27 & 28

1.3K 21 4
                                    

💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫

       _MASIFAFFIYAR KAUNA_


          ✍🏾M SHAKUR

EPISODE 2️⃣7️⃣ & 2️⃣8️⃣
Wanka yayi ya chanza kaya yafito daga ciki, tundaga stairs yake kallonta ganin yanda rigan jikinta yabaci da da pepper soup din tana zaune a inda yabarta tabude idanun da ayanzu sun dena mata zafin saidai kawai yana yana kaman cobweb dasukasa idanun sukai mata wani irin, tunda taji tafiyarshi tadago kanta ta kalli ta saitin datakejin tafiyan shi, kan kujeran datake zaune yasami gu a gefe yazauna ahankali  yace "you are hungry right, you haven't eaten" kasa amsashi tayi ta saukar da kanta kasa ahankali hadadden kamshin dayakeyi na ratsa hancinshi, doorbell dayay kara alamun an danna yasa ya kalli kofan yabada izinin ashigo, wasu guards suka shigo da warmers da plate hadaddun gaske aka kawo wajen, ijiye abinci akayi agabansu, yasa suka zubamai sanan yasa suka zubama Boy, ya karbi nata yadaura mata a hannu yace "eat" sanan yabasu izini dasu fita.

Lafiyayyen farin rice ne da stew dayaji namomi zako zako, spoon din tadauka tadebi first spoon of rice din takai bakinta da kyar tahadiye saikuma tahau bude baki tana hura iska tana kokarin danne yajin but ina takasa, yajin is something else da sauri ya kalleta yanda takeyi yas yace "is it pepprish?" Gyadamai kai tayi da sauri idanunta natara ruwa again sabida tsabagen yaji, ruwa yadauka yabude yabata takarba tareda kafawa abaki da sauri tana kwalkwala, sakin baki yayi ya tsaya yana kallonta ganin tana neman shanye ruwan goran sanan ta ijiye, da spoon din yaga rana ture stew din saman abincin gefe sanan tafaracin rice din hakanan tanayi tana shan ruwa hartadanci sosai sanan ta ijye shikuma har lokacin yanacin nashi ahankali yana kallon ball abinci dan in dasabo yasaba cin abinci dayaji tunda aka haifeshi.

Saida yaji ankira la'asar sanan yakawo glass din yabide yakama hannunta  yabata yace "saka muga" sakawa tayi ahankali ta kalleshi, ga mamakinta saitaga tana ganinshi amman kadan ba clear ba yafi babu da dazu bata gani ko kadan, da sauri yace "can you see me" gyadamai kai tayi tace "yes but small" ajiyan zuciya yayi da saida taji karanta yazauna kusada ita looking so relieved, ahankali tace "sir I want to go to my room and shower nacire kayan nan" da sauri ya kwalama guard kira, na bakin kofanshi ne suka shigo yace "sukai yaron dakinshi" tafiya dashi sukayi yabisu da kallo sanan yawuce sama yaje yay alwala yay zuhur da asir sanan yakoma ya kwanta sai bacci.

Itama wanka tayi tsaf sanan tadawo dakinta ta kulle tai salla tadade akan dadduma tana addu'an Allah ya tsareta yakareta sanan yabama Baba kudi yazo yacireta tagaji da gidanan nan yautaga azaba iya azaba, tagama tasake tofe kanta da addu'a sanan ta tashi tabude kofa takoma ta kwanta bata koma dakinba kuma bai aiko akirata ba saidai ya aikomata da magungunan ta sanan da biscuits da chocolate din dayasainata.

**************
WASHEGARI!!
Wuraren karfe shidda wani bakin mutumi dake sanye da farin zani kaman yadin likafani yadaurashi yamaidashi kaman wando da riga saidai shoulder shi daya abude da akai wasu irin zane da farin fenti ketahowa cikin fadan yana tafiya yana buga wata sandar hannunshi na karfe, kunenshi na sanye da wasu irin dankunnaye na cowries, hakama hannayenshi yay warwaro da cowries din, kafafunshi ma haka, sanan sandar karfen dayake rikeda shi duk cowries dinne akai dakesa abin yana kara idan yana tafiya yana kara, tundaga nesa duk guard din palace din dazai ganshi zubewa suke suna kwasan gaisuwa yay hanyar fada, da sauri  fadawan dake tsare gaban fadan suka budemai kofa ya shiga ciki ya zauna a tsakiyan fadan akasa, fadawan suka shigo suka zube dan gaidashi, cikin harshen yarensu yace "akiramin Oba dakuma Otun yanzun nan" davmsauri fadawan sukace angama, wasu suka fita sukai cikin gida wasu kuma suka fita dan zuwa kiran Waziri agidanshi da baida nisa sosai da nasu.

Waziri yafara isowa wuraren bakwai, saiga Sarki dan saida ya tsaya yay wanka sanan yazo ya shigo falon da Waziri ke zaune kan kujeranshi shikuma mutumin har lokacin yana kasa bai zauna akan daya daga cikin kujerun dake fadanba, Mai Martaba yashigo yakarasa kan kujeranshi ya zauna Otun na gaidashi, sanan Waziri yabada izini guards su fita suka fice aka rufo musu kofa yarage su kadaine afalon.

MASIFAFFIYAR KAUNAWhere stories live. Discover now