🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._*PAGE:9*
_____Washe gari tun ƙarfe goma har Sauda ta gama shirin ta. A lokacin ko Anwar be bar gidan ba duk ta ishi Hauwa da nacin, "ita fa ta gama shirin ta ita kaɗai take jira."
Anwar wanda ke zaune sa'ilin da Saudan ta bar bakin ƙofan ya kalli Hauwa yace, "wai da wannan Matar zaku je gidan Amaryan?"
"Eh, ita tace zata bi Ni mu je tare."
Tsaki ya ja yana miƙe wa da faɗin, "gaskiya matar nan tana takura min, ko kaɗan ba na son hulɗar ki da ita, Ni fa kwata-kwata ba na son kuna alaƙa ta koya miki halin nan nata, yanzu idan kun fita tare ta je ta janyo rigima ƙarshe har da ke a ciki, tunda kowa zai kalle ku tare ne."
Hauwa wacce take bin shi da kallo, murmushi kaɗai tayi da cewa, "to ya na iya? tunda zaman tare ta haɗa mu sai haƙuri."
"Babu wani zancen sai haƙuri, ke ya kamata ki riƙa janye jikin ki a tattare da ita, matar nan bata da hankali wlh." Sai ya kuma jan tsaki yana ɗaukar hulan sa tare da faɗin, "Ni kinga tafiya na, ki duba rigan can da na cire za ki ga kuɗi na ajiye miki." Daga haka ya fice bayan ya shura takalman sa ya saka ya bar gidan. Tana masa a dawo lafiya ma Ko bi ta kanta be yi ba
Numfashi ta ja cike da rashin jin daɗi, duk da ba yau ya saba da halin Sauda ba amma ita bata ga abun ɗaukar zafi ba, Sauda fitinanniya ce ba kowa yake iya zama da ita ba, sai dai kasancewar ita me haƙuri ne da kau da kai ba ta bari ma wani abu yana shiga a tsakanin su, don dai mutunci Sauda tana dashi matsalan ta kawai rigima da yawan fitina da mutane, ita kuma a yanzu har sun saba ma sabida tsawon shekarun da suka ɗauka, ga shi yanzu kusan shekaru uku kenan suna a tare babu abun da ke haɗa su tunda ta rigada ta laƙanci halin ta... Shigowar Saudan a wannan karo na uku kenan hakan yasa Hauwan tashi tana bata amsar maganar nata da cewa, "to kin dai koran min Miji kinji daɗi Sauda, gani nan yanzu zan yi wanka sai mu tafi, amma fa dole za ki jira in sauke dafen farar shinkafar can tunda bazan bar Mijina da yunwa ba, na san anjima zai dawo kuma ba na nan, tunda ina da miya na dole zan mishi kafin in fita."
Shewa Saudan ta saki tana sake hankaɗa labulen da cewa, "to Hauwa me Miji ai ba sai kin faɗa min kina da Miji ba, daɗin abun nima fa ina da shi bare ki ce za ki yi min gori, tun ɗazu me ya hana shi fita bayan ga shi har rana ta take ai ba haka yake yi ba? sai yau da zamu je anguwa ne zai wani maƙale a ɗaki, ba ga shi tun ɗazu Bilal ya fice ba shi yana zaune ya dirke a ɗaka. Ni wlh ba na son rana ne tayi bamu tafi ba, na fi son a gan mu da sassafe a san da zuwar mu."
YOU ARE READING
RAYUWAR CIKIN AURE
AdventureTSOKACI Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba...