🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱
*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._*PAGE: 2*
_____"Aslm lailum".
"Wa'alaikumus Salam, sannu da zuwa Mijina".
"Yauwa Matata sannu da gida". Yayi maganar bayan ya shigo yana tsaye riƙe da hulan sa
Hauwa amsar hulan tayi ta ajiye a kan gadon su kana tace, "bari in kawo maka ruwa".
"A'a bar ruwan nan bari in je in Yi sallan isha'i in dawo".
A dawo lafiya tayi masa sannan ya fice, ita kuma ta shimfiɗa tabarma a tsakar ɗakin kana ta ɗauko mishi coolarn tuwon shi, ta ajiye tare da ruwa da Plate, sai ta fice don yin kaye-kayen kayan ta sai tayi alwalan itama.
Sauda na zaune bakin ƙofar ta a saman tabarma ita da yaran ta, sun tasa tuwon da Hauwa ta basu suna ta ci. Ganin fitowar Hauwan sai tace, "don Allah Hauwa ki bani aron Naira ashirin Sulaiman ya siyo min maganin sauro, kafin Baban su ya shigo sai in ba ki ko zuwa gobe".
"To". Kawai tace da ita ta koma ta ɗauko mata, bayan ta kai mata ta wuce ta yi abinda ya kawo ta sannan ta koma ɗakin ta
Tana tayar da Sallah Anwar ya shigo da sallama a bakin sa, ganin tana sallah sai be ce komai ba ya samu wuri ya zauna yana tanƙwashe ƙafafuwan sa, tuwon ya buɗe ya zuba ya soma ci
Tana idar da sallan ta juyo tana kallon shi tana murmushi tace, 'meyasa baka bari na zuba maka ba zaka kwashe min lada na?"
Dariya yayi bayan da ya haɗiye loman tuwon bakin sa, yace, "yi haƙuri da Allah, wlh na kasa jira ne da yunwa na dawo".
Marairaice fuska tayi kafin tace, "Allah Sarki Mijina, meyasa ka zauna da yunwa yau?"
"To ya na iya Matata? ai tunda na san ban bar miki komai ba; to, kuwa nima bazan ci komai ɗin ba, kiyi haƙuri wlh yau gaba ɗaya buga-bugan ne sai a hankali, ban samu kuɗin bane shiyasa ban dawo na ba ki na cefane ba, wlh kina raina na rasa ya zan yi, duk bashi suka ci Abokan harƙallan nawa sai gobe zasu bani".
"Hmmm babu komai ai, ko baka faɗa min ba na san babu Mijina, ba yau muka saba haƙuri ba kuma haka nan zamu ci gaba da yi insha Allahu Allah zai taimake mu, duk sanda aka ce ka sami aikin ka na san komi zai wuce ai na lokaci ƙanƙani ne".
Murmushi yayi Anwar ɗin, cikin so da ƙauna da tausayin matar tashi yace, "haka ne Mata ta na san komi zai wuce, amma ina gani kamar gazawata ce ace Ni na kasa ciyar dake sai ke ce kike ci dani, ga shi yanzu duk na cinye miki ɗan jarin da kike taƙama dashi, yanzu kuma ban san ya aka yi kika samo na yau kika yi mana ba?"
YOU ARE READING
RAYUWAR CIKIN AURE
PertualanganTSOKACI Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba...