🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._*DATA SHARE*
Call, message or whatsap 07065334256
*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 daysAirtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 daysGlo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 daysCheap in safety.👌🏼
*PAGE:37*
_____Jamal ya rikice sabida ganin yanda Hafsah take kuka, hannayenta ya kamo yana cewa, "lafiya daughter? Me ke damun ki? Me ke faruwa faɗa min inji? Please dena kukan nan don Allah ki yi shiru."
Kasa dena kukan tayi duk da irin rarrashin da yake mata, sai ma duƙar da kanta da tayi tana ƙoƙarin ƙwace hannunta
Amma sai ya ƙi sakin ta yana sake furta, "Hafsah, meke damun ki ne haka ki faɗa min mana? Ko wani abun ne aka yi miki? Ba ki da lafiya ne?"
Sosai fa Jamal ya rikice yana tambayarta sabida ganin yanda take ɓarza kuka abun da bai saba gani ba, ji yake yi kamar ya rungume ta don tsananin tashin hankali da damuwar ganin halin da take cikiDaƙyar ya samu tayi shiru duk da wasu hawayen ne ke fita a cikin idanunta, kuma ta ƙi mishi magana sai faman jan majina take yi tana tunanin ta inda zata fara sanar mishi da maganar,
Hakan ne yasa ya gaji ya miƙa hannu ya janyo ta babu tsammani sai jinta a jikinsa tayi, "wai baza ki faɗa min meke damun ki ba duk kin bi kin tayar min da hankali? Ko so kike nima ki ga hawayen nawa?"
Yayi maganar yana duban fuskarta da tuni ta runtse ido jikinta sai faman rawa yake yiBata yi tunanin zai iya janyo ta jikinsa ba shi yasa lokaci ɗaya duk ta rikice kukan ya tsaya cak; tana rufe idanunta sabida tsananin kunya ta kasa ko motsi bare ta tashi
Shiru yayi yana kallonta, sai ya ɗan yi murmushi yana ɗaukar hannunsa ɗaya ya shafa face ɗin ta tare da furta, "oh! Tun farko da abun da nayi miki kenan tunda kin ƙi yin shiru, amma yanzu kina jin ki a jikin Mijinki har kukan ya ƙafe, buɗe idonki to."
Maimakon ta buɗe sai ta manne fuskar nata a ƙirjinsa tana ɓoye wa cikin kunyan sa
Dariya ya ɗan yi yana ƙara sanya hannu ya rungume ta tare da lumshe ido, shiru suka yi su dukkan su yana sauraron hucin ta da ke fita da ƙarfi, kasa motsa wa yayi illa ƙanƙame ta da ya ƙara yi yana jin wani irin yanayi a tare dashi, tamkar su dauwama a haka gaba ɗaya yanayin ya soma rikitar dashi, musamman yanda yake jin hucin ta da ke saukar masa a ƙirji
YOU ARE READING
RAYUWAR CIKIN AURE
AventuraTSOKACI Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba...