Page 8

135 10 0
                                    

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
            _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

          *P.W.A✍️*




             *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._














             *PAGE:8*

_____Already dama su Muhseen sun san da zuwan su, shiyasa Munira tayi musu girki me rai da lafiya har kala biyu ta jera musu a ƙaramin dainning ɗin su, kana kuma tayi musu zoɓo me daɗi tare da sauran drinks na kwalba dana Robber duk aka tanadar musu. Ta rigada ta gama komi a lokacin da suka iso, shiyasa suka yi musu tarba suka sauke su a falon nasu, su ma sun sha kwalliya sun yi ankon maroon color ɗin shadda uban-uban su iri ɗaya, yayinda Munira ta cakare ɗauri ta sha kwalliya kowa ya kalle ta ya san Amarya ce don sai tashin ƙamshi take yi tana walwali irin na Amare, ga lallin da ta sha hannu da ƙafa gunun sha'awa sun sake fito da ita.

Bayan sun zauna sun gaisa ne Munira Sarkin tsokana tace, "yau ranan taku ce masoya, babu wanda ya kai ku haɗuwa da dacewa wlh, kun matuƙar dacewa da juna, fatan mu Allah ya nuna mana bikin ku muna da rai da Lafiya."

Afnan wacce take shan drinks a kofi; hararan ta tayi sai dai bata ce komi ba illa kurɓan drinks ɗin da take yi

Munira ta sake cewa, "bar harara na addu'a ce nayi muku me kyau don na san shi ne a zuciyar ku, ba ma kamar ke Afnan, ko ba haka ba Husband?" Ta ƙare maganar da kallon Muhseen wanda suke dariya kaɗai

"Haka ne My wife, ai gaskiya kika faɗa idan kuma sun musa su ƙaryata."

Anwar murmushi yayi da cewa, "kun dai haɗe mana kai ne saboda mun zo gidan ku, kodayake ba ƙarya ku ka yi ba, amma kuma duk soyayyar mu ai bamu kai ku ba domin kuwa a bayan ku muke."

"To ai mu mun rigada mun shiga daga ciki mun wuce zancen nan." Cewar Munira tana dariya, sai kuma tace, "Ni dai fata na kar a yaudarar min ƙawata don na san halin ku Mazan nan kaɗan ne daga aikin ku, kar taje kuma ta saki baki tana jiran ka daga baya ka nuna mata halin ku na Maza don Allah."

"Ohh! Wato kina so ki nuna cewa Maza su ne mayaudara ko Wifey?" Inji Muhseen yana mata wani kallo irin tasu na soyayya

Dariya duk suka yi. inda Anwar yace, "yo ka ji zance, ashe kai ma kasan halin Matan nan; son ɗaurawa Maza laifi kamar a kansu aka ƙirƙiro gaskiya."

"Maganar gaskiya ƙawata gaskiya ta faɗa, ai halin ku kenan." Inji Afnan wacce sai yanzu tayi magana, idanunta a kan Anwar ɗin tana ɗan tura baki

Yayinda ya sakar mata wani kallo ba tare da yace komi ba yana yalwata fuskarsa da murmushi

Duk a idanunsu Munira, su ma sai suka yi murmushin kaɗai suna ɗauke kan su

Inda Munira tace, "wlh ba haka bane, Ni abinda yasa na faɗa haka saboda halin ku ne Maza, bare irin ku masu Mata a gida, sai kuyi ta yiwa ƴan mata daɗin baki kuna hana ta tsayawa da samarin ta, daga ƙarshe kuma ku ƙi auren su ku gudu ku bar su, Ni dai gaskiya a riƙe mana alƙawari ato."

RAYUWAR CIKIN AUREWhere stories live. Discover now