🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._*DATA SHARE*
Call, message or whatsap 07065334256
*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 daysAirtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 daysGlo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 daysCheap in safety.👌🏼
*PAGE:40*
_____Da farko Anwar yayi nufin bazai nemi Hauwa ba tunda bada iznin sa tabar gidan sa ba, tabbas ya nuna bazai damu da ita ba tunda kusan sati ɗaya kenan da tafiyar ta amma bai neme ta a waya ba, yace, "idan ta gaji da zaman gidan zata dawo, tunda nan ne rufin asirin ta."
Kuma iyayenta basu neme sa ba; haka shima Iyayansa basu yi masa maganar ta ba, tunda basu san da cewan Hauwa ta bar gidan sa ba, hakan yasa shima bai basu labari ba ya bar abun a ransaCan kuma tunda Hauwa ta koma gida ta kwanta ciwo rigigim,
A lokacin hankalin Hajiya yayi matukar tashi, ta rikice ta shiga tashin hankali da ta ga Hauwa ta dawo mata a wannan yanayin a firgice duk ta rame, ga kayanta da ta zubo a Jaka; wadda hakan yasa tayi tunanin Anwar ne ya sake ta,
Amma koda ta bincika sai Hauwa ta sanar mata da halin da take cikiTace, "ta gaji ne baza ta ci gaba da zama a haka tana ƙunsan baƙin ciki ba, zuciyarta zata iya buga wa ta mutu sabida yanda take ji a wannan lokacin."
Tabbas Hajiya ta yarda cewa an kai Hauwa maƙura, har zuciyarta gaskiya take faɗi, ta tausaya mata matuƙa musamman yanda ta ga ta kwanta jikinta ya rikice sai zazzaɓi,
Shi yasa ta kira Yayansu ta faɗa mishi halin da ake cikiDuk da ba ya garin yana zaune a Zaria ne tare da Iyalansa, amma haka a ranan ya taho suka ɗauke ta zuwa asibiti,
Sun yi tunanin kiran Anwar amma kuma basu samu dama ba har a washe gariA ranan jikin Hauwa da ɗan sauƙi tunda zazzaɓin ya sauka mata, har tana iya zama, sai dai babu walwala a tare da ita ko kaɗan tana cikin tsananin damuwa,
Koda ta ji suna maganar zasu kira Anwar su sanar mishi halin da ake ciki, amma ita ta nuna ba ta bukatar haka, kar su kira sa
YOU ARE READING
RAYUWAR CIKIN AURE
AdventureTSOKACI Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba...