30

1.3K 39 1
                                    

💫 _DISASTROUS LOVE_💫

    _MASIFAFFIYAR KAUNA_

        ✍🏾M SHAKUR

EPISODE 3️⃣0️⃣

Wani dan wahalallan gajeren ihu tasaki, gabaki dayan kanshi nakan cikinta, sauran jikinshi duka nakan kafafuwanta yamugun sakin mata nauyi dayasa taji kaman zata saki fitsari, hannayenta duka biyun tamika tadaura akan saman kanshi tana dan tureshi tace "Sir Sir" jin shiru ko beating heart dinshi bataji yasa gabanta yacigaba da dukan uku uku ahankali da kyar tai ihu dan yanda kanshi kekan cikinta yasa bamata iya fitarda ihu da kyau bamata iya numfashi da kyau tace "he........l.....p" sosai maganan yakasa fita daga bakinta sabida weight din dake kan cikinta, hannayenta tasake daurawa abayanshi tana bubbugawa cikin muryanta dabaya fita sosai tace "please please don't die kaji, wake up Aremo" saikuma tasaki kuka ahankali tana rerawa tana bubbuga bayanshi tana addu'a Allah ya shigoda wani dakin dazai dagashi akaishi asibiti.

Kaman amafarki yaji yaji ana bubbuga bayanshi gakuma sautin rera kuka dayaji anayi kaman na dan karaman yarinya with a very very cool voice, bude idanuwanshi yayi ahankali kadan kadan kafin idanunshi su sauka a dakin dayake akan abinda yake, yaji muryanta chan kasa tana "please don't die, wake up, please someone should come and help Aremo he is sick" maganan chan ciki takeyi hakan zaisa bazaka gane takamaimen dawata kalan murya takeba kona namiji me kona tamace ne tana rera kuka tana bubbugashi abaya, ahankali yadago kanshi yajuyo ya kalleta bamatasan yatashi ba ballema tasan yafarka, gabaki daya idanunta nakan kofan shiga dakin dakenan arufe tana kallo kaman tana jiran wani yabude kofan ya shigo, tana kuka sosai dakebin ta gefen idanunta suna gangarawa har kunnenta ta gefen glass din kan idanunta, tana tabe baki da pink lips dinta sosai duk cikin kuka kana ganinta kasan atsorace take, samin kanshi yayi da daga hannunshi dayaji babu karfi acikinshi yadaura akan kumatunta, jin saukar hannu dakuma sanyin hannun mutum akan fuskarta yasa da sauri tajuyo da kanta, hada ido tayida Tobi dake kallonta da idanunshi dasuka kankance sosai sukai lub, yatsanshi yakai ya sharce hawayen dake gangaromata ta gwfwn idanun har lokacin cikin wata irin murya da take da sanyi sosai irin na nara lafiya yace "why are you crying Boy" har lokacin hannunshi nakan kumatunta yana caressing chic dinta yatsunshi kuma na share hawayen dasuke zubowa, lumshe idanunta tayi dan takasa jure kallon dayake mata, chan kasan makoshi tai magana tace "I thought you died" murya chan kasa yace "you don't want me to die Boy"? Gyadamai kai tayi ahankali, saikuma bakinta yashiga rawa sosai kaman wacce ke shirin fashewa da kuka tace "i...d....ont...want you to die" kasa daina kallon fuskanta yayi sabida yanda hawaye ke bulbulo mata gefen ido suna zuba, murya chan kasa yace "stop crying, I will not be dead now, I will be here and protect this innocent boy okay" gyadamai kai tayi dudda batawani sami natsuwa ba tace "stand up lemme call your parents" sai alokacin ma yatuna ashe yanakan jikin dan yaron nanne, da sauri yatashi ya dagashi ahankali yana dan girgixa kanshi kaman kanshi naciwo yace "sorry" saida yatashi duka ya zauna agefe sanan taja kafanta dataji batajinsu tasaukesu akasa tareda mikewa tsaye baya tayi zata fadi sabida sunyi tsami sun kasa riketa da sauri yatareta ta hanyar rike cikinta yatareta, jiyayi kaman ba fatanta yarikeba hakan yasa yadan taba ciki fizge kanta tayi daga jikinshi da sauri ta matsa yace "how many clothes ne ajikinka Boy" bataredata kalleshi ba tace "plenty" tana goge fuskanta, sanan ta tashi da sauri yace "just sit don't tell them anything, I was angry that's the reason why I went blank, tun ina yaro nakanyi hakan" dan dago kanta tayi ta kalleshi ko kadan he don't look happy bakaman shi data saba ganiba baida surutu amman fuskanshi baida nuna damuwa ko bacin rai, zaka ganshi ko yana kallo, ko wasa da waya kokuma yana jin wakan BTS, kaman bazata ce komiba saikuma tace "why are you angry" da sauri yadagokai ya kalli yaron kaman mai tunani, sauke idanunta tayi kasa ahankali, dan shiru yayi yace "i am angry because of my parents Boy, I know u are too small to understand this, u will not even understand our culture, a yarenmu we don't believe in auren wuri, we believe in yara suyi karatu su gama tatas, sanan su sami aiki su sami gida su zuba komi na rayuwa ahakanne yaro namiji ya isa aure, my parents are caging me, basa barina nai abokanai I tried so many times nayi saisuce a'a ana using aboki acuceka, tun ina University a 🇦🇹Austria har abokanen ma sun rabu dani dan su Dad concrete warning suke basu su rabu da dansu, haka nahakura, da kyar then kakana was alive Maman Dad ita tasaka baki yabarni nafara football, nahakura da duka abubuwan dasuke hanani sabida kwallo zanje nai kwallo team dina I talk to them sunasona d abokantaka because of nasan halin iyayena ban yarda nayi, banson ana gadina yanzu sun kawo masu gadi dabanmasan iya yawansu ba, sun hanani tafiya, ina binsu ne kawai sabida abinda Allah yace muyi kenan kuma ina tausaya musu sabida nasan suna sonane but I hate abinda sukemin Boy" yay shiru yasake lumshe ido, tunda tafara aiki baitaba mata magana mai tsayi irin wanan ba, ga muryanshi da English dinshi dadi, dudda wasu turencin tagane wasu bata ganeba amman tagane asalin inda maganan shi ta dosa, kaman bazata ce komiba amman takasa sabida yabata tausayi and he's such a good man yanada kirki jibi yanda yazane yayarshi data watsa mata pepper soup yakaita asibiti dabadam shiba hala da yanzu ta makance yanzu that he is said zat iya bashi shawara. Ahankali cikin muryanta daba na maza ba bana mataba tace "mu yara munzo duniya ne danmubi iyayen mu, kuma kasan kome muka musu bamu fadi ba, watarana zamuga fa'idan yin hakan, kayakuri kamusu abinda sukeso nayan wasu lokuta kadan ne babu laifi danka tauye farincikin ka kabasu dan suma na tabbata  farin cikinka farin cikinsu ne, suma sun tauye tasu farin cikin ne, na kwana kadan ne xaka iya musu" tunda tafara maganan idanunshi arufe harta gama suna lumshe sanan ta tashi ta shiga maida kayayyakin cikin closet daya zubar duk yana zaune awajen idanunshi a lumshe amman yaron yake kallo tsaf, maganganun  dayayi yasa yaji yaron yawani irin mugun burgeshi, yakara shiganmai rai.

Saida yagama gyara kayan tsaf sanan tajuyo ta kalleshi ganin kaman yay bacci yasa tazohar gabanshi hannunshi takai ta saitin fuskanshi jin yana numfashi yasa ta sauke ijiyan zuciya tawuce tafita tareda bude kofan ahankali gudun karta tadashi, sauka tayi kasa tana kallon ko'ina na falon yanda ko'ina yake agyare sanan tawuce kitchen, fruits taciro daga fridge dinshi ta bare ta yayyanka sanan tazuba a blender tamai smoothie a juye a jar tarufe tasa straw aciki dan tagani yanda akeyi awani video a facebook ta wayan Maryam, dudda bata daddana ba but she hope yay dadi, tabude fridge tasake sakawa sabiya yay sanyi takoma ta dauraye blender ta ijye inda tagani sanan ta dauraye hannunta tawuce tadauko wani dan karamin tray taje fridge din tabude taciro jar na smoothie dayay sanyi sosai ta daura akan tray din fitowa daga kitchen din tayi tamaida kofan tarufe da hannu daya sanan tafito falo ga mamakinta ganinshi tayi zaune a falon yana sanye da farin singlet da boxer ya kishingida akujera ya sanya headphone yana sauraran wakan BTS ya lumshe idanu, kallo daya tamai ta sauke kanta kasa dan tunda take bata taba ganinshi da kananun kaya hakaba, koya tashi daga bacci kanta akasa so bata taba ganinshi ba, karasawa inda yake zaune tayi, jin alamun tafiya yasa yabude idanunshi ahankali, ganin abinda take xaune dashi yasa yadan bude ido ahankali tasauke tray din kusadashi, da sauri ya dauki jar din dashi baimasan yanada shi ba to saunawa ma yake shiga kitchen din baiyi watawataba yakai smoothie bakinshi yasha da straw sanan ya kalleta yace "My Lord Boy u are a pro at creating all this stuff, whats this that taste yum"? Murmushi tayi jin yayabeta shikuma ya tsaya yana kallon dimples dinta da fararen hakoranta ahankali tace "pineapple, coconut and banana smoothie, da little lemon juice, it is good for you, you will stop getting sick" shiru yayi yana kallon yaron saikuma ahankali yakira sunanshi da ayanzu shine abinda yake kiranshi dashi hakan yasa kowama na gidan Boy yake cemata dan ita kadaice karaman yar aiki agida. "Boy" dago kanta tayi ta kalleshi, gefenshi yanuna mata yace "come here" kasa cemai a'a tayi takuma kasa zuwa ganin babu kaya ajikinshi sai kawai ta tsugunna a inda take tsaye tai kneeling ahankali tace "thank you Sir" dan murmushi yayi kaman bashine ranshi abace ba yakara daga jar din ya kalla sanan yace "I love this, thank you Boy". Murmushi sosai tayi jin yagode mata tanemi waje tai xamanta.

**********
Kwanaki nata tafiya shiru Babanta, bata ganshi kullum sarai take zataji ance tazo babanta yazo yabiya kudi amman shiru, ko addu'an datakeyi ne Allah yaji tausayinta, kusan batada matsala da kowa agidan in banda yayyin prince din, duk randa aiki bai riketa ba saitaje wajen Waziri tafadamai komi dayayi wanda baya wuce game, kallo da sauransu, ita kanta yakan bata tausayi yanda akai cage yaron agida, ranan dayakamata yay tafiya Saudi zuwa match din dazai buga dudda batajin yarbanshi but tasan bakaramin bala'i yayi da iyayenshi saida yay kwana uku bata sakashi a ido ba ranan dazata ganshi yace akawoshi yamai aiki taga yarame, saiya zamto ma yarage mata magana, yarage murmushi yarage komi, baimason hayaniya, yana kwance, har Anty Ayobami saida tazo ta lallsheshi idanunshi sukai jajir, itama Ayobami idanunta sukai ja tana mugun son kaninta amman tace ya yakuri sugani nan da bayan kwana hamsin din sugani yace yaji.

Yaune kwana hamsin yacika, yaune kuma yakama watanta uku da kwana ashirin da hudu agidan, Allah narufa mata asiri koda wasa ba'a taba gane mace bane, watan daya wuce tayi ciwon mara, dan arana na uku magungunan ta suka kare amman ta dage ta daure taki nuna tana ciwo tunda ciwon yaragu daman, amman wanan watan tunda aka shiga ashirin gabanta ke faduwa tana tsoro Allah yarufa mata asiri batason tai ciwo, gawani irin zazzabi zazzabi takeji this days da ciwon kirji dan cikin yan kwanakin nan da rana takan dawo dakinta tarufe kofa ta kwance silkin kirjinta sabida kirjinta yahuta, asalin kirjinta namata ciwo sanan nonuwan namata ciwo bana wasaba suma daurewa kawai take take komi, dan babu abinda takejin dadin shi ayanzu aduniyan nan.

Yau tunkafin boka yazo Mum, Dad, da Otun ke zaune afalo suna jiran zuwanshi, bakwai daidai ya shigo ya zauna suka gaidashi, Waziri yace "yaya ake ciki Ooluwo"? Gyarazama Ooluwo yayi yace "inaso duk wasu tsaro dakasa na tsare yaron nan kacire su kabarshi yay rayuwanshi wanan shine abuna farko, mafarkin dakayi rokonka yake karage takuramai kabarshi yafita yay abokanai kakuma dena kallonshi as yaro" ajiyan zuciya Sarki dakowa ma na falon ya sauke, da sauri Mum tace "zancen destiny fa" buga cowries dinshi yayi akasa yace "wanan batun da shaidan nai magana direct yakuma bayyana agabana ya sanardani koshi baida masaniya akan abinda zai faru, kaddararra ce dole zata faru, kawai mu zuba idanu mugani koma ya ake ciki kunada ni sanan bazan hutaba, inaso kuciga sadaka da bakaken bunsurai, muna jiran koma menene, nabarku lpy" yatashi yafita, Mum ta sauke ijiyan zuciya tace "thank you Allah, my son is fine, yau wlh yafita yaje duk inda zashi, wayan nan security su watse mana daga gida abeg, su tashimin daga gaban dakin d'ana ya tsani ganinsu, lemme go and see my beautiful Tobi" ta tatshi tafita da saurinta, Dad ya kalli Otun yace "ka sallami guards din, just a week break sudawo, in as much as destiny bai bayyana ba bazan gaji da tsare d'ana ba, yanzu dai let's allow him to enjoy", gyadamai kai Otun yayi yatashi yafita.

MASIFAFFIYAR KAUNAWhere stories live. Discover now