🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._*DATA SHARE*
Call, message or whatsap 07065334256
*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 daysAirtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 daysGlo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 daysCheap in safety.👌🏼
*PAGE:38*
_____Koda ya je gidan su Afnan, ya tarar an tafi da ita asibiti, ashe tun jiya take ciwon naƙuda, yau da sassafe suka tafi da ita asibitin, kuma ba a samu an kira sa an faɗa masa ba sai yanzu da ya je can ake sanar mishi, shiyasa ya kama hanyar asibiti, a hanya ma ya kira Iyayensa ya sanar musu, sannan ya kira Hauwa ya faɗa mata itama
A tare suka isa asibitin da Hauwa da su Umma,
Lokacin hankula ya tashi har yanzu Afnan tana can tana naƙuda babu labarin haihuwa, tun suna tsammanin fitowar ta yanzu har sun gama fidda rai, musamman yanda suka ga ana ta sintiri a ɗakin da aka shigar da itaAnwar ya kasa tsaye ya kasa zaune, ko masallaci bai iya zuwa ba, sai daga baya ne da aka kira sallan Asar sannan ya je ya haɗa
Su ma su Umma tun suna zaune cikin daɗin rai har sun gaji, ga babu halin tafiya gida tunda har yanzu basu san halin da take ciki ba
Ƴan uwanta sai tururuwan zuwa suke yi duk da an ce musu bata haihu ba, suna ta zuwa su ga halin da take ciki
Bata haihu ba sai gab da magriba asalin naƙudan ya zo mata gadan-gadan, dama sun ƙi mata aiki ne don sun ga alamun zata iya haihuwa da kanta, lokaci ne bai gama yi ba,
Ilai kuwa sai ga ƴaƴa ta sako su har su biyu, abun mamakin basu taɓa tunanin ya'ya biyu zata haifa ba tunda ba a taɓa sanar musu ba, in fact ma ba a taɓa duba mata ba, su dai a hasashen likitoci sun ce ɗaya ne,
Sai ga shi ta sako yara biyu Mata tubarakallah Masha Allah kyawawa da su, sai dai basu da girma ne sosaiZo ku ga murna wurin Anwar, kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha don daɗi da farin ciki, bakin nan ya ƙi rufuwa
Bama shi kaɗai ba; jama'a duk sun yi farin ciki ba kaɗan ba, sai taya su murna ake yi,
Sai lokacin hankula ya kwanta wasu suka tafi gida aka bar dangi na kusa,
Daga Hauwa sai su Maman Afnan ɗin,
Ita kuma Umma tunda ta ga ta haihu sai ta tafi da nufin ta turo ƴar uwanta
YOU ARE READING
RAYUWAR CIKIN AURE
AventuraTSOKACI Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba...