🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._*PAGE: 4*
_____Koda suka kai su gida sai da suka tsaya suka ɓata lokaci tare, kafin suka yi musu sallama suka tafi
Inda Anwar Yace ma Muhseen ɗin, "ya kai shi shagon me ɗinki ya amshi ɗinkin shi".
Can suka wuce ya amsa, sannan ya kai shi gida ya sauke shi shima ya wuce
Yana shiga gidan, ledan hannun shi ya miƙa wa Hauwa sannan yayi alwala ya fice masallaci, domin a lokacin har an gama kiran sallan magriba.
Sanda ya dawo tana ɗaki itama ta idar da nata sallan, ya shigo da sallama ta amsa mishi
Zama yayi a gefen gadon yana zame hulan shi
Tayi mishi sannu da zuwa kana ta tashi ta ɗauko mishi abincin sa ta shirya mishi a kan tabarman da ta shimfiɗa
Ƙasa ya sauko ya zauna ya soma ci suna ɗan taɓa hira
Bayan ya gama ya fita ya wanke hannun sa da baki sannan ya wuce masallaci yin sallan isha'i
Da ya dawo ne yake faɗa mata "ta ɗauko ledan ta duba ɗinkunan".
Dama tunda ya bata ta ajiye shi bata duba ba, shiyasa yanzu ta ɗauko ta soma buɗe wa fuskarta a washe da murna, kaya ne har kala biyu yayi mata, Masha Allah sun yi kyau matuƙa. Sai ta ɗago kanta ta kalle shi tana cewa, "ya ban ga naka ba?"
"Ai nawa yana tare dana Muhseen, sai ana gobe bikin zamu amso".
Murmushi tayi sannan ta soma mishi godiya
Yayi dariya yace, "babu haka a tsakanin mu, amma yaushe za ki je gidan su Muhseen ɗin? Don ya kamata ki soma zuwa ko aiki ne ki taya Umma tunda kin san ita kaɗai ce ba wani ƴan uwa ne dasu a nan ba, amma kodayake naji yace ƙannin shi biyu zasu dawo nan ɗin da zama tunda yanzu Allah ya hore".
"Haka ne. Ai Muhseen yana da ƙoƙari, wai da na so ko jibi sai in soma leƙa wa".
"To Allah ya kaimu".
"Amin ya Allah".
"Bari in kwanta yau duk na gaji wlh, kuma gobe ina son fita da wuri".
"To wankan fa baza ka yi ba?" Tace dashi tana kallon shi
Sai da ya kishingiɗa kafin yace, "a'a bar shi wankan nan sai zuwa gobe sai in Yi da safe kafin in fita, kema mayar da kayan nan ki zo ki kwanta don na san kin gaji da yawa".
YOU ARE READING
RAYUWAR CIKIN AURE
AventuraTSOKACI Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba...