🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwarsa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._*PAGE: 1*
______Tana gaban murhu tana iza itace, sai da ta gama gyara wa kafin ta ɗago kanta tana fyace majina; ta dubi Hauwa dake gaban ɗakin ta
Inda ita kuma take dakan daddawan da zata zuba a miyan ta
Tace da ita, "Wai kin san me Atine tayi min ɗazu da naje amsar adashi na?"
Hauwa ɗago kai tayi itama tana kallon ta bayan ta tsayar da dakan tace, "A'a sai kin faɗa?"
"Hmm matsiyaciya; ai wlh duk wanda yaci tuwo dani, to, miya ya sha.. duk wani rashin mutuncin mutum dai-dai nake da ƙugun ɗan banza, wabillahil lazi idan har bata biya Ni kuɗi na a goben da tace ba, wlh sai mun kwashi ƴan kallo dani da ita. Kin san tun wancan satin nake bilayin zuwa gidanta ta biya Ni amma ta ƙi, yau kuma da naje take faɗa min zancen banza in dawo gobe".
Murmushi Hauwa tayi kafin tace, "ban da abin ki Sauda; tun yaushe nake faɗa miki ki dena wannan zubin na Atine? Wlh matsalar ta yawa ne da ita, kin san tana taƙama da Mijin ta ɗan sanda ne".
"Yo ɗan sandan uban ta. Ɗan sandan da shi ne me gadi uban waye ya isa yayi wa jan ido? Ina ce kuɗi na ne? Wlh dama duk abinda ake faɗa a kan ta don bata yi min bane, amma yanzu ta taɓo Ni kuma zata san ta taɓo Saudatu".
"To ki dai yi haƙuri don Allah tunda ta ce zata ba ki goben".
Sauda tace, "ai ba wai faɗan bane cikawan ne, Ni kuwa idan bata bani ba banga uban da ya isa na ɗaga mata ƙafa ba, duk anguwar nan sai an ji mu".
"To Allah ya kyauta". Cewar Hauwan tana ci gaba da dakan ta
Sauda tace, "Amin". Tana yin gaba ta ɗauki buta a ƙofar ɗakin ta tashige Toilet.
Lokacin ne yaran ta biyu suka shigo gidan sun dawo daga makaranta, babban ɗan shekara shida Sulaiman, sai ƙanin sa Haidar me shekara huɗu. Da gudu suka shigo gidan suna murna
Hauwa ta tare su da faɗin, "ah ah ƴan makaranta an dawo?"
"Eh Aunty. Kawo in miki dakan". Cewar Suleman yana son ƙwace taɓaryan
Yayinda shima Haidar ya saka hannu zai amsa yana cewa, "Ni ne zan miki Aunty, ai Ni na fi iyawa ko?"
Tana dariya tace, "a'a ku bar min kaya na, daga dawowar ku baku huta ba? Ku dai je ku cire kayan ku kun ji?"
YOU ARE READING
RAYUWAR CIKIN AURE
AdventureTSOKACI Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba...