zuwa zaure, fitowa tayi sanye da hijabi kanta akasa tawuce tafita daga falon tai hanyar zaure Baba tagani haryay parking machine din awaje ya shigo zauren murmushi yamata yamika mata takardan waec din yace "Allah yamaki albarka yabaki miji nagari kinji, wanda zai soki sanan yakula dake sama dani, kome ake miki kicigaba da hakuri dudda nasan ke yarinya ce mai hakuri ga kunya, ga kawaici wata rana sai labari kinji" gyadamai kai tayi ahankali, ahankali yace "kin koshi da abincin data zuba miki"? da sauri ta gyadamai kai tace "nakoshi wlh Baba" shiru yayi yana kallonta kaman wanda yake wani tunani ganin yanda yake kallonta yasa saitaji tadamu tace "Allah Baba nakoshi kasan banamaka karya ko" sosai idanunshi sukai ja yace "nasani Zahra, bakimin karya na shaidake da wanan y'ata" hannunshi yatura a aljihu yaciro last 1k dayake da ita, mika mata yayi yace "gashi ki boye kidinga kashewa ahankali, kome kikeso ki dinga siya kinji yanzu banda kati awaya, nadawo zan loda kati saina baki ki kira Babarki ki fadamata sakamakon waec dinki kinji" karban kudin tayi tareda dan dukawa tace "nagode Baba Allah ya saka da alkhairi yakara budi" sosai idanunshi sukai jajir yace "wuce kitafi hudu nayi ki tattara kanninki kuwuce islamiyya kinji, ki dage dakaratu ilimi shine adon y'a mace" gyadamai kai tayi tace "Tom Baba" kanta yashafa da hannunshi yadan rungumota side dinshi yace "kiyi addu'a Allah bama babanki kudi, zan sayamiki waya tunda kema yanzu kin dawo budurwa kaman kowace budurwa, da sababbin zannuwan da takalma kinji, da kayan kwalliya" murmushi tayi akunyace tace "Baba karka damu komi lokacine, Allah ya azurtaka da arziki na halas katafi karkai latti" tai maganan tareda juyawa da sauri batason ta nunamai kalamanshi sun tabata, tsayawa yayi shima yabita da kallo harta shige ciki, maganan da Ruka tamai dazu ya sosamai rai ba kadanba kuma deep down yasan da gaskene Zara batada ko mashinshini guda, kuma laifinshi ne yarinya batada kayan arziki tana mace kuma budurwa datake tasawa yanzu amman kayanta sunfi name abincin saidawa kodewa, hijaban ta biyu kacal da maroon dawani mai ruwan toka sun kode harsun fara ja akai tsabagen kodewa, batada wani takalmi na fita sai silifas, kullum fuskarnan nata fayau babu komi aciki yaza'ayi saurayi zai gani ya yaba, koya sami kudi yace zai mata Ruka tahana, saisa yakeson yarinya yanzu ta shirya taje wajen Babarta hutu amman yasan Ruka bazata bariba, ganin dogon tunanin dayake yasa kanshi yafar*a sarawa yasa yajuya yafita kar hawan jininshi yatashi, machine yatada yafice daga anguwan gabaki daya.

MASIFAFFIYAR KAUNAWhere stories live. Discover now